Bulus Ya Sake Rubuta Wa Timoti

Bulus, yana tsammanin mutuwa ta kusa, ya rubuta wasiƙarsa ta biyu zuwa ga Timoti. A matsayin wasiyyarsa ta ƙarshe, yana ƙarfafa Timoti ya yi aikinsa da aminci a kowane lokaci na ridda, tsanantawa da rarrabuwar kai.

65 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bulus Ya Sake Gaishe da Timoti 65 ko 66 bayan haihuwar Almasihu

A farkon wasiƙarsa, Bulus ya tabbatar da ikonsa a matsayin manzo, ya kuma bayyana cewa yana begen rai madawwami ta wurin Yesu Kiristi, ba ta wurin Shari’ar Musa ba.

2 Timoti 1:1–2

1 Bulus, manzon Kiristi Yesu ta wurin nufin Allah, bisa ga alkawarin rai wanda yake cikin Kiristi Yesu,

2 Zuwa ga Timoti, ƙaunataccen ɗana.

Alheri, jinƙai da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Ubangijinmu, su kasance tare da kai.

Bulus Yana Godiya ga Allah Saboda Bangaskiyar Timoti

Bulus yana gode wa Allah, wanda yake bauta masa kamar yadda kakanninsa suka yi, domin koyaushe yana tuna da Timoti a addu’o’insa. Yana tuna hawayen Timoti sa’ad da suka rabu, ko kuma, kamar yadda wasu suke zato, sa’ad da Bulus ya koya masa bangaskiyar Kirista. Yana kuma gode wa Allah saboda bangaskiyar Timoti ta gaskiya, wadda ya karɓa daga kakanninsa. Yana kiransa ya haɓaka baiwoyin Ruhu Mai Tsarki ta wurin amfani da su wajen kāre bishara a duk lokacin da ya dace. Domin tun da Kiristi ya ba mabiyansa masu aminci ruhun ƙarfin hali da hikima, bai kamata Timoti ya ji kunyar gaskiya, wadda ita ce shaidar Kiristi, ko kunyar Bulus, fursunansa ba (kamar yadda malaman da suke son a bi tsarin Yahudanci suka yi), sai dai ya yi tarayya cikin shan wahala saboda bishara gwargwadon ikon da aka ba shi. Allah, bayan ya ceci dukan ’yan Adam daga halakar zunubi, ya gayyace su su zama zaɓaɓɓun mutanensa, ta wurin alherinsa da tagomashinsa na kyauta, wanda aka ƙaddara tun farkon duniya amma yanzu aka bayyana ta wurin Yesu Kiristi. Kiristi ya kawar da ikon mutuwa, ta wurin rai madawwami na kurwa bayan mutuwa da rashin ruɓewar jiki bayan tashin matattu, abubuwan da aka nuna a cikinsa. Bulus yana magana game da naɗin da Allah ya yi masa a matsayin manzo, domin ya koya wa Al’ummai koyarwar ceto. Tsanantawar da ya sha a dā da wadda yake sha yanzu saboda wannan ba su girgiza bangaskiyarsa ga Kiristi ba.

2 Timoti 1:3–12

3 Na gode wa Allah wanda nake bauta wa, kamar yadda kakanni-kakannina suka yi da lamiri mai tsabta, yadda kullum dare da rana ina tuna da ku a cikin addu’o’ina. 4 Sa’ad da na tuna da hawayenka, nakan yi marmarin ganinka, don in cika da farin ciki. 5 An tunashe ni da sahihiyar bangaskiyarka, wadda a farko ta kasance a cikin kakarka Loyis da kuma mahaifiyarka Yunis yanzu kuwa na tabbata tana cikinka.

