Bulus Ya Rubuta wa Kolossiyawa
Bulus ya rubuta wasiƙarsa zuwa ga Kolossiyawa a matsayin amsa ga saƙon Efafaras. Ya rubuta ne domin ya tabbatar cewa begen ceton ’yan Adam ya dogara ne ga aikin kafarar Kiristi kaɗai, kuma domin ya kawar da kurakuran masu tilasta bin addinin Yahudawa ta wurin kafa gaskiyar da ta saɓa wa waɗannan kurakurai. Ba Dokar Musa kaɗai suke wa’azinta ba, har ma da ra’ayoyin masana falsafa na arna, na Gabas, ko na ɗariƙar Essene game da bautar mala’iku, saboda rawar da ake zaton suna takawa a cikin al’amuran ’yan Adam, da kuma game da wajibcin ƙaurace wa cin nama.
62 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Bulus Ya Gai da Kolossiyawa
Bulus ya fara wasiƙarsa da tabbatar wa Kolossiyawa cewa an naɗa shi manzon Kiristi bisa ga nufin Allah. Bulus da Timoti sun gai da su. Ba su daina addu’a ba domin Kolossiyawa su cika da cikakken sanin al’amuran Allah, suna fahimtar hikimar Allah ta ruhaniya; domin su ba da ’ya’ya cikin kowane kyakkyawan aiki, su kuma ƙara sanin ƙaunar Allah da gaskiyarsa ta wurin abin da suke fuskanta; domin kuma a ƙarfafa su a ruhu ta wurin ikonsa mai ɗaukaka, don su jure kome da matuƙar haƙuri da jimiri, har ma da farin ciki, suna sane cewa ta haka suna faranta wa Allah rai; domin kuma su gode wa Allah, wanda bisa ga jinƙansa da ya yi musu da yardar ransa, ta wurin aikin tsarkakewa na Ruhunsa, ya sa su cancanci rabo cikin gādon ruhaniya da aka tanada wa waɗanda suke rayuwa cikin hasken bishara. Ya cece su daga ikon zunubi da jahilci, ya kuma fitar da mu daga mulkin duhu zuwa mulkin haske, wanda Ɗansa ƙaunatacce yake mulka. Shi ne ya biya kuɗin fansa da jininsa, wato gafarar zunubai.
1 Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu, da kuma daga Timoti ɗan’uwanmu,
2 Zuwa ga tsarkaka da kuma amintattun ’yan’uwa cikin Kiristi da suke a Kolossi.
Alheri da salama daga Allah Ubanmu, su kasance tare da ku.
3 Kullum muna gode wa Allah, Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, sa’ad da muke addu’a dominku. 4 Gama mun ji labarin bangaskiyarku a cikin Yesu Kiristi da kuma ƙaunar da kuke yi saboda dukan tsarkaka. 5 Kuna yin haka ne kuwa domin abin da kuke bege yana a ajiye a sama. Kun riga kun ji game da wannan bege sa’ad da kuka gaskata saƙon nan na gaskiya wanda shi ne bisharar 6 da ta zo muku. Ko’ina a duniya wannan bishara tana yi ta haihuwa tana kuma girma, kamar yadda take yi a cikinku tun daga ranar da kuka ji ta kuka kuma fahimci alherin Allah cikin dukan gaskiyarta. 7 Kun koyi wannan gaskiya daga wurin Efafaras, ƙaunataccen abokin hidimarmu, wanda yake amintacce mai hidimar Kiristi a madadinmu, 8 wanda kuma ya faɗa mana ƙaunar da kuke yi cikin Ruhu.
9 Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka. 10 Ta haka za ku yi rayuwa wadda ta dace da Ubangiji, ku kuma gamshe shi a ta kowace hanya, kuna yin aiki mai kyau ta kowace hanya, kuna kuma yin girma cikin sanin Allah. 11 Allah yă ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki 12 kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske. 13 Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna, 14 wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai.
