Wani Bafarisiye Masanin Doka Ya Tambayi Yesu
Farisiyawa sun yi murna da shan kayen Sadukiyawa, sai wani masanin doka wanda yake Bafarisiye ya yi wa Yesu tambaya game da Doka.
A farfajiyar haikali. (Talata)
30 ko 29 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Mattiyu 22:34–40
22:34 Da jin Yesu ya ƙure Sadukiyawa, sai Farisiyawa suka tattaru. 35 Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Doka, ya gwada shi da wannan tambaya.
36 “Malam, wace doka ce mafi girma a cikin dokoki?”
37 Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’
38 Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma. 39 Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ 40 Dukan Doka da Annabawa suna rataya ne a kan waɗannan dokoki biyu.”
Markus 12:28–34
12:28 Wani daga cikin malaman dokoki ya zo ya ji suna muhawwara. Da ya lura cewa Yesu ya amsa musu daidai, sai ya tambaye shi ya ce, “A cikin dukan dokoki, wacce ta fi girma duka?”
29 Yesu ya ce, “Wadda ta fi girma duka, ita ce wannan. ‘Ku saurara, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.
30 Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’
31 Na biyun ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ Ba wata doka da ta fi waɗannan.”
32 Mutumin ya ce, “Malam, ka faɗi daidai. Daidai ne da ka ce, Allah ɗaya ne, babu kuma wani sai shi. 33 Nuna ƙauna ga Allah da dukan zuciyarka, da dukan ganewarka, da dukan ƙarfinka, da kuma nuna ƙauna ga maƙwabcinka kamar kanka, ya fi dukan hadayun ƙonawa da sadakoki.”
34 Da Yesu ya ga ya amsa da hikima, sai ya ce masa, “Ba ka da nisa da mulkin Allah.” Daga lokacin, ba wanda ya yi karambani yin masa wata tambaya.
Yesu Ya Rufe Bakin Maƙiyansa Game da Ɗan Dawuda
Abin farin ciki ga taron jama'a, Yesu ya rufe bakin maƙiyansa da tambaya mai kaifi game da yadda Almasihu ya fito daga zuriyar Dawuda, amma duk da haka shi ne Ubangijin Dawuda.
A farfajiyar haikali. (Talata)
Mattiyu 22:41–46
22:41 Yayinda Farisiyawa suke a tattare wuri ɗaya, sai Yesu ya tambaye su,
42 “Me kuke tsammani game da Kiristi? Ɗan wane ne shi?”
Suka amsa suka ce, “Ɗan Dawuda.”
43 Ya ce musu, “To, ta yaya Dawuda ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya kira shi ‘Ubangiji’? Gama ya ce,
44 “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
“Zauna a hannun damana,
sai na sa abokan gābanka
su zama matashin sawunka.” ’
45 To, in Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji,’ yaya zai zama ɗansa?” 46 Ba wanda ya iya tanka masa, daga wannan rana kuwa ba wanda ya sāke yin karambanin yin masa wata tambaya.
Markus 12:35–37
12:35 Yayinda Yesu yake koyarwa a filin haikalin, sai ya yi tambaya ya ce, “Yaya malaman dokoki suke cewa Kiristi ɗan Dawuda ne?
36 Dawuda da kansa ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce,
“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
“Zauna a hannun damana
sai na sa abokan gābanka
a ƙarƙashin sawunka.” ’
37 Dawuda da kansa ya kira shi ‘Ubangiji.’ To, ta yaya zai zama ɗansa?”
Taro mai yawa suka saurare shi da murna.
Luka 20:41–44
20:41 Sai Yesu ya ce musu, “Yaya suke cewa, ‘Kiristi ɗan Dawuda ne?’
42 Dawuda da kansa ya faɗa a cikin Zabura,
“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
“Zauna a hannun damana,
43 sai na sa abokan gābanka
su zama matashin sawunka.” ’
44 Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji.’ Ta, yaya zai zama ɗansa?”