6 Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwan nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗibiya maka hannuwana. 7 Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai. 8 Saboda haka kada ka ji kunyar ba da shaida game da Ubangijinmu, ko kuwa ka ji kunyata, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi. Sai dai ka haɗa kai tare da ni cikin shan wahala saboda bishara ta wurin ikon Allah, 9 wanda ya cece mu ya kuma kira mu ga rayuwar tsarki ba saboda wani abin da muka yi ba sai dai saboda nufinsa da kuma alherinsa. An ba mu wannan alheri cikin Kiristi Yesu tun fil azal, 10 amma yanzu an bayyana ta ta wurin bayyanuwar Mai Cetonmu, Kiristi Yesu, wanda ya hallaka mutuwa ya kuma kawo rai da rashin mutuwa a sarari ta wurin bishara. 11 A wannan bishara ce, aka naɗa ni mai shela da manzo da kuma malami. 12 Shi ya sa nake shan wahalar da nake sha. Duk da haka ba na jin kunya, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata cewa yana iya kiyaye abin da na danƙa masa amana don wancan rana.

Ka Kāre Bishara, Ka Yi Hidima Kamar Soja

Bulus yana ƙarfafa Timoti, a cikin haɗarurruka da hamayya, ya riƙe shirin ceto da ya karɓa daga gare shi da ƙarfi, ta wurin bangaskiya ga Kiristi da ƙaunarsa. Ta wurin Ruhu Mai Tsarki da ke cikinsa, zai kiyaye bisharar da aka danƙa masa da tsarki, ba tare da gurɓatar da ita da koyarwar ƙarya ba. Bulus ya nuna bukatar tsayawa daram cikin bangaskiya ta wurin ba da labarin yadda Kiristoci da yawa a Asiya suka juya masa baya saboda wulakancinsa da wahalarsa (2 Timoti 4:16). Yana addu’a a sāka wa Onesiforus saboda alherinsa, shi da ya ci gaba da amincewa da shi kuma ya yi masa hidima a kurkuku, ya kuma sami jinƙai daga Ubangiji Yesu a ranar shari’a. Bulus kuma yana ƙarfafa Timoti ya yi ƙarfi cikin alheri, ya kuma danƙa gaskiyar da ya karɓa daga Bulus, wadda shaidu da yawa suka tabbatar, ga maza waɗanda aka gwada amincinsu, domin bayan tafiyar Bulus su ma su iya koya wa waɗansu. Kamar soja na gaske, ya nisanci shagulgulan duniya, domin ya keɓe kansa ga hidimar Kiristi. Gama wanda yake shiga gasar wasannin jama’a ba ya samun rawani sai ya yi gasa bisa ƙa’idoji. Dole manomi ya fara aiki kafin ya sami rabo daga amfanin ƙasa. Haka kuma dole mai hidima na Kirista ya yi aikinsa yadda Kiristi ya tsara, ya yi aiki a gonar inabinsa ta ruhaniya kafin ya karɓi ladan da aka yi alkawari. Bulus yana roƙonsa ya yi tunani sosai a kan waɗannan abubuwa, yana kuma addu’a Ubangiji ya ba shi fahimta a dukan al’amuran addini.

2 Timoti 1:13–2:7

13 Abin da ka ji daga gare ni, ka kiyaye shi kamar tsarin sahihiyar koyarwa, cikin bangaskiya da ƙauna cikin Kiristi Yesu. 14 Ka kiyaye kyakkyawar ajiyan nan da aka danƙa maka amana, ka lura da ita da taimakon Ruhu Mai Tsarki wanda yake raye a cikinmu.

15 Ka san cewa kowa a lardin Asiya ya juya mini baya, har da Figelus da Hermogenes.

16 Bari Ubangiji yă yi wa iyalin Onesiforus jinƙai, domin sau da dama yakan wartsakar da ni, bai kuma ji kunyar sarƙoƙina ba. 17 A maimakon haka ma, sa’ad da yake a Roma, ya neme ni ido a rufe sai da ya same ni. 18 Bari Ubangiji yă sa yă sami jinƙai daga Ubangiji a wancan ranar! Ka sani sarai yadda ya taimake ni a hanyoyi dabam-dabam a Afisa.

