Rarrabuwa Saboda Masu Hidima Tana Rushe Rayuwar Ruhaniya

Bulus ya nuna cewa rarrabuwa a cikin ikilisiya, wadda ta samo asali daga ra’ayoyin mutane game da baiwoyi daban-daban na masu hidimarsu, tana rusa rayuwar ruhaniya.

57 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Korintiyawa 3:1–10

1 ’Yan’uwa, ban iya yi muku magana kamar masu ruhaniya ba, sai dai kamar masu halin mutuntaka, jarirai cikin bin Kiristi kawai. 2 Na ba ku madara ba abinci mai tauri ba, domin ba ku balaga ba a lokacin. Kai, har yanzu ma, ba ku balaga ba. 3 Har yanzu kuna rayuwa bisa ga halin mutuntaka. Da yake akwai kishi da faɗace-faɗace a cikinku, ba rayuwa irin ta halin mutuntaka ke nan kuke yi ba? Kuma ba rayuwa irin ta mutane ce kawai kuke yi ba? 4 Gama sa’ad da wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afollos ne,” ba rayuwa irin ta mutane ke nan kuke yi ba?

5 Shin, wane ne Afollos? Wane ne kuma Bulus? Ai, bayi ne kawai waɗanda ta wurinsu kuka gaskata, kamar yadda Ubangiji ya ba kowannensu aikinsa. 6 Ni na shuka iri, Afollos kuma ya yi banruwa, amma Allah ne ya sa irin ya yi girma. 7 Don haka, da wanda ya yi shuki, da wanda ya yi banruwa, ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai, mai sa abubuwa su yi girma. 8 Mutumin da ya yi shuki, da mutumin da ya yi banruwa nufinsu ɗaya ne, kuma kowannensu zai sami lada gwargwadon aikinsa. 9 Gama mu abokan aiki ne na Allah; ku kuwa gonar ce ta Allah, ginin Allah kuma.

10 Ta wurin alherin da Allah ya ba ni, na kafa tushen gini kamar ƙwararren magini, wani kuma dabam yana gini a kai. Amma kowa yă lura da yadda yake gini.

Kiristi Ne Kaɗai Tushen Gini

Yesu Kiristi ne kaɗai tushen ginin bangaskiyar Kirista. An gargaɗi waɗanda suke gini a kan wannan tushe su yi hankali, domin dole ne su fuskanci gwaji mai tsanani. Malamin da ya shigar da koyarwar ƙarya zai ga waɗanda ya juyo da su suna barin bangaskiya a lokacin tsanantawa, kamar itace, ciyawa da tattaka a cikin wuta, shi kansa kuwa da ƙyar zai tsira. A gefe guda kuma, waɗanda suka gina ingantacciyar koyarwa mai kyau a kan wannan tushe za su ga waɗanda suka juyo da su suna tsallake gwajin wuta kamar azurfa da zinariya, malamin kansa kuma zai sami ladan wahalarsa.

1 Korintiyawa 3:11–15

11 Gama babu wanda zai iya kafa wani tushen gini dabam da wanda aka riga aka kafa, wanda yake Yesu Kiristi. 12 In wani ya yi gini a kan tushen ginin nan da zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja, itace, ciyawa ko kara, 13 aikin zai bayyana kansa, domin za a nuna shi a sarari a Ranar. Wuta ce za tă bayyana aikin, wutar kuwa za tă gwada ingancin aikin kowa. 14 In abin da kowane mutum ya gina ya tsaya, zai sami lada. 15 In ya ƙone, zai yi hasara, amma zai sami ceto, sai dai kamar wanda ya bi ta tsakiyar wuta ne.

Hikimar Duniyar Nan Wauta Ce

Bulus ya bayyana cewa za a hallaka malamin da ya shigar da koyarwar ƙarya cikin ikilisiya da gangan, kome girman nasararsa. Hikimar duniyar nan wauta ce a gaban Allah. Don haka kada su yi fahariya da malamansu ko falsafarsu da suke taƙama da ita, suna haddasa rarrabuwa a cikin ikilisiya. Ainihin ɗaukakar Kirista tana cikin Kiristi, wanda yake na Allah ne, kuma ta wurinsa kaɗai muke karɓar alkawuran ceto, waɗanda masu wa’azin bishara ba za su iya bayarwa ba.

