Ƙarin Karin Maganar Solomon (continued)

984 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Karin Magana 26–27

1 Kamar ƙanƙara a rani ko ruwan sama a lokacin girbi,

haka girmamawa bai dace da wawa ba.

2 Kamar gwara mai yawo ko alallaka mai firiya,

haka yake da la’anar da ba tă dace tă kama ka ba take.

3 Bulala don doki, linzami don jaki,

sanda kuma don bayan wawaye!

4 Kada ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa,

in ba haka ba kai kanka za ka zama kamar sa.

5 Ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa,

in ba haka ba zai ga kansa mai hikima ne.

6 Kamar datsewar ƙafafun wani ko shan dafi

haka yake da a aika da saƙo ta hannun wawa.

7 Kamar ƙafafun gurgun da suka yi laƙwas

haka karin magana yake a bakin wawa.

8 Kamar ɗaura dutse a majajjawa

haka yake da girmama wawa.

9 Kamar suƙar ƙaya a hannun wanda ya bugu

haka karin magana yake a bakin wawa.

10 Kamar maharbi wanda yake jin wa kowa rauni

haka yake da duk wanda ya yi hayan wawa ko wani mai wucewa.

11 Kamar yadda kare kan koma ga amansa,

haka wawa kan maimaita wautarsa.

12 Gwamma riƙaƙƙen wawa

da mutum mai ganin kansa mai hikima ne.

13 Rago yakan ce, “Akwai zaki a kan hanya,

zaki mai faɗa yana yawo a tituna!”

14 Kamar yadda ƙofa kan juya a ƙyaurensa,

haka rago yake jujjuya a gadonsa.

15 Rago kan sa hannunsa a kwano

ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa.

16 Rago yana gani yana da hikima

fiye da mutane bakwai da suke ba da amsa da dalilai a kan ra’ayinsu.

17 Kamar wani da ya kama kare a kunnuwa

haka yake da mai wucewa da ya tsoma baki a faɗan da ba ruwansa.

18 Kamar yadda mahaukaci yake harbin

cukwimai ko kibiyoyi masu dafi

19 haka yake da mutumin da ya ruɗe maƙwabci

sa’an nan ya ce, “Wasa ne kawai nake yi!”

20 In ba itace wuta takan mutu;

haka kuma in ba mai gulma ba za a yi faɗa ba.

21 Kamar yadda gawayi yake ga murhu, itace kuma ga wuta,

haka mutum mai neman faɗa yake ga faɗa.

22 Kalmomin mai gulma suna kama da burodi mai daɗi;

sukan gangara can cikin cikin mutum.

23 Kamar kaskon da aka dalaye da azurfar da ba a tace ba

haka leɓuna masu mugun zuciya.

24 Mai yin ƙiyayya yakan ɓoye kansa da maganar bakinsa,

amma a cikin zuciyarsa yana cike da munafunci

25 Ko da jawabinsa ya ɗauki hankali, kada ka gaskata shi,

gama abubuwa ƙyama guda bakwai sun cika zuciyarsa.

26 Wataƙila ya ɓoye ƙiyayyarsa da ƙarya,

duk da haka za a tone muguntarsa a cikin taro.

27 In mutum ya haƙa rami, shi zai fāɗi a ciki;

in mutum ya mirgino dutse, dutsen zai mirgine a kansa.

28 Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai,

daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.

27:1 Kada ka yi fariya a kan gobe

gama ba san abin da ranar za tă kawo ba.

2 Ka bar wani ya yabe ka, ba kai kanka ba;

wani dabam, ba leɓunanka ba.

3 Dutse yana da nauyi yashi kuma wahala ce,

amma tsokanar wawa ta fi su duka nauyi.

4 Fushi mugun abu ne mai hallakarwa,

amma wa zai iya tsaya a gaban kishi?

5 Gara tsawatawar da ake yi a fili

da ƙaunar da ake yi a ɓoye.

6 Za a iya amince da rauni daga aboki,

amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi!

7 Duk wanda ya ƙoshi da zuma, ba ya marmarinsa kuma

amma wanda yake yunwa ko abin da yake da ɗaci ma zai ji shi da zaƙi.

8 Kamar tsuntsun da ya ɓace daga sheƙarsa

haka yake da mutumin da ya bar gidansa.

9 Man shafawa mai ƙanshi da kuma turare kan faranta zuciya,

gaisuwar amini kuma takan fito daga shawarar kirki.

10 Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka,

kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka,

gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.

11 Ka zama mai hikima, ɗana, ka kuma faranta mini zuciya;

zan iya amsa kowace irin suƙar da wani zai yi mini.

12 Mai basira kan hango hatsari ya kuma kauce,

marar azanci zai yi ta kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.

13 A karɓe rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo;

a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci.

14 In mutum ya albarkaci maƙwabcinsa da murya mai ƙarfi da sassafe,

za a ɗauka shi a matsayin la’ana.

15 Mace mai fitina kamar

ɗiɗɗigar ruwa take ba ƙaƙƙautawa;

16 hana ta yana kamar yin ƙoƙari tsai da iska ne

ko yin ƙoƙarin cafke mai a tafin hannunka.

17 Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe

haka mutum kan koyi daga mutum.

18 Duk wanda ya lura da itacen ɓaure, zai ci ’ya’yansa,

kuma duk wanda ya lura da maigidansa za a girmama shi.

19 Kamar yadda ruwa kan nuna yadda fuska take,

haka zuciyar mutum kan nuna irin mutumin.

20 Mutuwa da Hallaka ba sa ƙoshi,

haka idanun mutum ba sa ƙoshi da gani.

21 Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta,

amma akan gwada mutum ta wurin yabon da ya samu.

22 Ko da ka daka wawa a turmi,

kana daka shi kamar hatsi da taɓarya,

ba za ka fid da wauta daga gare shi ba.

23 Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka,

ka mai da hankali ga garken shanunka;

24 domin dukiya ba ta dawwama har abada,

ba a kuma kasance da rawani daga tsara zuwa tsara.

25 Sa’ad da aka yanki ingirci sabon toho kuma ya bayyana

aka kuma tattara ciyawa daga tuddai,

26 gashin raguna za su tanada maka tufafi,

za ka iya sayi gonaki masu kyau da kuɗin awaki.

27 Za ka kasance da madarar awaki mai yawa

don ka ciyar da kanka da kuma iyalinka

ka kuma inganta bayinka mata.