Bulus Yana Kāre Haƙƙoƙinsa a Matsayin Manzo
A nan Bulus yana kāre matsayinsa na manzo ta wajen nuna tubarsu daga bautar gumaka da kuma baye-bayen ruhaniya da ya ba su. Ya amsa zargin da maƙiyansa, waɗanda ra’ayoyinsu da halayensu suka saɓa wa nasa ƙwarai, suka yi wa matsayinsa na manzo. Ya tabbatar da cewa, ko da yake ya ƙi karɓar tallafi daga Korintiyawa, yana da cikakken haƙƙin nemansa don kansa da kuma ’yar’uwarsa, ko matarsa, kamar yadda sauran manzanni suke da shi. Ya kāre haƙƙinsa na samun tallafi bisa ga al’adar mutane gaba ɗaya, da Dokar Musa, da kuma umarnin Kiristi bayyananne.
57 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Ba ni da ’yanci ne? Ni ba manzo ba ne? Ni ban gan Yesu Ubangijinmu ba ne? Ba ku ne sakamakon aikina cikin Ubangiji ba? 2 Ko da waɗansu ba su ɗauke ni a matsayin manzo ba, tabbatacce, ni manzo ne a gare ku! Gama ku ne hatimin manzancina a gaban Ubangiji.
3 Wannan ita ce kāriyata ga waɗanda suke tuhumata game da manzancina. 4 Ba mu da ’yancin ci da sha ne? 5 Ba mu da ’yancin tafiya tare da matar da muka aura mai bi kamar sauran manzanni da ’yan’uwan Ubangiji da kuma Kefas suke yi? 6 Ko ni da Barnabas ne kawai ba mu da ’yanci a ɗauke mana aikin ci da kai?
7 Wa yake ciyar da kansa yayinda yake aikin soja? Wa yake shukar gonar inabi, da ba ya cin amfaninta? Wa yake kiwon garke, da ba ya sha madararsa? 8 Ina faɗin wannan bisa ga ra’ayin mutum kawai ne? Ashe, Doka ma ba tă faɗa haka ba? 9 Gama yana a rubuce a cikin Dokar Musa cewa, “Kada ka sa wa saniya takunkumi sa’ad da yake sussukar hatsi.” Kuna tsammani a kan shanu ne Allah ya damu sa’ad da ya ce haka? 10 Babu shakka, ya yi maganan nan saboda mu ne. Ko ba haka ba? I, an rubuta wannan saboda mu ne, domin sa’ad da mai noma yake noma, mai sussuka kuma yana sussuka, suna wannan ne da bege za su sami rabonsu daga girbin. 11 In muka shuka iri na ruhaniya a cikinku, ashe, bai kamata mu yi girbin abin biyan bukatarmu daga gare ku ba? 12 In waɗansu suna samun wannan taimako daga gare ku, ashe, mu ba mu fi cancanta mu samu ba?
Amma ba mu yi amfani da wannan ’yancin ba. A maimakon haka, mun jure da kome, domin kada mu hana bisharar Kiristi yaɗuwa.
13 Ashe, ba ku san cewa waɗanda suke hidima a haikali suna samun abincinsu daga haikali ba ne, waɗanda kuma suke hidima a bagade suna samun rabo a hadayar da suka miƙa ba ne? 14 Haka ma Ubangiji ya umarta cewa ya kamata waɗanda suke wa’azin bishara, su sami abin biyan bukatarsu daga bisharar.
Bulus Ya Bar Haƙƙinsa na Samun Tallafi
Bulus ya bayyana dalilansa na rashin neman haƙƙinsa na samun tallafi daga cocin Kirista da ke Korint: yana tsoron cewa idan ya ɗora musu nauyi, zai iya rage nasarar bishara. Ya bayyana babban burinsa na yin fice a hidimarsa. Da yake ya wadatu da yin wa’azi, aikin da ba zai iya bari ba tare da ya yi shi ba, ya nuna yadda yake saukar da kansa don ya dace da kasawar mutane iri-iri da ra’ayoyinsu na son zuciya, domin ya jawo su zuwa ga Kiristi. Daga aya ta 24, Bulus ya nuna cewa ya dace ya jefa kansa cikin wahaloli da ayyuka masu wahala waɗanda ba lallai ne ya yi su ba, ta wurin yin nuni ga wata al’adar mutanen ƙasarsu, waɗanda suke fatan samun kambi mai lalacewa kawai. Ya gayyaci dukan waɗanda suka tuba su bi misalinsa, suna samun ƙarfafawa daga tabbataccen begen samun kambi marar lalacewa. An ƙarfafa su su yi rayuwar ƙin biyan bukatun kansu da kame kai a kullum.
15 Amma ban yi amfani da ko ɗaya daga cikin waɗannan ’yancin ba. Ba kuma ina rubuta muku wannan da fata za ku yi mini waɗannan abubuwa ba ne. Gwamma in mutu, da wani yă hana ni wannan abin taƙama. 16 Duk da haka, sa’ad da ina wa’azin bishara, ba na taƙama, domin tilas ne a gare ni in yi wa’azi. Kaitona, in ban yi wa’azin bishara ba! 17 In na yi wa’azi da yardar rai, ina da lada; in ba da yardar rai ba, ina dai cika amana da aka danƙa mini ne. 18 To, mene ne ladana? Ladana kaɗai shi ne, in yi wa’azin bishara, in kuma yi shi a kyauta, yadda ba zan yi amfani da ’yancina cikin wa’azin ba.
