Sashe na 7: Zunubin Solomon (continued)

980 zuwa 975 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Mai Hadishi 6–7

1 Na ga wani mugun abu a duniya, ya kuma nawaita wa mutane ƙwarai. 2 Allah yakan ba mutum dukiya, da wadata da kuma girma, don kada yă rasa abin da ransa yake so, amma Allah bai ba shi zarafin more su ba, a maimakon haka ma sai baƙo ne yă more su. Wannan ba shi da amfani, mugun abu ne ƙwarai.

3 Mutum zai iya kasance da ’ya’ya ɗari, yă kuma yi shekaru masu yawa; duk da haka kome daɗewarsa, in bai more wadatarsa ba, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba, na ce, gara wanda aka haife shi gawa. 4 Haihuwa ba tă amfane wanda aka haifa gawa ba, gama ya zo daga duhu ya koma duhu inda aka manta da shi. 5 Ko da yake bai ga hasken rana ba, bai kuma san kome ba, duk da haka ya dai huta, fiye da mutumin da bai more wa ransa ba, 6 ko da ya yi shekara dubu biyu amma bai more wadatarsa ba. Ba wuri ɗaya dukansu biyu za su tafi ba?

7 Dukan ƙoƙarin da mutum yake yi, yana yi ne domin bakinsa,

duk da haka bai taɓa gamsar da abin da yake marmari.

8 Da me mai hikima ya fi wawa?

Wace riba ce matalauci yakan samu don yă iya zama da mutane?

9 Gara abin da ido ya gani

da kwaɗayin da bai sami biyan bukata ba.

Wannan ma ba shi da amfani,

naushin iska ne kawai.

10 Duk abin da ya kasance, to, yana da suna,

kuma duk abin da mutum yake, an riga an sani.

Ba mutumin da zai iya ƙarawa

da wanda ya fi shi ƙarfi.

11 Yadda yawan magana take

haka ƙarancin amfaninta,

yaya wannan zai amfane wani?

12 Gama wa ya san abin da ya fi dacewa ga mutum a ’yan kwanakinsa marasa amfani da sukan wuce kamar inuwa? Wa kuma zai iya faɗa masa abin da zai faru a duniya bayan ya rasu?

7:1 Suna mai kyau ya fi turare mai ƙanshi,

kuma ranar mutuwa ta fi ranar haihuwa.

2 Gara a tafi gidan makoki

da a je gidan biki,

gama mutuwa ce ƙaddarar kowane mutum;

ya kamata masu rai su lura da haka.

3 Baƙin ciki ya fi dariya,

gama baƙin ciki yakan kawo gyara.

4 Zuciyar masu hikima tana a gidan makoki,

amma zuciya wawaye tana a gidan shagali.

5 Gara ka saurari tsawatawar mai hikima

da ka saurari waƙar wawaye.

6 Kamar ƙarar ƙayar da take karce gindin tukunya,

haka dariyar wawaye take.

Wannan ma ba shi da amfani.

7 Zalunci yakan mai da mutum mai hikima wawa,

cin hanci kuma yakan lalace hali.

8 Ƙarshen abu ya fi farkonsa,

haƙuri kuma ya fi girman kai.

9 Kada ranka yă yi saurin tashi,

gama fushi yana zama a cinyar wawaye.

10 Kada ka ce, “Me ya sa kwanakin dā sun fi waɗannan?”

Gama ba daidai ba ne a yi irin waɗannan tambayoyi.

11 Hikima, kamar gādo, abu mai kyau ne

tana kuma da amfani ga waɗanda suka ga rana.

12 Hikima mafaka ce

takan kāre mutum kamar yadda kuɗi suke yi.

Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita

ita ce amfanin ilimi.

13 Ku lura da abin da Allah ya yi.

Wa zai iya miƙe

abin da ya tanƙware?

14 Sa’ad da al’amura suke tafiya daidai, ka yi farin ciki,

amma sa’ad da suka lalace, ka tuna,

Allah ne ya yi wancan

shi ne kuma ya yi wannan.

Saboda haka, mutum ba zai san

wani abu game da nan gabansa ba.

15 A cikin rayuwan nan ta rashin amfani nawa, na lura da waɗannan abubuwa biyu,

mai adalci yana hallakawa cikin adalcinsa,

mai mugunta kuma yana tsawon rai cikin muguntarsa.

16 Kada ka cika yin adalci, fiye da kima,

kada kuma ka cika yin hikima,

don me za ka hallaka kanka!

17 Kada ka cika yin mugunta,

kada kuma ka cika yin wauta,

don me za ka mutu kafin lokacinka?

18 Yana da kyau ka kama ɗaya

ba tare da ka saki wancan ba.

Mai tsoron Allah zai guji wuce gona da iri.

19 Hikima takan sa mutum guda mai hikima yă yi ƙarfi

fiye da masu mulki goma a cikin birni.

20 Babu mai adalci a duniya

wanda yake yin abin da yake daidai da bai taɓa yin zunubi ba.

21 Kada ka mai da hankali ga dukan abin da mutane suke faɗi,

in ba haka ba wata rana za ka ji bayinka suna zaginka.

22 Gama kai kanka ka sani

cewa sau da yawa ka zagi waɗansu.

23 Dukan waɗannan na gwada su ta wurin hikima na kuma ce,

“Na ƙudurta in zama mai hikima,”

amma abin ya fi ƙarfina.

24 Ko da me hikima take,

Abin ya yi mana zurfi ƙwarai, yana da wuyar ganewa,

wa zai iya gane shi?

25 Saboda haka na mai da hankalina ga fahimi,

don in bincika in nemi hikima da yadda aka tsara abubuwa,

in kuma fahimci wawancin mugunta

da haukar wauta.

26 Sai na iske wani abin da ya fi mutuwa ɗaci

mace wadda take tarko ne,

wadda zuciyarta tarko ne

wadda kuma hannuwanta sarƙa ne.

Mutumin da ya gamshi Allah zai tsere mata,

amma za tă kama mai zunubi.

27 Malami ya ce, “Duba, abin da na gane ke nan.

“Na tara abu guda da wani, don in gane tsarin abubuwa,

28 yayinda nake cikin nema

amma ban samu ba,

sai na sami adali guda cikin dubu,

amma ba mace mai adalci guda a cikinsu duka.

29 Wannan ne kaɗai abin da na gane.

Allah ya yi mutum tsab

amma sai muka rikitar da kanmu.”