1 Korintiyawa 3:16–23

16 Ashe, ba ku sani ba cewa ku kanku haikalin Allah ne, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikinku? 17 Duk wanda ya ɓata haikalin Allah, Allah zai ɓata shi, don haikalin Allah mai tsarki ne, ku ne kuwa haikalin nan.

18 Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yă zama mai hikima. 19 Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”; 20 kuma a rubuce yake cewa, “Ubangiji ya san dukan tunanin masu hikima banza ne.” 21 Saboda haka, kada wani yă yi taƙama da mutum! Gama kome naku ne, 22 ko Bulus ko Afollos ko Kefas ko duniya ko rai ko mutuwa ko abubuwa na yanzu ko na nan gaba, ai, duka naku ne, 23 ku kuwa na Kiristi ne, Kiristi kuma na Allah ne.

Allah Kaɗai Yake Hukunta Bayinsa

Manzanni, a matsayinsu na bayin Kiristi, suna da alhakin bayyana asiran bishara gwargwadon yadda mutane suke shirye su karɓe su. Da yake amsa sukar da malaman ƙarya suke yi masa saboda bai koya wa Korintiyawa koyarwar bangaskiyar Kirista mai zurfi ba, Bulus ya bayyana cewa hukuncin mutane da yake la’anta shi ba wani babban abu ba ne, domin Allah kaɗai zai iya yin hukunci daidai, kuma shi kaɗai ya san asiran zuciya. Saboda haka ya roƙe su kada su yanke wa malamansu na ruhaniya hukunci.

1 Korintiyawa 4:1–5

1 Saboda haka, ya kamata mutane su ɗauke mu a matsayin bayin Kiristi, da kuma a matsayin waɗanda aka ba su amanar asirin abubuwan Allah. 2 Yanzu fa, ana bukatar waɗanda aka ba su riƙon amana, dole su zama masu aminci. 3 Ƙaramin abu ne a gare ni a ce ku ne za ku gwada ni, ko kuwa a gwada ni a wata kotun mutane, ai, ko ni kaina ba na yanka wa kaina hukunci. 4 Lamirina bai ba ni laifi ba, sai dai wannan bai mai da ni marar laifi ba. Ubangiji ne mai hukunta ni. 5 Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.

Ana Rena Manzanni, Ana Girmama Malaman Ƙarya

Bulus ya bayyana cewa ya yi amfani da sunansa da na Afollos domin su koyi kada su ɗaukaka shugabanninsu daban-daban fiye da kima, har su cika da girman kai da fushi da raina juna. Bulus da Afollos bayin Kiristi ne kawai, waɗanda ta wurin hidimarsu ne Kiristoci suka ba da gaskiya. Sun ƙi duk wani laƙabi da bambancin matsayi a tsakaninsu, domin ta misalinsu Korintiyawa su koyi kada su ɗaukaka malamansu fiye da abin da ya rubuta. Daga nan Bulus ya juya ga malaman ƙarya. Ana kiran manzanni jahilai da wawaye domin suna wa’azin jigon farko na bangaskiyar Kirista, amma ana ɗaukan malaman ƙarya a matsayin masu hikima da masana falsafa saboda hasashe-hasashensu da al’adunsu. Ana rena manzanni; ana girmama malaman ƙarya. Manzanni suna fuskantar kowane irin haɗari, amma malaman ƙarya suna more dukiya da kowane irin jin daɗi.

1 Korintiyawa 4:6–13

6 To, fa ’yan’uwa, ga zancen waɗannan abubuwa, na misalta su ne ga kaina, da kuma Afollos saboda ku, don ku yi koyi da mu a kan abin da ake nufi da cewa, “Kada ku zarce abin da yake a rubuce.” Ta haka, ba za ku yi taƙama da wani mutum fiye da wani ba. 7 Wa ya ce ka fi sauran mutane? Me kuma kake da shi, wanda ba karɓa ka yi ba? In kuma karɓa ka yi, me ya sa kake taƙama kamar ba karɓa ba ne ka yi?

