Farisiyawa da mutanen Hiridus suna ƙoƙarin sa Yesu cikin tarko game da haraji

Farisiyawa da mutanen Hiridus suna ƙoƙarin sa Yesu cikin tarko game da biyan haraji ga Kaisar.

30 ko 29 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Mattiyu 22:15–22

22:15 Sai Farisiyawa suka yi waje, suka ƙulla yadda za su yi masa tarko cikin maganarsa.

16 Suka aiki almajiransu tare da mutanen Hiridus wurinsa. Suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci, kuma kana koyar da maganar Allah bisa gaskiya. Mutane ba sa ɗaukan hankalinka, domin ba ka kula ko su wane ne ba. 17 To, ka gaya mana, a ra’ayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?”

18 Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, “Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko?

19 Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.” Sai suka kawo masa dinari,

20 sai ya tambaye su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?”

21 Suka amsa, “Na Kaisar ne.”

Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”

22 Da suka ji haka, sai suka yi mamaki. Saboda haka suka ƙyale shi, suka yi tafiyarsu.

Markus 12:13–17

12:13 Daga baya, sai suka tura waɗansu Farisiyawa da mutanen Hiridus zuwa wurin Yesu, domin su sa masa tarko a cikin maganarsa.

14 Suka zo wurinsa suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci. Ba ka bin ra’ayin mutane, don ba ka nuna bambanci. Amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. Daidai ne a biya wa Kaisar haraji, ko babu?

15 Mu biya ko kada mu biya?”

Amma Yesu ya san munafuncinsu, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku kawo mini dinari in ga.”

16 Suka kawo masa kuɗin, sai ya tambaye, su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne wannan?”

Suka ce, “Na Kaisar.”

17 Sai Yesu ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku ba wa Allah kuma abin da yake na Allah.”

Suka yi mamakinsa ƙwarai.

Luka 20:20–26

20:20 Sai suka sa masa ido, suka aiki ’yan leƙen asiri, waɗanda suka nuna kamar su masu gaskiya ne, suna nufin su kama shi game da abin da zai faɗa, domin su ba da shi ga gwamna mai mulki, da mai iko.

21 Sai ’yan leƙen asirin suka tambaye shi, suka ce, “Malam, mun sani kana faɗin, kuma kana koyar da abin da yake daidai, ba ka kuma nuna bambanci, amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya.

22 Daidai ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?”

23 Ya gane makircinsu, sai ya ce musu,

24 “Nuna mini dinari. Hoton wane ne, kuma rubutun wane ne a kai?”

Suka amsa, “Na Kaisar.”

25 Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”

26 Ba su iya kama shi a kan abin da ya faɗa a fili ba. Amsarsa ya ba su mamaki, shi ya sa suka yi shiru.

Tambayar Sadukiyawa mai ɗaure kai game da tashin matattu

Sadukiyawa sun yi wa Yesu tambaya mai rikitarwa game da tashin matattu.

A farfajiyar haikali. (Talata)

Mattiyu 22:23–33

22:23 A ranan nan Sadukiyawa, waɗanda suke cewa babu tashin matattu, suka zo wurinsa da tambaya.

24 Suka ce “Malam, Musa ya faɗa mana cewa in mutum ya mutu ba shi da ’ya’ya, dole ɗan’uwansa yă auri gwauruwar yă kuma haifar wa ɗan’uwan ’ya’ya.

25 A cikinmu an yi ’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu, da yake bai sami ’ya’ya ba, sai ya bar matarsa wa ɗan’uwansa.

26 Haka ya faru da ɗan’uwa na biyu da na uku, har zuwa na bakwai.

27 A ƙarshe, macen ta mutu.

28 To, a tashin matattu, matar wa a cikinsu bakwai ɗin nan za tă zama, da yake dukansu sun aure ta?”

29 Yesu ya amsa ya ce, “Kun ɓata, domin ba ku san Nassi ko ikon Allah ba.

30 Ai, a tashin matattu, mutane ba za su yi aure ko su ba da aure ba; za su zama kamar mala’iku a sama.

31 Amma game da tashi daga matattu na waɗanda suka mutu ba ku karanta abin da Allah ya ce muku ba ne, 32 ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’? Ai, shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne.”

33 Da taro suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.

Markus 12:18–27

12:18 Sa’an nan Sadukiyawa da suke cewa, babu tashin matattu, suka zo masa da tambaya.

19 Suka ce, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, in ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata babu ’ya’ya, dole mutumin ya auri gwauruwar, yă kuma samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya.

20 To, an yi waɗansu ’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu babu ’ya’ya.

21 Na biyun ya auri gwauruwar, sai shi ma ya mutu, babu ’ya’ya. Haka kuma na ukun. 22 A gaskiya, ba ko ɗaya daga cikin bakwai ɗin da ya bar ’ya’ya. Daga ƙarshe, macen ta mutu.

23 To, a tashin matattu, matar wa za tă zama, don duk su bakwai nan sun aure ta?”

24 Yesu ya ce, “Ashe, ba a cikin kuskure kuke ba saboda rashin sanin Nassi, ko ikon Allah?

25 Sa’ad da matattu suka tashi, ba za su yi aure ba, ba kuwa za a ba da su ga aure ba. Za su zama kamar yadda mala’iku suke a cikin sama.

26 Game da tashin matattu kuwa, ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’?

27 Shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne. Kun yi mummunan kuskure!”

Luka 20:27–40

20:27 Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa,

28 “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, ‘In ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata amma ba ’ya’ya, dole mutumin ya aure gwauruwar, ya samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya.’

29 To, an yi waɗansu ’yan’uwa bakwai. Na fari ya auri wata mace, ya mutu ba ’ya’ya.

30 Na biyun, 31 da na ukun suka aure ta. Haka nan dukansu bakwai suka mutu babu ’ya’ya.

32 A ƙarshe, ita macen ma ta mutu.

33 Shin, a tashin matattu, matar wa za tă zama? Tun da su bakwan nan, sun aure ta.”

34 Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure, 35 amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba.

36 Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar mala’iku ne. Su ’ya’yan Allah ne, tun da su ’ya’yan tashin matattu ne.

37 Amma bisa ga labari na bishiya nan, mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, ko Musa ma, ya nuna cewa, matattu suna tashi. Gama ya kira Ubangiji, ‘Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yaƙub.’

38 Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai ne, gama a gare shi, duka na da rai.”

39 Sai waɗansu malaman dokoki suka amsa suka ce, “Ka faɗi daidai, malam!” 40 Kuma ba wanda ya sami ƙarfin halin yin masa waɗansu tambayoyi.