Sashe na 5: Tafiyar Bulus ta Uku ta Wa'azi
Bulus Ya Sake Ziyartar Galatiya da Firjiya
Bulus ya sake barin Antiyok domin ya ziyarci ikilisiyoyin Galatiya da Firjiya.
55 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
23 Bayan ya yi ’yan kwanaki a Antiyok, Bulus ya tashi daga can ya zaga ko’ina a yankin Galatiya da Firjiya, yana ƙarfafa dukan almajirai.
Afollos Ya Yi Wa'azi a Afisa
Labarin Afollos, wanda a wannan lokaci yake yi wa ikilisiyar da Bulus ya kafa a Afisa wa'azi.
24 Ana cikin haka sai wani mutumin Yahuda mai suna Afollos, ɗan ƙasar Alekzandariya, ya zo Afisa. Shi masani ne, yana da cikakken sani na Nassosi. 25 An horar da shi a hanyar Ubangiji, ya kuma himma ƙwarai a magana, ya kuma yi koyarwa game da Yesu, daidai, ko da yake baftismar Yohanna ce kaɗai ya sani. 26 Sai ya fara magana gabagadi a majami’a. Sa’ad da Firiskila da Akwila suka ji shi, sai suka gayyace shi gidansu suka ƙara bayyana masa hanyar Allah sosai.
27 Sa’ad da Afollos ya so ya tafi Akayya, sai ’yan’uwa suka ƙarfafa shi suka kuma rubuta wa almajiran da suke can da su marabce shi. Da isowarsa, ya zama da taimako ƙwarai ga waɗanda ta wurin alheri suka gaskata. 28 Gama da ƙwazo ya ƙaryata Yahudawa a muhawwara a fili, yana tabbatar daga Nassosi cewa Yesu shi ne Kiristi.
Daga Firjiya zuwa Afisa
Bulus ya ci gaba daga Firjiya zuwa Afisa, ya kuma tattauna da Yahudawa a can.
1 Lokacin da Afollos yake a Korint, Bulus ya bi hanyar da ta ratsa ta Asiya ya zo Afisa. A can ya sadu da waɗansu almajirai, 2 sai ya tambaye, su ya ce, “Kun karɓi Ruhu Mai Tsarki sa’ad da kuka gaskata?”
Suka amsa suka ce, “A’a, ba mu ma san akwai Ruhu Mai Tsarki ba.”
3 Saboda haka Bulus ya yi tambaya ya ce, “To, wace baftisma aka yi muku?”
Suka ce, “Baftismar Yohanna.”
4 Bulus ya ce, “Ai, baftismar Yohanna, baftisma ce ta tuba. Ya ce wa mutane su gaskata a wani wanda yake zuwa bayansa, wato, Yesu.” 5 Da ji wannan, sai aka yi musu baftisma a cikin sunan Ubangiji Yesu. 6 Da Bulus ya ɗibiya musu hannuwansa, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka musu, suka kuwa yi magana da harsuna, suka kuma yi annabci. 7 Mutane kuwa su wajen mutum goma sha biyu ne.
8 Bulus ya shiga majami’a ya yi magana gabagadi a can na watanni uku, yana muhawwara yana kuma rinjayarsu game da mulkin Allah. 9 Amma waɗansunsu suka taurara; suka ƙi su gaskata kuma a gaban jama’a suka yi baƙar magana game da Hanyar. Bulus kuwa ya bar su. Ya tafi tare da almajirai ya dinga tattaunawa da su kullum a babban ɗakin jawabi na Tirannus. 10 Wannan ya ci gaba har shekara biyu, sai da ya sa dukan Yahudawa da Hellenawa da suke zaune a lardin Asiya suka ji maganar Ubangiji.
An Ƙone Littattafan Sihiri a Afisa 56 bayan haihuwar Almasihu
Bulus ya zauna shekara biyu a Afisa. Mutanen sun ƙone littattafansu na sihiri.
11 Allah ya yi ayyukan banmamakin da suka wuce misali ta hannu Bulus, 12 har ma ana kai hankicif da adikan da suka taɓa jikinsa wa marasa lafiya, suka kuwa warke daga cututtukansu mugayen ruhohi kuma suka rabu da su.
13 Waɗansu Yahudawa masu yawo gari-gari suna fitar da mugayen ruhohi suka yi ƙoƙari su yi amfani da sunan Ubangiji Yesu a kan waɗanda suke da aljanu. Suna cewa, “A cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa’azi, na umarce ku, ku fito.” 14 ’Ya’ya bakwai maza na Sikeba, wani babban firist na Yahudawa, suna yin haka. 15 Wata rana mugun ruhu ya amsa musu ya ce, “Yesu kam na sani, Bulus kuma na sani, amma ku kuma su wane ne?” 16 Sai mutumin da yake da mugun ruhun ya fāɗa musu ya sha ƙarfinsu duka. Ya yi musu dūkan tsiya har suka fita a guje daga gidan tsirara jini yana zuba.
17 Da Yahudawa da Hellenawan da suke zama a Afisa suka ji wannan labari sai duk tsoro ya kama su, aka kuwa darjanta sunan Ubangiji Yesu ƙwarai. 18 Da yawa cikin waɗanda suka gaskata yanzu suka zo a fili suka furta mugayen ayyukansu. 19 Waɗansu masu yin sihiri suka kawo naɗaɗɗun littattafansu wuri ɗaya suka kuwa ƙone su a gaban jama’a. Sa’ad da aka lissafta yawan kuɗin naɗaɗɗun littattafan nan, sai jimillar ta kai darik dubu hamsin. 20 Ta haka maganar Ubangiji ta bazu ko’ina ta kuma yi ƙarfi.
Bulus Ya Aiki Timoti da Erastus zuwa Makidoniya da Akayya
21 Bayan dukan wannan ya faru, sai Bulus ya yanke shawara ya ratsa Makidoniya da Akayya in za shi Urushalima. Ya kuma ce, “Bayan na tafi can, dole in ziyarci Roma ita ma.” 22 Sai ya aiki biyu daga cikin masu taimakonsa, Timoti da Erastus, zuwa Makidoniya, yayinda shi kuwa ya ɗan dakata a lardin Asiya.