Bangaskiyar Kirista Ba Ta Canja Dangantakar Rayuwa

Bulus ya koya cewa bangaskiyar Kirista ba ta canja dangantakar yau da kullum da wajibai na halitta a rayuwa.

57 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Korintiyawa 7:18–24

18 In an riga an yi wa mutum kaciya sa’ad da aka kira shi, to, kada yă zama marar kaciya. In an kira mutum sa’ad da yake marar kaciya, to, kada a yi masa kaciya. 19 Kaciya ba wani abu ba ne, rashin kaciya kuma ba wani abu ba ne. Kiyaye umarnin Allah shi ne muhimmin abu. 20 Ya kamata kowa yă kasance a matsayin da yake ciki sa’ad da Allah ya kira shi.

21 Kai bawa ne sa’ad da aka kira ka? Kada wannan yă dame ka, sai dai in kana iya samun ’yanci, sai ka yi amfani da wannan dama. 22 Gama wanda yake bawa sa’ad da Ubangiji ya kira shi, ’yantacce ne na Ubangiji; haka ma, wanda yake ’yantacce sa’ad da aka kira shi, bawa ne na Kiristi. 23 Da tsada fa aka saye ku, kada ku zama bayin mutane. 24 ’Yan’uwa, a duk matsayin da mutum yake sa’ad da aka kira shi, sai yă kasance haka a sabuwar dangantakarsa da Allah.

An Shawarci Budurwai da Zawarawa Su Ci Gaba Ba Tare da Aure Ba

Bulus ya shawarci budurwai da zawarawa su ci gaba ba tare da aure ba a lokutan tsanantawa. Domin su rage damuwa game da sha’anoni da jin daɗin rayuwar yanzu, ya tuna musu da yadda rayuwar take da gajarta da kuma ƙarancin muhimmanci.

1 Korintiyawa 7:25–40

25 To, game da budurwai. Ba ni da wani umarni daga Ubangiji, sai dai na yanke hukunci a matsayi wanda yake amintacce ta wurin jinƙan Ubangiji. 26 Saboda ƙuncin rayuwar da ake ciki, ina gani ya fi kyau ku kasance yadda kuke. 27 In kuna da aure, kada ku nemi kashe auren. In ba ku da aure, kada ku nemi yin aure. 28 Amma idan ka riga ka yi aure, to, ba laifi, ba zunubi ba ne, kuma idan yarinya ta yi aure, ba tă yi laifi ba. Sai dai waɗanda suka yi aure za su fuskanci damuwoyi masu yawa a cikin rayuwa, ni kuwa ina so in fisshe su daga wannan.

29 ’Yan’uwa, abin da nake nufi shi ne, lokaci ya rage kaɗan. Daga yanzu, waɗanda suke da mata ya kamata su yi rayuwa kamar ba su da su; 30 waɗanda suke kuka kuma kamar ba kuka suke yi ba, waɗanda suke farin ciki kuwa kamar ba farin ciki suke yi ba. Waɗanda suka sayi abu su yi kamar ba nasu ba ne; 31 masu amfani da kayan duniya kuwa, kada su duƙufa a cikinsu. Gama duniyan nan a yadda take mai shuɗewa ce.

32 Zan so ku ’yantu daga damuwa. Mutum marar aure ya damu ne da al’amuran Ubangiji, yadda zai gamshi Ubangiji. 33 Amma mutumin da yake da aure yakan damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda zai gamshi matarsa 34 hankalinsa a rabe yake. Mace marar aure ko kuwa budurwa ta damu ne da al’amuran Ubangiji. Nufinta shi ne ta ba da kanta ga Ubangiji cikin jiki da ruhu. Amma mace da take da aure ta damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda za tă gamshi mijinta. 35 Na faɗa haka don amfaninku ne, ba don in ƙuntata muku ba. Sai dai don ku yi rayuwa a hanyar da ta dace da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.