2:1 Kai kuma, ɗana, ka yi ƙarfi cikin alherin da yake cikin Kiristi Yesu. 2 Abubuwan da ka ji na faɗa a gaban shaidu masu yawa kuwa ka danƙa wa amintattun mutane waɗanda su ma za su iya koya wa waɗansu. 3 Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu. 4 Ba wanda yake aikin soja da zai sa kansa a sha’anin mutumin da ba ya aikin soja, domin yakan so yă gamshi wanda ya ɗauke shi soja. 5 Haka ma, in wani ya yi gasa a matsayi shi ɗan wasa ne, ba ya sami rawanin nasara, sai in ya yi gasar bisa ga dokoki. 6 Manomi mai aiki sosai ya kamata yă zama na fari wajen samun rabon amfanin gona. 7 Ka yi tunani a kan abin da nake faɗi, gama Ubangiji zai ba ka ganewa cikin dukan wannan.

Tashin Matattu Shi Ne Tushen Bishara

Bulus yana roƙon Timoti ya tuna cewa koyarwar da take tushen bishara ita ce tashin Yesu daga matattu cikin jikinsa na ɗan Adam, saɓanin koyarwar Himenayus da Filetus, waɗanda suka yi wa’azin tashin matattu na misali kawai (2 Timoti 2:18). Yanzu Bulus yana shan wahala cikin sarƙoƙi kamar mai laifi saboda bishara. Amma da yake maƙiyansa ba za su iya ɗaure bishara da sarƙoƙi ba, yana jimre wa dukan abubuwa da haƙuri saboda Al’ummai, domin su ma su sami albarkun ceto. Gama tabbas ne waɗanda suka mutu tare da Kiristi cikin jiki za su kuma rayu tare da shi cikin ɗaukaka, waɗanda kuma suka sha wahala tare da shi za su yi mulki tare da shi; amma waɗanda suka yi musunsa saboda tsoro, shi ma zai yi musunsu a ranar shari’a. Gama ko da mutum bai da aminci, Allah yana nan mai aminci ga dukan alkawuransa da gargaɗinsa, kuma ba zai iya yin abin da ya saɓa wa kansa ba.

2 Timoti 2:8–13

8 Ka tuna da Yesu Kiristi, wanda aka tā da shi daga matattu, zuriyar Dawuda, wanda shi ne bisharata, 9 wadda nake shan wahala har ga daurin sarƙa kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a daure take ba. 10 Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka.

11 Ga wata magana tabbatacciya,

“In muka mutu tare da shi,

za mu rayu tare da shi;

12 in muka jimre,

za mu yi mulki tare da shi.

In muka yi mūsunsa,

shi ma zai yi mūsunmu;

13 in ba mu da aminci,

shi dai mai aminci ne,

domin shi ba zai iya mūsun kansa ba.”

Malamai Kamar Kayan Amfani na Daraja da na Rashin Daraja

Bulus ya umarci Timoti ya tunasar da Afisawa waɗannan manyan dalilan riƙe aminci, yana gargaɗinsu kamar a gaban Kiristi kada su yi jayayya game da kalmomi. Shi kansa Timoti ya zama ma’aikacin da Allah ya amince da shi, yana amfani da maganar gaskiya yadda kowane yanayi yake buƙata, yana kuma ƙin dukan maganganun rashin tsoron Allah da marasa amfani, waɗanda suke ƙara rashin tsoron Allah kuma suke halakar da rai kamar yadda cutar ruɓewar nama take lalata jiki. Irin waɗannan su ne koyarwar Himenayus da Filetus, waɗanda suka kauce nesa da gaskiya, suna cewa tashin matattu ya riga ya faru sa’ad da mutane suka ba da gaskiya. Duk da waɗannan riddoji, an gina ikilisiyar Allah a kan tushen manzanni (Afisawa 2:20), kuma ikonsu yana nan daram, yana ɗauke da wannan rubutu (Ƙidaya 16:5, 26). Wannan yana nufin cewa nisantar irin waɗannan mugayen malamai ya zama dole domin kāriyar Afisawa, kamar yadda nisantar tantunan Kora da abokansa ya zama dole ga Isra’ilawa idan suna so su kuɓuta daga hukuncin da zai sami waɗannan mutane. A gidan babban mutum akwai tasoshin zinariya da azurfa, da na itace da yumɓu, waɗansu don amfani na daraja, waɗansu kuma don amfani marar daraja. Haka kuma a gidan Allah, wato ikilisiyarsa, akwai malamai iri dabam-dabam: waɗansu suna aikin hidima mai daraja, waɗansu kuma suna aikin marar daraja na ɓatar da mutane. Duk wanda ya tsarkake kansa daga irin wannan gurɓatawa zai zama tasar daraja, wadda aka keɓe, mai amfani ga Allah, wanda yake shugaban ikilisiyar Kirista.

