Kalmomin Agur da Sarki Lemuwel

984 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Karin Magana 30–31

1 Maganganun Agur ɗan Yake, magana ce horarriya.

Wannan mutum ya furta wa Itiyel da kuma ga Ukal,

2 “Ni ne mafi jahilci a cikin mutane;

ba ni da fahimi irin na mutum.

3 Ban koyi hikima ba,

ba ni kuma da sani game da Mai Tsarkin nan,

4 Wane ne ya taɓa haura zuwa sama ya dawo?

Wane ne ya tattara iska a tafin hannuwansa?

Wane ne ya nannaɗe ruwaye a cikin rigarsa?

Wane ne ya kafa dukan iyakokin duniya?

Mene ne sunansa, da kuma sunan ɗansa?

Faɗa mini in ka sani!

5 “Kowace maganar Allah ba ta da kuskure;

shi ne garkuwa ga waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.

6 Kada ka ƙara ga maganarsa,

in ba haka ba zai tsawata maka ya kuma nuna kai maƙaryaci ne.

7 “Abu biyu ina roƙonka, ya Ubangiji;

kada ka hana ni kafin in mutu.

8 Ka kawar da ƙarya da kuma ƙarairayi nesa da ni;

kada ka ba ni talauci ko arziki,

amma ka ba ni abincina na yini kaɗai.

9 In ba haka ba, zan wadace in ƙi ka

har in ce, ‘Wane ne Ubangiji?’

Ko kuwa in zama matalauci in yi sata

ta haka in kunyata sunan Allahna.

10 “Kada ka baza ƙarairayi game da bawa ga maigidansa,

in ba haka ba, zai la’ance ka, za ka kuwa sha wahala a kan haka.

11 “Akwai waɗanda sukan zagi mahaifinsu

ba sa kuma sa wa mahaifiyarsu albarka;

12 waɗanda sukan ɗauka su tsarkaka ne a ganinsu

alhali kuwa ƙazamai ne su;

13 waɗanda kullum idanunsu masu kallon reni ne,

waɗanda kallon da suke yi na daurin gira ne;

14 waɗanda haƙoransu takuba ne

waɗanda kuma muƙamuƙansu tarin wuƙaƙe ne

don su cinye matalauta daga duniya

da kuma mabukata daga cikin mutane.

15 “Matsattsaku tana da ’ya’ya mata biyu.

Suna kuka suna cewa, ‘Ba ni! Ba ni!’

“Akwai abubuwa uku da ba sa taɓa ƙoshi,

guda huɗu ba sa taɓa cewa, ‘Ya isa!’

16 Kabari, mahaifar da ba ta haihuwa,

ƙasa, wadda ba ta taɓa ƙoshi da ruwa,

da kuma wuta, wadda ba ta taɓa cewa ‘Ya isa!’

17 “Idon da yake yi wa mahaifi ba’a,

wanda yake wa mahaifiya dariyar rashin biyayya,

hankakin kwari za su ƙwaƙule masa ido,

ungulai za su cinye su.

18 “Akwai abubuwa uku da suke ba ni mamaki,

abubuwa huɗu da ba na iya fahimtarsu,

19 yadda gaggafa take firiya a sararin sama,

yadda maciji yake tafiya a kan dutse,

yadda jirgin ruwa yake tafiya a teku,

da kuma sha’ani tsakanin namiji da ’ya mace.

20 “Ga yadda mazinaciya take yi.

Takan ci ta share bakinta

ta ce, ‘Ban yi wani abu marar kyau ba.’

21 “Akwai abubuwa uku da duniya kan yi rawan jiki,

abubuwa huɗu da ba ta iya jurewa,

22 bawan da ya zama sarki,

wawan da ya ƙoshi da abinci,

23 macen da ba a ƙauna wadda ta sami miji,

da kuma baiwar da ta ɗauki matsayin uwargijiyarta.

24 “Akwai abubuwa huɗu a duniya da suke ƙanana,

duk da haka suna da hikima ƙwarai.