Kiristi, Kamannin Allah Marar Ganuwa
Domin ya tabbatar musu cewa mutuwar Kiristi tana da ikon samar da gafarar zunubin ’yan Adam, Bulus ya bayyana allahntakar Kiristi da matsayinsa mafi ɗaukaka. Shi ne kamanni, ko cikakkiyar siffar Allah marar ganuwa, Mahaliccin dukan abubuwan da suka sami farko, masu ganuwa da marasa ganuwa, kuma Shi ne sanadin samuwarsu. Da kansa ya halicci kome, kuma domin kansa. Ya kasance tun kafin kowane abin halitta, saboda haka dole ne ya zama Allah na gaskiya wanda yake kasancewa da kansa. Kamar yadda ikonsa ya halicci kome, haka kuma yake kiyaye su: kamar yadda dukan abin da yake akwai ya samo asali daga gare shi, haka kuma ta wurinsa ne dole ya ci gaba da kasancewa. Shi ne Shugaban ikkilisiya, wadda yake ɗauka a matsayin jikinsa na ruhaniya. Ta wurin ɗaukar siffar mutum, shi ne sanadin farko ko mafarin ikkilisiya, kuma shi ne na farko da ya tashi daga matattu cikin siffar mutum mai ɗaukaka, domin ya zama mafifici cikin kome, a allahntakarsa da kuma a yanayinsa na mutum. Gama ya gamshi Uba cewa dukan ɗaukaka, da iko, da jinƙan Allahntaka su bayyana a cikinsa, ko su zauna a cikinsa. Da yake ya kawo zaman lafiya tsakanin Allah da mutum ta wurin jinin da ya zubar a gicciyensa, ta haka kuma ya rushe bangon da ya raba Yahudawa da al’ummai, ya sulhunta su da kansa, tare da dukan abubuwan da suke sama da waɗanda suke duniya, ko mutane ko mala’iku, ya haɗa su cikin zumunci guda mai tsarki na ruhaniya. Al’ummai kuwa, waɗanda a dā suke nesa da Allah, ayyukansu kuma suna tabbatar da cewa tunaninsu yana gāba da shi, yanzu ya sulhunta su ta wurin mutuwar jikinsa na mutum, domin ya gabatar da su masu tsarki marasa aibi, ba tare da wani abin zargi a gabansa ba, a ranar shari’a. Hakika zai yi haka idan suka ci gaba da kasancewa a kafe cikin bangaskiyar Yesu Kiristi, suka kuma tsaya daram a cikin koyarwarsa, ba tare da malaman ƙarya sun kawar da su daga bege mai albarka da alkawuran bishara ba. An yi wa mutumin Yahuda da Ba’al’umme wa’azin wannan bishara, wadda aka naɗa Bulus mai hidimarta.
15 Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta. 16 Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne. 17 Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe. 18 Shi ne kuma kan ikkilisiya, wadda take jikinsa. Shi ne mafari da kuma na farko da ya tashi daga matattu, domin a cikin kowane abu yă zama mafifici. 19 Gama Allah ya ji daɗi yă sa dukan cikarsa ta kasance a cikin Kiristi, 20 ta wurin Kiristi ne ya komar da kome zuwa ga kansa. Ya kawo salama ga abubuwan da suke ƙasa da abubuwan da suke sama, ta wurin jinin Kiristi da ya zubar a kan gicciye.
21 A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku. 22 Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi. 23 Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta.
Bulus Yana Farin Ciki Cikin Shan Wahala Saboda Al’ummai
A matsayinsa na mai hidimar Kiristi ga al’ummai, Bulus ya tabbatar musu cewa yana farin ciki cikin wahalolinsa, bisa ga amanar bishara da Allah ya ba shi domin amfaninsu, don ya cika nufin Allah kamar yadda annabawansa suka annabta. Wannan nufi shi ne asirin fansa ta wurin bangaskiya ga al’ummai, wanda aka ɓoye tsawon zamanai da yawa amma yanzu aka bayyana shi sarai: Kiristi yana zaune a cikin zukatansu, yana ba su gafarar zunubai ta wurin jininsa, ta wurin Ruhunsa kuma yana ba su begen samun ɗaukaka. Manzanni suna wa’azin Kiristi, suna gargaɗin kowa game da zunubinsa da haɗarin da yake ciki, suna kuma koya musu da dukan hikima ta ruhaniya. Domin wannan ne Bulus yake aiki tuƙuru, yana ƙoƙari da dukan ƙarfinsa. A matsayin shaidar wannan, yana so su san tsanantawa da wahalolin da ya jure saboda wa’azin bishara ga ikkilisiyar al’ummai, wato ga dukan al’ummai masu ba da gaskiya. Yana so su haɗu cikin ƙauna, su kuma sami cikakken tabbaci game da yalwar arzikin Kiristanci, su gane asirin Allah ta wurin Kiristi a cikin ceton Yahudawa da al’ummai duka; a cikinsa da cikin bishararsa ne dukan taskokin hikimar Allah da saninsa suke a ɓoye. Ya faɗi wannan ne don kada wani ya yaudare su da hujjoji masu wayo ko kalamai masu jan hankali na falsafar mutane. Ko da yake ba ya tare da su a jiki, yana tare da su ta wurin Ruhu, yana farin cikin ganin kyakkyawan tsarinsu da ladabinsu da bangaskiyarsu mai ƙarfi. Da yake sun karɓi bisharar Kiristi, ya ƙarfafa su su dawwama cikin bangaskiyarsa, su kafu a cikinsa, suna gina dukan begensu na gafara da ceto a kansa, domin, bayan an kafa su cikin tsarkin bangaskiyarsa kamar yadda aka koya musu, su ƙara yawaita wajen ba da ’ya’yanta, suna gode wa Allah saboda ya kira su su sami rabo cikin albarkunta.
