Bulus Ya Rubuta wa Korintiyawa

Bulus ya rubuta wasiƙarsa ta farko zuwa ga Korintiyawa domin ya tabbatar da ikonsa a matsayin manzo, ya tsauta wa rashin bin ƙa'ida da hargitsin da ke cikin ikilisiya, ya kuma amsa tambayoyin waɗanda suka tuba a kan batutuwa dabam-dabam na koyarwa da ladabtarwa.

57 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bulus Ya Gaishe da Korintiyawa

Gabatarwar Bulus, inda ya tabbatar da manzancinsa da haɗin kan waɗanda suka gaskata da Kiristi Yesu.

1 Korintiyawa 1:1–3

1 Bulus, wanda aka kira domin yă zama manzon Kiristi Yesu, bisa ga nufin Allah, da kuma ɗan’uwanmu Sostenes,

2 Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, da waɗanda aka tsarkake cikin Kiristi Yesu, aka kuma kira domin su zama masu tsarki, tare da dukan waɗanda suke ko’ina da suke kiran sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, Ubangijinsu da kuma namu.

3 Alheri da salama daga Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

Bulus Ya Yi Farin Ciki da Juyowarsu Zuwa ga Bangaskiya da Baiwowinsu

Bulus ya yi farin ciki da juyowarsu zuwa ga bangaskiya da kuma baiwowin ruhaniya da suka karɓa a matsayin shaida ga gaskiyar Kiristi.

1 Korintiyawa 1:4–9

4 Ina gode wa Allah kullum dominku, saboda alherinsa da aka ba ku a cikin Kiristi Yesu. 5 Gama a cikinsa kuka sami wadata ta kowace hanya, a cikin dukan maganarku, da kuma cikin dukan saninku 6 gama shaidarmu game da Kiristi ta tabbata a cikinku. 7 Saboda haka, ba ku rasa kowace baiwa ta ruhaniya ba, yayinda kuke jira da marmari, saboda bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi. 8 Zai ƙarfafa ku har zuwa ƙarshe, domin ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Kiristi. 9 Allah, wanda ya kira ku zuwa ga zumunci tare da Ɗansa Yesu Kiristi Ubangijinmu, shi mai aminci ne.

Bulus Ya Ƙarfafa Haɗin Kai, Ba Ƙungiyoyi Ba

Bulus ya ƙarfafa su su kasance da haɗin kai cikin sunan Yesu Kiristi, wanda babu rarrabuwa a cikinsa, maimakon su bi shugabannin da su mabiyan suka yi rajista a ƙarƙashin sunayensu.

1 Korintiyawa 1:10–17

10 Ina roƙonku ’yan’uwa, a cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, dukanku ku yarda da juna, domin kada a sami tsattsaguwa a cikinku, domin kuma ku zama ɗaya, cikakku a cikin halinku da tunaninku. 11 ’Yan’uwana, waɗansu daga iyalin gidan Kulos sun gaya mini cewa, akwai faɗa a cikinku. 12 Abin da nake nufi shi ne, ɗaya daga cikinku na cewa, “Ni ina bin Bulus,” wani na cewa, “Ni ina bin Afollos,” wani kuma, “Ni ina bin Kefas,” har wa yau wani kuma, “Ni ina bin Kiristi.”

13 Kiristi a rabe ne? Bulus ne aka gicciye dominku? An yi muku baftisma a cikin sunan Bulus ne? 14 Ina godiya domin ban yi wa wani baftisma a cikinku ba, sai dai Kirisbus da Gayus kaɗai. 15 Don haka, ba wanda na iya cewa an yi muku baftisma a cikin sunana. 16 (I, na kuma yi wa iyalin gidan Istifanas baftisma, ban da wannan, ban tuna da wani da na yi masa baftisma ba.) 17 Gama Kiristi bai aike ni yin baftisma ba, sai dai wa’azin bishara ba da kalmomin hikimar mutum ba, domin kada gicciyen Kiristi ya rasa ikonsa.

