Ƙarin Karin Maganar Solomon (continued)

984 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Karin Magana 28–29

1 Mugu yakan gudu ko babu wanda yake korarsa,

amma adalai suna da ƙarfin hali kamar zaki.

2 Sa’ad da ƙasa ta yi tayarwa, takan kasance da masu mulki da yawa,

amma mai fahimi da sani kan mai da zaman lafiya.

3 Mai mulkin da ya danne talakawa

yana kama da ruwan saman da ya lalatar da hatsi.

4 Duk waɗanda ba sa bin doka yabon mugaye suke yi,

amma waɗanda suke yin biyayya da doka suna gāba da mugaye ke nan.

5 Mugaye ba su san gaskiya ba,

amma waɗanda suke neman Ubangiji sun santa sosai.

6 Gara matalauci wanda yake tafiya babu abin zargi

da mai arziki wanda hanyoyinsa mugaye ne.

7 Duk wanda ya kiyaye doka ɗa ne mai la’akari,

amma wanda yake abokantaka da masu zari yakan jawo wa mahaifinsa kunya.

8 Duk wanda ya tara dukiyarsa ta wurin ba da bashi da ruwan da ya wuce misali

yana tara wa wani ne wanda zai yi wa talakawa alheri.

9 In wani ya yi kunnuwa ƙashi ga doka

ko addu’arsa ma abar ƙyama ce.

10 Duk wanda ya jagorance masu aikata gaskiya a hanyar mugunta

zai fāɗa cikin tarkonsa

amma marasa abin zargi za su sami gādo mai kyau.

11 Mai arziki zai yi zato shi mai hikima ne a ganinsa,

amma matalauci mai basira ya fi shi sanin abin da yake daidai.

12 Sa’ad da adalai suka yi nasara, kowa yakan yi biki;

amma sa’ad da mugu ya samu shugabanci, mutane sukan yi ta ɓuya.

13 Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara,

amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai.

14 Mai albarka ne mutumin da kullum yake jin tsoron Allah,

amma duk wanda ya taurare zuciyarsa yakan shiga wahala.

15 Kamar rurin zaki ko sanɗar beyar

haka mugun mutum mai mulki a kan mutane marasa ƙarfi yake.

16 Mugu mai mulki ba shi da azanci,

amma duk wanda yake ƙin ƙazamar riba yakan yi tsawon rai.

17 Mutumin da laifin kisa ya yi ta damunsa

zai zama mai gudu don tsoro har mutuwa;

kada wani ya taimake shi.

18 Duk wanda ya yi tafiya marar abin zargi zai zauna lafiya,

amma duk wanda hanyoyinsa mugaye ne zai fāɗi nan da nan.

19 Duk wanda ya nome gonarsa zai sami amfani a yalwace,

amma duk wanda yake zaman banza zai zama matalauci a koyaushe.

20 Mutum mai aminci zai cika da albarka,

amma duk mai son yin arziki dare ɗaya zai sha hukunci.

21 Nuna sonkai ba shi da kyau,

duk da haka mutum zai aikata abin da ba daidai ba saboda ’yar ƙaramar rashawa.

22 Mai rowa yana alla-alla ya yi arziki

bai san cewa talauci ne ke jiransa ba.

23 Duk wanda ya tsawata wa wani mutum zai sami yabo a ƙarshe

fiye da wanda yake mai daɗin baki.

24 Duk wanda ya yi wa mahaifin ko mahaifiyarsa sata

ya kuma ce, “Ai, ba laifi ba ne”

abokin mai hallakarwa ne shi.

25 Mai haɗama yakan jawo tā-da-na-zaune-tsaye,

amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai yi nasara.

26 Duk mai dogara ga kansa wawa ne,

amma duk wanda yake tafiya da hikima zai zauna lafiya.

27 Duk wanda yake bayarwa ga matalauta ba zai rasa kome ba,

amma duk wanda bai kula da su ba yana samu la’ana masu yawa.

28 Sa’ad da mugu ya samu shugabanci, mutane sukan yi ta ɓuya;

amma sa’ad da mugu ya hallaka, adali kan ci gaba cikin arziki da lafiya.

29:1 Mutumin da ya ci gaba da taurinkai bayan an kwaɓe shi

ba da daɗewa ba zai hallaka ba makawa.

2 Sa’ad da masu adalci suke cin nasara, mutane kan yi farin ciki

sa’ad da mugaye suke mulki, mutane kan yi nishi.

3 Duk mai ƙaunar hikima kan kawo wa mahaifinsa farin ciki,

amma wanda yake ma’amala da karuwai kan lalatar da dukiyarsa.

4 Ta wurin yin adalci sarki kan sa ƙasa tă yi ƙarƙo

amma duk mai haɗama don cin hanci kan rushe ƙasar.

5 Duk wanda yake wa maƙwabcinsa daɗin baki

yana sa wa ƙafafunsa tarko ne.

6 Mugun mutum tarko ne ta wurin zunubinsa,

amma mai adalci zai iya rera ya kuma yi murna.

7 Masu adalci sun damu game da adalci don talakawa,

amma mugaye ba su da wannan damuwa.

8 Masu ba’a kan kuta faɗa a birni,

amma masu hikima sukan kwantar da fushi.

9 In mai hikima ya je wurin shari’a da wawa,

wawa kan yi ta fushi yana ta dariya, ba kuwa za a sami salama ba.

10 Masu kisankai sukan ƙi mutum mai mutunci

su kuma nema su kashe mai aikata gaskiya.

11 Wawa yakan nuna fushinsa a fili,

amma mai hikima kan kanne fushinsa.

12 In mai mulki yana sauraran ƙarairayi,

dukan ma’aikatansa za su zama mugaye.

13 Matalauci da azzalumi suna da wannan abu ɗaya.

Ubangiji ne yake ba dukansu gani.

14 In sarki yana hukunta talakawa da adalci

kursiyinsa kullum zai kasance lafiya.

15 Sandar gyara kan ba da hikima,

amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.

16 Sa’ad da mugaye suke cin nasara, haka zunubi zai yi ta ƙaruwa,

amma masu adalci za su ga fāɗuwar waɗannan mutane.

17 Ka hori ɗanka, zai kuwa ba ka salama;

zai ba ka farin cikin da kake so.

18 Inda ba wahayi, mutane kan kangare;

amma masu albarka ne waɗanda suke kiyaye doka.

19 Ba a yi wa bawa gyara ta wurin magana kawai;

ko da ya fahimta ma, ba zai kula ba.

20 Ka ga mutum mai yin magana da garaje?

To, gara a sa zuciya ga wawa da a sa zuciya gare shi.

21 In mutum ya yi wa bawansa shagwaɓa tun yana yaro,

zai jawo baƙin ciki a ƙarshe.

22 Mutum mai cika fushi yakan tā da faɗa,

mai zafin rai kuma kan yi zunubai masu yawa.

23 Fariyar mutum kan jawo masa ƙasƙanci

amma mai sauƙinkai kan sami girmamawa.

24 Duk wanda yake abokin ɓarawo abokin gāban kansa ne;

yana jin sa yana ta rantsuwa, amma bai isa ya ce kome ba.

25 Jin tsoron mutum tarko ne,

amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai zauna lafiya.

26 Mutane sukan nemi samun farin jini daga wurin sarki,

amma daga wurin Ubangiji ne mutum kan sami adalci.

27 Masu adalci suna ƙyamar masu rashin gaskiya;

mugaye sukan yi ƙyamar masu aikata gaskiya.