24 Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya. 25 Na zama mai hidimar ikkilisiya bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da maganar Allah sosai. 26 Wannan magana da nake gaya muku asiri ne da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, wanda yanzu aka bayyana ga tsarkaka. 27 Su ne Allah ya so yă sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al’ummai, asirin nan kuwa shi ne Kiristi a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana.
28 Saboda haka ko’ina muka tafi, muna shela, muna gargaɗi, muna kuma koyar da kowa da dukan hikima, don mu miƙa kowa cikakke a cikin Kiristi. 29 Don haka ne ina fama, ina kuma ƙoƙari da duk ƙarfin nan da Kiristi ya ba ni.
2:1 Ina so ku san irin famar da nake yi saboda ku da kuma waɗanda suke a Lawodiseya, da kuma saboda dukan waɗanda ba su taɓa ganina ido da ido ba. 2 Manufata ita ce a ƙarfafa su su kuma zama ɗaya a cikin ƙauna. Ina so su kasance da cikakken ƙarfin hali domin suna da cikakken fahimtar asirin Allah, wato, Kiristi kansa, 3 a cikinsa ne aka ɓoye dukkan dukiya ta hikima da ta sani. 4 Ina faɗa muku wannan ne don kada wani yă ruɗe ku da daɗin baki. 5 Gama ko da yake ba na nan tare da ku a cikin jiki, ina tunaninku kullum, ina kuma farin ciki da gani kuna rayuwa yadda ya kamata, kuna kuma dāgewarku a kan bangaskiyarku a cikin Kiristi.
6 To, da yake kun karɓi Kiristi Yesu a matsayin Ubangiji, sai ku ci gaba da rayuwa a cikinsa, 7 ku tsaya daram ku kuma ginu a cikinsa, ku sami ƙarfafawa a cikin bangaskiya kamar yadda aka koya muku, kuna kuma cike da godiya.
An Yi Kaciya Cikin Kiristi, An Binne Cikin Baftisma
Bulus ya gargaɗe su game da malaman da suke son su bi al’adun Yahudawa, waɗanda suke koyar da bautar mala’iku da ƙaurace wa cin nama. Waɗannan abubuwa suna bin al’adun mutane da ƙa’idodin farko na addini da aka bayar cikin Dokar Musa; amma cetonsu ya zama cikakke cikin Kiristi, wanda shi ne Maɗaukakin Kai da Mai Mulkin dukan abubuwan da aka halitta, ko mene ne matsayinsu. A cikinsa kuma, ba cikin mala’iku ba, aka yi musu kaciya, aka kuma ba su ikon ƙin dukan ayyukan jiki mai zunubi ta wurin aikin Ruhu Mai Tsarki. An nuna musu wannan ta wurin wannan farilla wadda za a iya ɗauka a matsayin kaciyar da Kiristi yake bukata a bishara: a cikinta an binne su ga zunubi a ƙarƙashin ruwa, kamar yadda aka binne Kiristi saboda zunubi a ƙarƙashin ƙasa, an kuma tashe su tare da shi daga cikin ruwa zuwa rayuwa ta ruhaniya, ta wurin bangaskiya ga ikon Allah mai banmamaki, wanda shi ma ya ta da Kiristi daga kabarin mutuwa zuwa rai madawwami. Haka kuma al’ummai, waɗanda suke matattu cikin zunubai da rashin kaciyar jiki, Allah ya rayar da su tare da shi ta wurin Ruhunsa zuwa rai madawwami. Ya shafe rubutacciyar dokar farillai wadda take gāba da mutumin Yahuda da Ba’al’umme da kuma cetonsu, domin ta sa dukansu ƙarƙashin la’anar mutuwa ta har abada saboda zunubi. Bayan ya ƙwace mulkin masu mulki da hukumomin duhu da aka naɗa, ya nuna nasararsa a fili, yana yin galaba a kan ikonsu cikin tashinsa mai ɗaukaka daga kabari.
