Sashe na 7: Zunubin Solomon (continued)
980 zuwa 975 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Wa yake kama da mai hikima?
Wa ya san bayanin abubuwa?
Hikima takan haskaka fuskar mutum,
ta kuma kawo sakin fuska.
2 Ka yi biyayya da umarnin sarki, na ce, saboda alkawarin da ka yi a gaban Allah. 3 Kada ka yi hanzarin tashi daga gaban sarki. Kada ka kāre abin da ba daidai ba, gama zai iya yin duk abin da ya ga dama. 4 Da yake maganar sarki ita ce mafificiya, wa zai iya ce masa, “Me kake yi?”
5 Duk wanda ya yi biyayya da umarninsa ba zai sami lahani ba,
zuciya mai hikima kuma zai san lokacin da ya dace da kuma hanyoyin da suka fi.
6 Gama akwai lokaci da hanyoyin da suka dace da yin kowane abu,
ko da yake wahalar mutum ta yi masa yawa.
7 Da yake ba wanda ya san nan gaba,
wa zai iya faɗa masa abin da zai faru?
8 Ba wanda yake da iko a kan iska har da zai riƙe ta,
saboda haka babu mai iko kan ranar mutuwarsa.
Kamar yadda ba a sallamar mutum a lokacin yaƙi,
haka ma mugunta ba za tă saki masu aikata ta ba.
9 Na ga dukan waɗannan, yayinda na lura da kowane abin da ake yi a duniya. Akwai lokacin da mutum yakan nauyaya wa waɗansu ba da sonsa ba. 10 Sa’an nan kuma, na ga an binne masu mugunta, waɗanda suke shiga da fita daga tsattsarkan wuri suke kuma samun yabo a birnin da suka yi wannan. Wannan ma ba shi da amfani.
11 In ba a hanzarta aka yanke hukunci a kan laifi ba, zukatan mutane sukan cika da ƙulle-ƙullen aikata abubuwan da ba daidai ba. 12 Ko da yake mugu ya aikata laifi ɗari ya kuma yi tsawon rai, na san cewa zai fi wa masu tsoron Allah kyau, waɗanda suke girmama Allah. 13 Duk da haka, domin masu mugunta ba su ji tsoron Allah ba, abubuwa ba za su yi musu kyau ba, ransu kamar inuwa yake ba zai yi tsawo ba.
14 Akwai kuma wani abu marar amfani da yake faruwa a duniya, masu adalci sukan sha hukuncin da ya dace da masu mugunta, masu mugunta kuma sukan karɓi sakayyar da ya cancanci masu adalci su samu. Na ce, wannan ma, ba shi da amfani. 15 Saboda haka abin da na ce, shi ne mutum yă ji daɗi, domin iyakar jin daɗinsa a wannan rai, shi ne yă ci, yă sha, yă ji wa kansa daɗi. Aƙalla yana iya yin wannan in ya yi aiki a kwanakin da Allah ya ba shi a wannan duniya.
16 Da na mai da hankalina don in sami hikima in kuma lura da wahalar mutum a duniya, ko da a ce idanunsa ba sa barci dare da rana, 17 sam, ba zai taɓa fahimci abin da Allah yake yi ba. Iyakar ƙoƙarin da ka yi duk ba za ka iya ganewa ba. Masu hikima suna iya cewa sun sani, amma kuwa ba su sani ba.
9:1 Sai na yi tunani a kan wannan na kuma gane cewa masu adalci da masu hikima da kuma abubuwan da suke yi suna a hannun Allah ne, amma ba wanda ya san ko ƙauna ko ƙiyayya ce take jiransa. 2 Dukansu makomarsu ɗaya ce, masu adalci da masu mugunta, masu kirki da marasa kirki, masu tsabta da marasa tsabta, masu miƙa hadaya da waɗanda ba sa yi.
Kamar yadda yake ga mutumin kirki,
haka yake ga mai zunubi.
Kamar yadda yake ga masu yin rantsuwa,
haka ma da masu tsoron yi.
3 Wannan ita ce muguntar da take faruwa a cikin dukan abubuwa a duniya. Ƙaddara ɗaya ce take a kan kowa. Amma zukatan mutane cike suke da mugunta, akwai kuma hauka a zukatansu yayinda suke a raye, bayan haka kuma sai su mutu. 4 Duk wanda yake da rai a wannan duniya ta rayayyu, yana sa zuciya, gara rayayyen kare da mataccen zaki!
5 Gama rayayyu sun san za su mutu,
amma matattu ba su san kome ba;
ba su da wata lada nan gaba
an manta da su ke nan gaba ɗaya.
6 Ƙaunarsu, ƙiyayyarsu,
da kuma kishinsu tuni sun ɓace;
ba za su taɓa zama sashen
wani abin da yake faruwa a duniya ba.
7 Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da farin zuciya, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah. 8 Kullum ka kasance cikin farin riguna, ka kuma shafe kanka da mai kullum, 9 Ka more rayuwa da matarka, wadda kake ƙauna, dukan kwanakin nan marasa amfani da Allah ya ba ka a duniya. Gama wannan ne rabonka a rayuwa da kuma na faman aikinka a duniya. 10 Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima.
11 Na kuma ga wani abu a duniya.
Ba kullum maguji ne yake nasara a tsere ba,
ba kullum jarumi ne yake yin nasara ba,
ba kullum mai hikima ne da abinci ba
ba kullum mai basira ne yake da wadata ba
ba kullum gwani ne yake samun tagomashi ba;
amma sa’a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu.
12 Ban da haka ma, ba wanda ya san sa’ad da lokacin mutuwarsa zai yi.
Kamar yadda akan kama kifi a muguwar raga,
ko a kama tsuntsu a tarko,
haka mugun lokaci yakan auko wa mutane, ba tsammani.
13 Na kuma ga wani misali game da hikima a duniya wanda ya burge ni sosai. 14 An yi wani ɗan ƙaramin birni mai mutane kaɗan a ciki. Sai wani babban sarki ya kawo masa yaƙi, ya kafa masa babban sansani. 15 A cikin birnin nan kuwa akwai wani mutum matalauci amma mai hikima, ya kuma ceci birnin ta wurin hikimarsa. Amma ba wanda ya tuna da matalaucin nan. 16 Sai na ce, “Hikima ta fi ƙarfe ƙarfi.” Amma aka rena hikimar matalaucin, ba a ma jin maganarsa.
17 Raɗar mai hikima da aka saurara cikin natsuwa
ta fi ihun mai mulkin wawaye.
18 Hikima ta fi kayan yaƙi,
amma mai zunubi ɗaya yakan rushe alheri mai yawa.