Majalisa Ta Ƙalubalanci Ikon Yesu

Shugabanni (Majalisa) sun ƙalubalanci ikon Yesu a hukumance a matsayinsa na malamin da aka amince da shi (rabbi).

A farfajiyar haikali. (Talata) Ranar muhawara

Yesu ya kafa ikonsa na ɗan Adam a kan Yohanna Mai Baftisma, wanda ya riga shi zuwa, ya kuma yi masa baftisma, sannan ya nemi ra'ayin Majalisa game da baftismar Yohanna. Wannan tambayar mayar da martani mai kaifi ta sa shugabannin Yahudawa suka kasa amsawa, Yesu kuma ya ƙarfafa hujjarsa da misalai uku: (a) misalin 'ya'ya maza biyu; (b) misalin mugayen manoma masu haya; (c) misalin liyafar auren ɗan sarki.

30 ko 29 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Mattiyu 21:23–22:14

21:23 Sai Yesu ya shiga filin haikali, yayinda yake koyarwa, sai manyan firistoci da dattawan mutane suka zo wurinsa suka yi tambaya, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Kuma wa ya ba ka wannan iko?”

24 Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku tambaya guda. In kuka ba ni amsa, ni ma zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa.

25 Baftismar Yohanna, daga ina ta fito? Daga sama ce, ko daga mutane?”

Sai suka tattauna a junansu suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama,’ zai ce, ‘To, me ya sa ba mu gaskata shi ba?’

26 In kuma muka ce, ‘Daga mutane,’ muna tsoron mutane, gama duk sun ɗauka Yohanna annabi ne.”

27 Saboda haka suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.”

Sai ya ce, “Ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”

28 “Me kuka gani? An yi wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza. Sai ya je wajen ɗan farin ya ce, ‘Ɗana, yau tafi gonar inabi ka yi aiki.’

29 “Ya amsa ya ce, ‘Ba zan tafi ba,’ amma daga baya ya sāke tunani, ya tafi.

30 “Sai mahaifin ya tafi waje na biyun ya faɗa masa iri magana guda. Sai ya amsa ya ce, ‘Zan tafi, ranka yă daɗe,’ amma bai tafi ba.

31 “Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?”

Suka amsa, “Na farin.”

Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah. 32 Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo wurinku don yă nuna muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba, amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata. Har ma bayan kun ga wannan, ba ku tuba kun gaskata shi ba.”

33 “Ku saurari wani misali. An yi wani mai gona wanda ya yi gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsin inabi a ciki, ya kuma gina hasumiyar gadi. Sa’an nan ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, ya kuma yi tafiya.

34 Da lokacin girbi ya yi kusa, sai ya aiki bayinsa wajen ’yan hayan, su karɓo masa ’ya’yan inabi.

35 “Amma ’yan hayan suka kama bayinsa; suka dūke ɗaya, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi na ukun.

36 Sai ya sāke aiken waɗansu bayi wurinsu, fiye da na dā yawa, amma ’yan hayan suka yi musu kamar yadda suka yi wa na farin.

37 A ƙarshe, sai ya aiki ɗansa a wurinsu. Ya ce, ‘Za su girmama ɗana.’

38 “Amma da ’yan hayan suka hangi ɗan, sai suka ce wa juna, ‘Wannan shi ne magājin. Ku zo, mu kashe shi, mu ci gādonsa.’

39 Saboda haka suka kama shi, suka jefar da shi bayan katangar gonar inabin, suka kashe shi.

40 “To, idan mai gonar inabin ya zo, me zai yi da ’yan hayan nan?”

41 Suka amsa suka ce, “Zai yi wa banzan mutanen nan mugun kisa, yă ba da hayar gonar inabin ga waɗansu ’yan haya, waɗanda za su ba shi rabonsa na amfanin gona a lokacin girbi.”

42 Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta a cikin Nassi cewa,

“ ‘Dutsen da magina suka ƙi shi

ne ya zama dutsen kusurwar gini.