8 Ku lura kada wani yă ruɗe ku da ilimin banza da wofi. Wannan koyarwa ta mutane ce kawai. Ta fito daga ikokin wannan duniya ne ba daga Kiristi ba.
9 Gama a cikin Kiristi cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata, 10 an kuma mai da ku cikakku a cikin Kiristi, wanda yake shi ne kai a kan kowane iko da kuma hukuma. 11 A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Kiristi ya yi muku, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka. 12 Da yake an binne ku tare da shi cikin baftisma haka kuma aka tashe ku tare da shi ta wurin bangaskiyarku a cikin ikon Allah, wanda ya tashe shi daga matattu.
13 Kun zama matattu saboda ku masu zunubi ne kuma saboda halin zunubanku aka ware. Sa’an nan Allah ya sa kuka rayu tare da Kiristi. Ya gafarta mana dukan zunubanmu. 14 Ya soke rubutacciyar doka tare da ƙa’idodinta, wadda take gāba da mu, take kuma hamayya da mu; ya kuma kawar da ta, ya kafe ta a kan gicciye. 15 Bayan ya ƙwace makaman ikoki da hukumomi, ya kunyata su a sarari, ya ci nasara a bisansu ta wurin gicciye.
Abinci da Bukukuwa Inuwar Kiristi Ne
Tun da yake ta wurin Kiristi kaɗai ake kuɓutar da ’yan adam daga ikon zunubi da mutuwa ta har abada, Bulus ya roƙe su kada su bar kowa ya hukunta su a kan bambance-bambancen abinci da abin sha da ke cikin Dokar Musa, ko kuwa a kan bukukuwanta da Asabbataina. Waɗannan ayyukan kiyaye ƙa’idoji alamu ne kawai ko inuwa ta kyawawan abubuwan da za su zo; ainihinsu duka ya cika cikin Kiristi kansa da kuma albarkun ruhaniya na addininsa. Tun da yake Kiristi kaɗai, ta wurin hadayar gicciye, aka mai da shi Kai da Mai Mulkin kome da kuma hanyar ceto, ya gargaɗe su kada malaman ƙaryarsu ko masana falsafarsu su ruɗe su su riƙa yin tawali’u na riya ta wurin bautar mala’iku, suna kutsa kai da girman kai cikin abubuwan duniyar da ba a gani, suna kumbura saboda ilimin banza na tunaninsu na duniya. Irin waɗannan mutane ba su amince da Yesu Kiristi a matsayin Mai Ceto da Mai Mulkin ’yan adam shi kaɗai ba. Daga gare shi dukan jikinsa, wato ikkilisiya, yake samun abinci da ƙarfi na ruhaniya, yana haɗuwa ya zama ɗaya, yana kuma girma cikin alheri da tsarki yayin da baye-bayen Ruhu Mai Tsarkinsa suke ƙaruwa.
16 Saboda haka kada ku bar wani yă shari’anta ku a kan abin da kuke ci ko sha, ko bisa ga abin da ya shafi wani bikin addini, ko Bikin Sabon Wata ko na ranar Asabbaci. 17 Waɗannan su ne hoton abubuwan da za su zo; amma Kiristi ne ainihinsu. 18 Kada ku yarda wani yă ɓata ku, cewa shi wani abu ne don yă ga wahayi. Irin mutumin nan yakan nuna ƙasƙancin kai na ƙarya, yă kuma ce yana yi wa mala’iku sujada. Irin mutumin nan yana kumbura kansa ba dalili, sai son zuciya irin na halin mutuntaka. 19 Ya yanke dangantaka da Kiristi wanda yake kai, wanda ta gare shi ne dukan jiki yake a haɗe, yake tsaye ta wurin taimakon gaɓoɓi da jijiyoyi, yana kuma girma kamar yadda Allah yake sa yă yi girma.