2 Timoti 2:14–21

14 Ka riƙa tuna masu da haka, ka kuma gama su da Allah, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi. 15 Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai. 16 Ka yi nesa da maganganun banza na rashin tsoron Allah, gama waɗanda suka mai da hankali ga yin waɗannan za su ƙara zama marasa tsoron Allah. 17 Koyarwarsu za tă bazu kamar ruɓaɓɓen gyambo. A cikinsu akwai Himenayus da Filetus, 18 waɗanda suka bauɗe daga gaskiya. Suna cewa tashin matattu ya riga ya faru, suna kuma ɓata bangaskiyar waɗansu. 19 Duk da haka, ƙaƙƙarfan tushen nan na Allah yana nan daram, an hatimce shi da wannan rubutu, “Ubangiji ya san waɗanda suke nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, dole yă yi nesa da aikata mugunta.”

20 A babban gida akwai kayayyakin da ba na zinariya da na azurfa kaɗai ba, amma har da na katako da na yumɓu ma; waɗansu domin hidima mai daraja waɗansu kuwa domin hidima marar daraja. 21 In mutum ya tsabtacce kansa daga na farkon zai zama kayan aikin hidima mai daraja, mai amfani ga Maigida, kuma shiryayye domin yin kowane aiki mai kyau.

Timoti Ya Guje wa Sha’awoyin Ƙuruciya

Domin Timoti ya zama kayan amfani da aka keɓe don Allah, Bulus yana ƙarfafa shi ya nisanci dukan sha’awoyin ƙuruciya, da tsananin kwaɗayin matsayi da iko, ya kuma himmantu ga neman adalci, aminci, ƙaunar Allah da mutane, da zaman lafiya da kowa, musamman waɗanda suke da tsarkakakkiyar niyya ta ɗaukaka sunan Allah. Ya ƙi ra’ayoyi da ayyukan wauta na masu nacewa a tilasta bin al’adun Yahudawa. Kada ya yi amfani da hanyoyin tashin hankali, sai dai ya zama mai tausayi, yana aikata kyawawan halayen da yake yabawa, yana kuma koya wa masu hamayya da shi cikin tawali’u, ko wataƙila ta wurin alherin Allah su kai ga amincewa da gaskiya. Ta haka, bayan bawan Allah ya kuɓutar da su da rai daga tarkunan Iblis, wato kurakurai da bin sha’awoyin jiki na masu nacewa a tilasta bin al’adun Yahudawa, za a iya kiyaye su daga hallaka, su kuma farka daga buguwar zunubi, domin su ga haɗarin da suke ciki, su san nufin Allah kuma su aikata shi.

2 Timoti 2:22–26

22 Ka yi nesa da mugayen sha’awace-sha’awace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta. 23 Kada wani abu yă haɗa ka da gardandamin banza da wofi, domin ka san yadda suke jawo faɗa. 24 Bai kamata bawan Ubangiji yă zama mai neman faɗa ba; a maimako, dole yă nuna alheri ga kowa, mai iya koyarwa, mai haƙuri kuma. 25 Waɗanda suke gāba da shi kuwa dole yă yi musu gargaɗi cikin hankali, da fata Allah zai sa su tuba su kai ga sanin gaskiya, 26 su kuma dawo cikin hankulansu su kuɓuta daga tarkon Iblis, wanda ya sa suka zama kamammu don su aikata nufinsa.