Ubangiji ne ya aikata wannan,

kuma abin mamaki ne a idanunmu’?

43 “Saboda haka, ina gaya muku cewa za a karɓe mulkin Allah daga gare ku, a ba wa mutanen da za su ba da amfani.

44 Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Amma duk wanda dutsen nan ya fāɗi a kansa, za a murƙushe shi.”

45 Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan Yesu, sai suka gane cewa da su yake.

46 Suka nemi hanyar kama shi, amma suka ji tsoron taron, don mutane sun ɗauka shi annabi ne.

22:1 Yesu ya sāke yin musu magana da misalai, yana cewa, 2 “Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya bikin auren ɗansa. 3 Sai ya aiki bayinsa su kira waɗanda aka gayyata zuwa bikin, amma waɗanda aka ce su zo bikin, suka ƙi zuwa.

4 “Sai ya sāke aiken waɗansu bayi ya ce, ‘Ku ce wa waɗanda aka gayyata cewa na shirya abinci. An yanka bijimai da shanun da aka yi kiwo, kome a shirye yake. Ku zo bikin auren mana.’

5 “Amma ba su kula ba, suka kama gabansu, ɗaya ya tafi gonarsa, ɗaya kuma ya tafi kasuwancinsa. 6 Sauran suka kama bayinsa suka wulaƙanta su, suka kuma kashe su. 7 Sai sarkin ya yi fushi. Ya aiki mayaƙansa suka karkashe masu kisankan nan, aka kuma ƙone birninsu.

8 “Sa’an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin aure fa ya shiryu, sai dai mutanen da na gayyata ba su dace ba. 9 Ku bi titi-titi ku gayyato duk waɗanda kuka gani, su zo bikin.’ 10 Saboda haka bayin suka bi titi-titi, suka tattaro duk mutanen da suka samu, masu kirki da marasa kirki, zauren bikin ya cika makil da baƙi.

11 “Amma da sarkin ya shigo don yă ga baƙin, sai ya ga wani can da ba ya sanye da kayan auren. 12 Ya yi tambaya ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa.

13 “Sai sarkin ya ce wa fadawa, ‘Ku daure shi hannu da ƙafa, ku jefar da shi waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’

14 “Gama kirayayu da yawa, amma zaɓaɓɓu kaɗan ne zaɓaɓɓu.”

Markus 11:27–12:12

11:27 Suka sāke dawowa cikin Urushalima. Da Yesu yana tafiya a filin haikali, sai manyan firistoci, malaman dokoki da kuma dattawa suka zo wurinsa.

28 Suka tambaye, shi suka ce, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Wa kuma ya ba ka ikon yin wannan?”

29 Yesu ya ce, “Zan yi muku tambaya guda. Ku ba ni amsa, ni kuma zan gaya muku, ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa.

30 Baftismar Yohanna, daga sama ce, ko daga mutane? Ku faɗa mini!”

31 Sai suka tattauna a junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai ce, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’

32 In kuma muka ce, ‘Daga wurin mutane ne’; suna jin tsoron mutane, don kowa ya ɗauka cewa, Yohanna, annabi ne na gaskiya.”

33 Saboda haka, suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.”

Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”

12:1 Sa’an nan ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ya shuka gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa rami domin matsin inabin, ya kuma gina ɗakin gadi. Sai ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, sa’an nan ya yi tafiya.

2 Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki wani bawa wajen ’yan hayan, don yă karɓo masa ’ya’yan inabin daga wurinsu.

3 Amma suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hannun wofi.

4 Sai ya sāke aikan wani bawa wurinsu, amma suka bugi wannan mutum a kai, suka wulaƙanta shi.

5 Har yanzu ya sāke aikan wani. Wannan kuwa suka kashe. Ya aika waɗansu da yawa; suka bubbuge waɗansu, sauran kuwa suka kashe.