19 Ko da yake ina da ’yanci ba na kuma ƙarƙashin kowa, na mai da kaina bawa ga kowa, domin in rinjayi mutane da yawa. 20 Ga Yahudawa na zama kamar mutumin Yahuda, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda suke ƙarƙashin doka kuma, na zama kamar wanda yake ƙarƙashin Dokar (ko da yake ni kaina ba na ƙarƙashin Doka), domin in rinjayi waɗanda suke ƙarƙashin Doka. 21 Ga waɗanda ba su da Dokar kuwa, na zama kamar wanda ba shi da Dokar (ko da yake ba ni da ’yanci daga dokar Allah, amma ina ƙarƙashin dokar Kiristi), domin in rinjayi waɗanda ba su da dokar. 22 Ga waɗanda ba su da ƙarfi, na zama marar ƙarfi, domin in rinjayi waɗanda ba su da ƙarfi. Na zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko ta yaya in zai yiwu, in ceci waɗansu. 23 Ina yin dukan waɗannan ne saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.
24 Ba ku sani ba cewa a gasar gudu, dukan masu gudu sukan yi gudu, amma guda ne kaɗai yakan sami lada? To, sai ku yi gudu yadda za ku sami lada. 25 Duk ’yan wasan gasa sukan hori kansu sosai. Sukan yi haka domin su sami rawanin da ba zai daɗe ba. Amma mu muna yi ne domin mu sami rawanin da zai dawwama. 26 To, ni fa ba gudu nake yi kamar mai gudu ba wurin zuwa ba. Dambena kuma ba naushin iska nake yi ba. 27 A’a, ina horon jikina in mai da shi bawana, saboda bayan na yi wa waɗansu wa’azi, ni kaina kada in kāsa cancantar samun lada.
Misalin Isra’ila Yana Gargaɗin Korintiyawa
Ta wurin halin Isra’ilawa na dā, Bulus yana so ya tabbatar wa Korintiyawa cewa, kamar yadda aka hukunta mutanen da Allah ya nuna wa tagomashi da tsanani saboda rashin ɗa’arsu da bautar gumaka, haka ma Kiristoci da suke ƙarƙashin bishara, waɗanda suke more irin waɗannan zunubai da jin daɗi, tabbas za a hukunta su kamar Isra’ilawa da suke ƙarƙashin Doka. Ta waɗannan misalai ya gargaɗe su su guji irin waɗannan laifofi. Ya gargaɗe su kada su dogara da kansu fiye da kima saboda su ’yan ikilisiyar Kirista ne, sai dai su yi hankali kada su ma su faɗa cikin zunubi.
1 Ba na so ku kasance da rashin sani, ’yan’uwa, cewa dukan kakannin-kakanninmu sun yi tafiya a ƙarƙashin girgije, dukansu kuma suka bi ta tsakiyar teku. 2 An yi wa dukansu baftisma ga bin Musa a cikin girgije da kuma cikin teku. 3 Dukansu sun ci abincin ruhaniya guda 4 suka kuma sha ruwan ruhaniyan nan guda; gama sun sha daga dutsen ruhaniya nan, wanda ya yi tafiya tare da su, wannan dutsen kuwa Kiristi ne. 5 Duk da haka, Allah bai ji daɗin yawancinsu ba; gawawwakinsu kuwa suka bazu ko’ina a cikin hamada.
6 To, waɗannan abubuwa misalai ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi. 7 Kada ku zama masu bautar gumaka, yadda waɗansunsu suka zama; kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mutanen suka zauna don su ci su kuma sha, suka kuma tashi suka shiga rawa ta rashin kunya.” 8 Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har a rana guda mutane dubu ashirin da uku a cikinsu suka mutu. 9 Kada mu gwada Kiristi yadda waɗansunsu suka yi, har macizai suka kakkashe su. 10 Kada kuma ku yi gunaguni yadda waɗansunsu suka yi, har mala’ika mai hallakarwa ya hallaka su. 11 Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana. 12 Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi!
Dole Korintiyawa Su Guji Bautar Gumaka
Ana gargaɗin Korintiyawa, waɗanda ba sa fuskantar wasu jarabobi dabam da na sauran mutane, su nisanci bautar gumaka da cin abin da aka miƙa wa gumaka. Bulus ya tabbatar, ta wurin Jibin Ubangiji da muke yi da kuma dokar da ta shafi al'amuran ibada, cewa irin wannan aiki nuna bautar aljanu ne a fili, domin suna cin hadayun da aka miƙa wa aljanun, suna kuma haɗa kansu da su. Bautar Allah na gaskiya da bautar gumaka ba za su iya tafiya tare ba, kuma hakan yana zubar da mutuncin Kiristi.
13 Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.
14 Saboda haka abokaina ƙaunatattu, ku guje wa bautar gumaka. 15 Ina magana da ku a kan ku mutane ne fa masu azanci; ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa. 16 Kwaf nan na godiya da muke yin godiya da shi, ashe ba tarayya ce a cikin jinin Kiristi ba? Wannan burodi kuma da muke karya mu ci, ashe, ba tarayya ne a cikin jikin Kiristi ba? 17 Da yake burodin nan ɗaya ne, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama dukanmu muna ci daga burodi nan guda.
18 Ku dubi mutanen Isra’ila mana. Ashe, waɗanda suke cin hadayu, ba ɗaya suke da juna cikin cin hadayun da aka miƙa a bagade ba? 19 To, me kuke tsammani nake nufi a nan? Hadayar da aka miƙa wa gunki ce wani abu, ko kuma gunkin ne wani abu? 20 A’a, ina nufin akan miƙa hadayun da masu bautar gumaka suka wa aljanu ne, ba Allah ba. Ba na so ku zama ɗaya da aljanu. 21 Ba zai yiwu ku sha daga kwaf na Ubangiji ku kuma sha daga kwaf na aljanu ba, ba ya yiwuwa ku ci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a teburin aljanu. 22 Ashe, so muke mu tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?