Sashe na 7: Zunubin Solomon (continued)
980 zuwa 975 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Kamar yadda matattun ƙudaje sukan ɓata ƙanshin turare,
haka ’yar wauta takan ɓata hikima da daraja.
2 Zuciyar mai hikima takan karkata ga yin abin da yake daidai,
amma zuciyar wawa takan karkata ga yin mugun abu.
3 Ko yayinda yake tafiya a kan hanya
wawa yakan nuna cewa ba shi da hankali,
yakan nuna wa kowa wawancinsa.
4 In hankalin mai mulki ya tashi game da kai,
kada ka bar inda kake,
gama kwantar da hankali yakan sa a yafe manyan laifofi.
5 Akwai muguntar da na gani a duniya,
irin kuskuren da yake fitowa daga masu mulki.
6 Akan sa wawaye a manyan matsayi,
yayinda masu arziki suna ƙarƙashi.
7 Na taɓa ganin bayi a kan dawakai,
yayinda ’ya’yan sarki suna takawa a ƙasa kamar bayi.
8 Duk wanda ya haƙa rami shi ne zai fāɗa a ciki;
duk wanda ya rushe katanga, shi maciji zai sara.
9 Duk mai farfasa duwatsu shi za su yi wa rauni;
duk mai faskaren itace yana cikin hatsarinsu.
10 In gatari ya dakushe
ba a kuma wasa shi ba,
dole a yi amfani da ƙarfi da yawa,
amma ƙwarewa yana kawo nasara.
11 In maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi,
ina amfanin maganin?
12 Kalmomi daga bakin mai hikima alheri ne,
amma maganganun wawa za su hallaka shi.
13 Farkon maganarsa wauta ce,
ƙarshenta kuma takan zama muguwar hauka,
14 wawa kuma yakan yi ta surutu.
Ba wanda ya san abin da zai zo
wa zai iya faɗa masa abin da zai faru bayan rasuwarsa?
15 Aikin wawa yakan gajiyar da shi,
har bai san hanyar zuwa gari ba.
16 Kaitonki, ya ke ƙasa wadda sarkinki bawa ne
wadda kuma hakimanta ke ta shagali tun da safe.
17 Mai albarka ce, ya ke ƙasa wadda sarkinki haifaffen gidan sarauta ne,
wadda hakimanta suke samun abincinsu a daidai lokacin
don samun ƙarfi ba don buguwa ba.
18 In mutum rago ne, sai tsaiko yă lotsa,
in hannuwansa ba masa yin kome, ɗaki yakan yi yoyo.
19 Akan shirya abinci don jin daɗi,
ruwan inabi kuwa don faranta zuciya,
amma kuɗi ne amsar kome.
20 Kada ka zagi sarki ko da a cikin tunaninka ne,
ko ka zagi mai arziki ko da a ɗakin kwananka ne,
gama tsuntsun sararin sama zai iya ɗauki maganarka,
tsuntsu mai fikafikai zai sanar da abin da ka ce.
11:1 Ka jefa burodinka a bisa ruwaye,
gama bayan kwanaki masu yawa, za ka sāke samunsa.
2 Ka raba abin hannunka ga mutum bakwai, I, har ma takwas,
gama ba ka san bala’in da zai auko wa ƙasar ba.
3 In gizagizai sun cika da ruwa,
sukan zub da ruwan sama bisa duniya.
Itace ya fāɗi, ko wajen kudu ne, ko wajen arewa,
inda ya fāɗi a nan zai kwanta.
4 Duk mai la’akari da iska, ba zai yi shuka ba,
mai la’akari da gizagizai kuma, ba zai yi girbi ba.
5 Kamar yadda ba ka san hanyar iska ba,
ko yadda aka siffanta jiki a cikin mahaifiya,
haka ba za ka fahimci aikin Allah
Mahaliccin dukan abubuwa ba.
6 Ka shuka irinka da safe,
da yamma kuma kada ka janye hannunka,
gama ba ka san wanda zai yi albarka ba,
ko wannan ko wancan,
ko kuma duka biyunsu su yi albarka.
7 Haske da yana da kyau,
abu mai kyau ne kuma idanu su dubi rana.
8 Kome tsawon rayuwar mutum,
bari yă more su duka.
Amma bari kuma yă tuna da kwanakin duhu,
gama su ma za su yi yawa.
Duk abin da zai faru ba shi da amfani.
9 Ka yi murna, kai matashi, a ƙuruciyarka,
bari zuciyarka kuma tă yi farin ciki a kwanakin ƙuruciyarka.
Ka bi shawarar zuciyarka
da kuma duk abin da idanunka suka gani,
amma ka sani fa, cikin dukan al’amuran nan
Allah zai shari’anta ka.
10 Saboda haka, ka fid da tsoro daga zuciyarka
ka kakkaɓe duk wani abin da ya dami rayuwarka,
gama ƙuruciya da ƙarfi ba su da amfani.
12:1 Ka tuna da Mahaliccinka
a kwanakin ƙuruciyarka,
kafin lokacin wahala ta zo
shekaru kuma su ƙarato sa’ad da za ka ce,
“Ba na jin daɗinsu,”
2 kafin rana da haske
wata da taurari su daina haske,
gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙa ruwa;
3 sa’ad da masu tsaron gida suke rawar jiki,
majiya ƙarfi kuma suka rasa ƙarfi,
sa’ad da masu niƙa suka daina don ba su da yawa,
idanun da suke duba ta taga suka duhunta;
4 sa’ad da aka rufe ƙofofin shiga tituna
ƙarar niƙa kuma ya tsagaita;
sa’ad da kukan tsuntsaye ta farkar da mutane,
ba a kuwa jin waƙoƙinsu,
5 sa’ad da mutane suke jin tsoron tudu
da kuma hatsarori a tituna;
sa’ad da itacen almon ya toho,
fāra kuma ya yi ta jan jikinsa da ƙyar,
sha’awace-sha’awace sun kafe.
Daga nan mutum ya tafi madawwamiyar gidansa
ya bar masu makoki suna ta yi.
6 Ka tuna da shi, kafin igiyar azurfa ta katse,
ko tasar zinariya ta fashe;
kafin tulu yă ragargaje a maɓulɓula,
ko guga ta tsinke a rijiya,
7 turɓaya ta koma ƙasar da ta fito,
rai kuma yă koma ga Allah wanda ya ba da shi.
8 “Ba amfani! Ba amfani!” In ji Malami,
“Gaba ɗaya ba amfani!”
9 Ba kawai Malami ya kasance mai hikima ba, amma kuma ya koyar da mutane. Ya yi tunani ya kuma yi binciken da ya tsara karin magana masu yawa. 10 Malami ya yi bincike don yă sami kalmomin da suka dace, kuma abin da ya rubuta daidai ne da kuma gaskiya.
11 Kalmomin masu hikima kamar tsinken tsokanar dabba ne, tarin maganganunsu kuma kamar ƙusoshi ne da aka kafa daram, da aka ba wa Makiyayi guda. 12 Ka yi hankali ɗana, game da duk wani ƙari a kan waɗannan.
Wallafa littattafai ba shi da iyaka, kuma yawan karatu yakan gajiyar da jiki.
13 Yanzu an ji kome;
ga ƙarshen magana.
Ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye umarnansa,
gama wannan shi ne dukan hakkin mutum.
14 Gama Allah zai shari’anta kowane irin aiki,
har da waɗanda aka yi a ɓoye,
ko nagari ne, ko mugu.