8 Kun riga kun sami duk abin da kuke nema! Kun riga kun yi arziki! Kun zama sarakuna, kun kuma zama haka ɗin ba tare da mu ba! Da a ce kun riga kun zama sarakuna mana da sai mu zama sarakuna tare da ku! 9 Gama a ganina fa, Allah ya baje mu manzanni a ƙarshen jerin gwanon, a matsayin mutanen da aka hukunta ga mutuwa a filin wasanni. Mun zama abin kallo ga dukan duniya, ga mala’iku da kuma mutane. 10 Mun zama masu wauta saboda Kiristi, ku kuwa kuna da hikima sosai a cikin Kiristi! Ba mu da ƙarfi, amma ku kuna da ƙarfi! Ana girmama ku, mu kuwa ana ƙasƙantar da mu! 11 Har yă zuwa wannan sa’a, yunwa da ƙishirwa muke ciki, muna sanye da tsummoki, ana wulaƙanta mu, ba mu kuma da gida. 12 Muna aiki da gaske da hannuwanmu. In aka la’anta mu, mukan sa albarka. In aka tsananta mana, mukan jimre; 13 in aka ɓata mana suna, mukan mayar da alheri. Har yă zuwa wannan lokaci, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.

Bulus Yana Gargaɗinsu a Matsayin Ubansu

Bulus ya bayyana cewa ba ya rubuta waɗannan abubuwa don ya kunyata su ba, sai dai don ya koya musu, ya kuma gargaɗe su game da malaman ƙarya, waɗanda ba za su zama musu abin da shi ya kasance ba, wato ubansu na ruhaniya. Saboda haka ya roƙe su su yi koyi da shi, ya kuma aika musu Timoti domin ya tuna musu da koyarwarsa.

1 Korintiyawa 4:14–17

14 Ba don in kunyata ku ba ne na rubuta wannan, sai dai don in gargaɗe ku a kan cewa ku ’ya’yana ne, ƙaunatattu. 15 Ko da kuna da iyayen riƙo dubu goma cikin Kiristi, ba ku da ubanni da yawa, gama a cikin Kiristi Yesu, na zama mahaifi a gare ku, ta wurin bishara. 16 Saboda haka, ina roƙonku ku yi koyi da ni. 17 Saboda wannan dalili ina aika muku Timoti, ɗana, wanda nake ƙauna, mai aminci kuma a cikin Ubangiji. Zai tunashe ku game da yadda za ku bi Kiristi Yesu da kuma yadda ya yi daidai da yadda nake koyarwa a ko’ina, a kowace ikkilisiya.

Bulus Zai Zo, da Horo ko da Ƙauna

Malamin ƙaryar ya yi da’awar cewa Bulus yana tsoron fuskantar abokan gāba masu ilimi da iya magana irin waɗannan. Bulus ya bayyana cewa yana nufin ya ziyarce su ba da daɗewa ba, sa’an nan zai binciki ba maganar abokan gābarsa ba, sai dai ikonsu na banmamaki, domin ba hikimar da masu wa’azin bishara suke taƙama da ita ce take tabbatar da bisharar ba, sai dai ikon yin mu’ujizai da aka ba su domin su tabbatar da ita. Daga nan ya tambaye su ko ya kamata ya yi amfani da nasa ikon na banmamaki a kansu don hukunta su, ko kuma ya zo musu cikin ruhun salama da ƙauna domin sun gyara kurakuransu.

1 Korintiyawa 4:18–21

18 Waɗansunku suna tsammani ba zan zo wurinku ba har suna ɗagankai. 19 Amma in Ubangiji ya yarda zan zo wurinku ba da daɗewa ba. Sa’an nan zan bincike ko masu wannan yawan ɗagan kan nan suna da wani iko. 20 Gama mulkin Allah ba cika baki ba ne, sai dai ga iko. 21 Wanne kuka fi so in na zo? Kuna so in tsananta muku ko in zama mai hankali da kuma sauƙinkai?