Gicciye Ya Fi Hikimar Ɗan Adam

Bulus ya tabbatar cewa an aike shi ya yi wa'azin bishara ba da ƙwarewar magana ta ilimi da fasaha ba, domin kada a ƙyale ikon Allah. Ya bayyana cewa ba a iya gano gaskiyar bishara ta hikimar ɗan Adam ko ilimi. Ko da yake wa'azin gicciye yana zama kamar wauta ga waɗanda ba su gaskata ba, ya fi hikimar mutane, kuma shi ne ikon Allah don ceto ga mutumin Yahuda da mutumin Hellenawa waɗanda suka tuba. Allah ya zaɓi waɗanda aka fi rainawa cikin mutane domin ya kunyatar da masana falsafa masu ilimi da manyan mutanen Yahudawa, waɗanda suka yi gāba da hikimar bishara. Ta hanyar kwatantawa ya nuna yadda duk nasarorin ɗan Adam suke ƙasa, domin kada kowa ya yi fahariya sai cikin Ubangiji.

1 Korintiyawa 1:18–31

18 Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne. 19 Gama a rubuce yake cewa,

“Zan rushe hikimar mai hikima,

basirar mai azanci kuma zan rikita shi.”

20 Ina mai hikima? Ina mai zurfin bincike? Ina masana na wannan zamani? Ashe, Allah bai wofinta hikimar duniya ba? 21 Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara. 22 Yahudawa suna so su ga alama, Hellenawa kuma suna neman hikima, 23 amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai, 24 amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah. 25 Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum.

26 ’Yan’uwa, ku tuna yadda kuke sa’ad da aka kira ku. Babu masu hikima da yawa a cikinku, bisa ga ganin mutum; babu masu iko da yawa, babu masu martaba da yawa bisa ga haihuwa. 27 Amma Allah ya zaɓi abubuwa masu wautata duniya, don yă kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abubuwa marasa ƙarfi na duniya, domin ya ba wa masu ƙarfi kunya. 28 Ya zaɓi abubuwa marasa martaba na wannan duniya da kuma abubuwan da aka rena da abubuwan da ba a ɗauka a bakin kome ba, domin a wofinta abubuwan da ake ganinsu da daraja, 29 domin kada wani ya yi taƙama a gabansa. 30 Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu. 31 Saboda haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Duk wanda yake taƙama, ya yi taƙama a cikin Ubangiji.”

Bulus Ya Yi Wa'azi Ba Tare da Ƙwarewar Maganar Ɗan Adam Ba

Bulus ya bayyana cewa sa'ad da ya yi musu wa'azin bishara, ba kamar malamansu na ƙarya ba, bai ƙawata ta da ilimin ɗan Adam ko ƙwarewar magana ba. Hujjojinsa sun fito ne daga shaidar wahayi daga Allah, wanda ikon mu'ujizai ya tabbatar. Saboda haka kada bangaskiyarsu ta dogara ga hikima ko falsafar mutane.

1 Korintiyawa 2:1–5

1 Da na zo wurinku ’yan’uwa, ban zo da iya magana ko wani mafificin hikima yayinda na yi muku shelar shaida game da Allah ba. 2 Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye. 3 Na zo wurinku cikin rashin ƙarfi da tsoro, da rawan jiki ƙwarai. 4 Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu, 5 domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah.

Hikimar Allah da Aka Ɓoye Ta Bayyana ta Wurin Ruhu

Daga nan Bulus ya nuna cewa, ko da yake ba ya amfani da hikimar duniya, Korintiyawa ba su da dalilin yin fahariya da malamansu na ƙarya. Domin yana faɗin ɓoyayyen asirin Allah da Ruhu ya bayyana masa, wanda babu ƙoƙarin ɗan Adam ko nazari da zai iya kaiwa gare shi. Ta wurin wa'azin Ruhu Mai Tsarki yana bayyana musu zurfafan al'amuran Allah, waɗanda Ruhu na Allah kaɗai zai iya bayyana. Ko ma karɓarsu mutum na ɗabi'a, wanda ba na ruhaniya ba ne, ba zai iya yi ba, domin ba shi da wani taimako sai iyawarsa ta ɗan Adam.

1 Korintiyawa 2:6–16

6 Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba. 7 A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai. 8 Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba. 9 Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Ba idon da ya taɓa gani,

ba kunnen da ya taɓa ji,

ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin

abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”

10 Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa.

Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah. 11 Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah. 12 Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake. 13 Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya. 14 Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu. 15 Mutumin ruhaniya yakan gwada dukan abubuwa, amma shi kansa ba ya ƙarƙashin shari’ar mutum.

16 “Wa ya taɓa sanin hankalin Ubangiji,

har da zai koya masa?”

Amma muna da tunani iri na Kiristi ne.