6 “Sauran mutum ɗaya da ya rage ya aika, ɗa, da yake ƙauna. Daga ƙarshe sai ya aike shi, yana cewa, ‘Za su girmama ɗana.’

7 “Amma ’yan hayan suka ce wa juna, ‘Aha! Wannan shi ne magājin. Ku zo mu kashe shi, gādon kuma yă zama namu.’

8 Sai suka kama shi suka kashe, suka jefa shi bayan gonar inabin.

9 “To, me, mai gonar inabin zai yi ke nan? Zai zo yă karkashe dukan ’yan hayan nan, ya kuma ba wa waɗansu gonar inabin.

10 Ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba,

“ ‘Dutsen da magina suka ƙi,

shi ne kuwa ya zama dutsen kusurwan gini.

11 Ubangiji ya yi wannan,

ya kuma yi kyau a idanunmu’?”

12 Sai manyan Firistoci da malaman dokoki da shugabanni suka nemi hanyar da za su kama shi, domin sun gane ya yi misalin a kansu ne. Amma suka ji tsoron taron, saboda haka suka bar shi suka yi tafiyarsu.

Luka 20:1–19

20:1 Wata rana da Yesu yana koyar da mutane, yana musu wa’azin bishara a filin haikalin, sai manyan firistoci da malaman dokoki, tare da dattawan suka zo wurinsa.

2 Suka ce masa, “Gaya mana, da wane iko kake yin waɗannan abubuwa. Wa ya ba ka wannan ikon?”

3 Ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku faɗa mini, 4 baftismar Yohanna, daga sama ne ta fito, ko kuwa daga wurin mutane ne?”

5 Sai suka yi shawara da junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai tambaya, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’

6 Amma in kuma muka ce, ‘Daga mutane ne,’ dukan mutanen za su jajjefe mu da duwatsu, domin sun tabbata cewa, Yohanna annabi ne.”

7 Don haka, sai suka amsa cewa, “Ba mu san inda ta fito ba.”

8 Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku, ko da wane iko ne, nake yin waɗannan abubuwa ba.”

9 Sai ya ci gaba da gaya wa mutanen wannan misali ya ce, “Wani mutum ya yi gonar inabi, sai ya ba da hayarta ga waɗansu manoma, sa’an nan ya yi wata doguwar tafiya.

10 A lokacin girbi, sai ya aiki bawa zuwa wurin masu hayan, don su ba shi daga cikin ’ya’yan inabin. Amma ’yan hayan suka yi wa bawan nan dūka, suka kore shi hannu wofi.

11 Ya sāke aikan wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka kunyata shi, suka kuma kore shi hannu wofi.

12 Har yanzu, ya sāke aikan na uku, amma suka ji masa rauni, suka jefar da shi waje.

13 “Sai mai gonar inabin ya ce, ‘Me zan yi? Zan aiki ɗana da nake ƙauna, wataƙila za su girmama shi.’

14 “Amma da ’yan hayan suka gan shi, sai suka tattauna zancen, suka ce, ‘Wannan shi ne magājin, mu kashe shi sa’an nan gādon zai zama namu!’

15 Sai suka fitar da shi waje, suka kashe shi.

“To, me mai gonar inabin zai yi da su?

16 Zai zo ya karkashe masu hayan nan, ya ba wa waɗansu gonar inabin.”

Da mutanen suka ji wannan, sai suka ce, “Allah ya sawwaƙa!”

17 Yesu ya zura musu ido ya ce, “To, mene ne ma’anar abin da aka rubuta cewa,

“ ‘Dutsen da magina suka ƙi,

shi ne kuwa ya zama dutsen kan ginin’

18 Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Kuma in dutsen nan ya fāɗi a kan wani, zai murƙushe shi.”

19 Malaman dokoki da manyan firistoci, suka nemi hanyar kama shi nan da nan, domin sun san cewa, ya yi wannan misali a kansu ne, amma suna jin tsoron mutane.