36 In mutum ya ga cewa ba ya nuna halin da ya kamata ga budurwar da ya yi alkawarin aure da ita, in kuma shekarunta suna wucewa, shi kuma ya ga ya kamata yă yi aure, to, sai yă yi. Ba zunubi ba ne. Ya kamata su yi aure. 37 Amma mutumin da ya riga ya yanke shawara a ransa, wanda kuma ba lalle ba ne amma yana iya shan kan nufinsa, kuma ya riga ya zartar a zuciyarsa ba zai auri budurwar ba, wannan mutum ma ya yi abin da ya dace. 38 Don haka, wanda ya auri budurwar ya yi daidai, amma wanda bai aure ta ba ya ma fi.

39 Mace tana haɗe da mijinta muddin yana da rai. Amma in mijinta ya mutu, tana da ’yanci ta auri wanda take so. Amma fa, sai mai bin Ubangiji. 40 A nawa ra’ayi, za tă fi jin daɗi in ta zauna haka, a ganina kuwa ina ba ku shawara ce daga Ruhun Allah da na ce haka.

Abincin da Aka Miƙa wa Gumaka da Masu Rauni

Da yake amsa waɗanda suka tuba, Bulus ya koya cewa ko da yake cin abubuwan da aka miƙa wa gumaka ba shi da wani laifi a kansa, ya kamata a guji wannan al’ada, domin misalinsu zai iya kai ’yan’uwa masu rauni ga zunubi ta wajen ƙarfafa musu tunanin cewa gunkinsu allah ne na gaske.

1 Korintiyawa 8

1 To, game da abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa. Mun san cewa dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kawo girman kai, amma ƙauna takan gina. 2 Mutumin da yake tsammani ya san abu, sanin da yake da shi bai isa ba. 3 Amma mutumin da yake ƙaunar Allah, Allah yana sane da shi.

4 To, game da cin abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa, mun san cewa “Gunki ba kome ba ne a duniya”, kuma “Babu wani Allah sai dai ɗaya.” 5 Gama ko da akwai abubuwan da ake ce da su alloli, a sama ko a ƙasa (don kuwa akwai “alloli” da “iyayengiji” da yawa), 6 duk da haka a gare mu dai akwai Allah ɗaya kaɗai, Uba, wanda dukan abubuwa suke daga gare shi, wanda kuma saboda shi ne muke rayuwa, kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa ne aka yi dukan abu, ta wurinsa ne kuma muke rayuwa.

7 Amma ba kowa ne ya san wannan ba. Har yanzu, waɗansu mutane sun saba da tunani cewa gumaka ainihi ne, saboda haka sa’ad da suka ci irin abincin nan, sukan ɗauka cewa kamar an miƙa wa ga gunki ne, kuma da yake lamirinsu ba ƙarfi, yakan ƙazantu. 8 Gaskiya ne cewa ba ma samun yardar Allah ta wurin abin da muke ci. Ba ma rasa wani abu idan ba mu ci ba, kuma ba ma ƙaru da wani abu in muka ci.

9 Sai dai ku yi hankali, kada yin amfani da ’yancinku yă zama abin sa tuntuɓe ga marasa ƙarfi. 10 Gama in wani wanda lamirinsa ba shi da ƙarfi ya gan ka, kai da kake da wannan sani, kana ci a haikalin gumaka, ashe, ba zai sami ƙarfin halin cin abin da aka miƙa wa gumaka ba? 11 Saboda haka ta wurin sanin nan naka sai ka sa wannan ɗan’uwa marar ƙarfi wanda Kiristi ya mutu dominsa yă hallaka. 12 Sa’ad da ka rushe lamiri mai bi marar ƙarfi, ka yi wa Kiristi zunubi ke nan. 13 Saboda haka, in abin da nake ci zai sa ɗan’uwana yă yi zunubi, ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa shi yă yi tuntuɓe.