25 Kyashi halittu ne da ba su da ƙarfi sosai,

duk da haka suna ajiyar abincinsu da rani;

26 remaye halittu ne da ba su da ƙarfi sosai,

duk da haka sukan yi gidajensu a duwatsu;

27 fāra ba su da sarki,

duk da haka suna tafiya tare bisa ga girma;

28 ana iya kama ƙadangare da hannu,

duk da haka akan same shi a fadodin sarakuna.

29 “Akwai abubuwa uku da suke jan jiki da kuma taƙama a tafiyarsu

abubuwa huɗu waɗanda suke kwarjini da taƙama a tafiyarsu,

30 zaki mai ƙarfi a cikin namun jeji, wanda ba ya ratse wa kowa;

31 zakara mai taƙama,

da bunsuru,

da kuma sarki mai sojoji kewaye da shi.

32 “In ka yi wauta ka kuma ɗaukaka kanka,

ko kuwa wani yana ƙulla maka mugunta,

ka dāfa hannunka a bisa bakinka!

33 Gama kamar yadda kaɗaɗɗen madara takan kawo mai,

murɗa hanci kuma takan sa a yi haɓo,

haka tsokanar fushi takan kawo faɗa.”

31:1 Maganganun Sarki Lemuwel, magana ce horarriya mahaifiyarsa ta koya masa,

2 “Ka saurara, ya ɗana! Ka saurara, ɗan cikina!

Ka saurara, ya ɗan amshin addu’ata!

3 Kada ka ba da ƙarfinka a kan mata,

ƙarfinka ga waɗanda suka hallaka sarakuna.

4 “Ba na sarakuna ba ne, ya Lemuwel,

ba na sarakuna ba ne su sha ruwan inabi,

ba na masu mulki ba ne su yi marmarin barasa,

5 don kada su sha su manta da abin da doka ta umarta,

su hana wa waɗanda aka danne hakkinsu.

6 A ba da barasa ga waɗanda suke cikin halin ƙaƙa naka yi,

ruwan inabi ga waɗanda suke cikin wahala;

7 bari su sha su manta da talaucinsu

kada kuma su ƙara tunawa da ɓacin ransu.

8 “Yi magana domin bebaye,

domin hakkin dukan waɗanda suke naƙasassu.

9 Yi magana a kuma yi shari’ar adalci;

a tsare hakkin talakawa da masu bukata.”

10  Wa yake iya samun mace mai halin kirki?

Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai.

11 Mijinta yana da cikakken amincewa da ita

kuma ba ya rasa wani abu mai daraja.

12 Takan yi masa alheri ba mugunta ba,

dukan kwanakin ranta.

13 Takan zaɓi ulu da lilin

ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki.

14 Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne

tana kawo abincinta daga nesa.

15 Takan farka tun da sauran duhu;

ta tanada wa iyalinta abinci

ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.

16 Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta;

daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.

17 Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru;

hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.

18 Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta,

kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.

19 Da hannunta take riƙe abin kaɗi

ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta.

20 Takan marabci talakawa

takan kuma taimaki masu bukata.

21 Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta;

gama dukansu suna da tufafi masu kauri.

22 Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa;

tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.

23 Ana girmama mijinta a ƙofar shiga birni

inda yakan zauna a cikin dattawan gari.

24 Takan yi riguna na lilin ta sayar;

takan kuma sayar wa ’yan kasuwa da ɗamara.

25 Ƙarfi da mutunci su ne suturarta;

za tă iya yin dariyar kwanaki masu zuwa.

26 Tana magana da hikima,

kuma umarnai mai aminci yana a harshenta.

27 Tana lura da sha’anin gidanta

kuma ba ta cin abincin ƙyuya.

28 ’Ya’yanta sukan tashi su ce da ita mai albarka;

haka mijinta ma, yakan kuma yabe ta yana cewa,

29 “Mata da yawa suna yin abubuwan yabo,

amma ke kin fi su duka.”

30 Kayan tsari yana ruɗu, kyau kuma kan shuɗe;

amma mace mai tsoron Ubangiji abar yabo ce.

31 Ka ba ta ladar da ya dace tă samo wa kanta,

bari kuma ayyukanta su kawo mata yabo a ƙofar shiga birni.