Abinci na Halas da Amfanin Wasu
Bulus ya tabbatar cewa, ko da yake a ƙarƙashin bishara dukan abinci halal ne, yana hamayya da malaman ƙarya ta wurin bayyana cewa ba dukan abinci ne ya dace a ci ba, domin gina waɗansu ya kamata ya zama abu na farko. Korintiyawa za su iya cin duk abin da ake sayarwa a kasuwar nama ko aka ajiye a kan teburin arne, sai dai idan yin haka zai ɓata lamirin ’yan’uwa masu rauni. Dole Kiristoci su nemi ɗaukakar Allah da amfanin waɗansu maimakon biyan son ransu, har ma a ayyukan da a kansu ba nagarta ba ne kuma ba mugunta ba ne. An kira su su yi koyi da rashin son kai na Bulus, wanda ya bi Kiristi.
57 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
23 “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne mai ginawa. 24 Kada wani yă kula da kansa kawai, sai dai yă kula da waɗansu kuma. 25 Ku ci kowane abin da ake sayarwa a kasuwar nama ba sai kun tambaya ba don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito, 26 gama “Duniya da duk abin da yake cikinta na Ubangiji ne.”
27 In wani marar bi ya gayyace ku cin abinci kuka kuwa yarda ku je, sai ku ci ko mene ne da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito. 28 Sai dai in wani ya ce muku, “Ai, wannan an miƙa ne wa gunki,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan da ya gaya muku, don kuma lamiri yă kasance babu laifi 29 ina nufin lamirin wancan mutum ne fa, ba naku ba. Don me lamirin wani zai shari’anta ’yancina? 30 In na ci abinci da godiya, don me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?
31 Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah. 32 Kada ku sa wani yă yi tuntuɓe, ko mutumin Yahuda ne, ko mutumin Al’ummai ko kuma ikkilisiyar Allah 33 kamar dai yadda nake ƙoƙarin faranta wa kowa rai, ta kowace hanya. Gama ba don kaina kaɗai nake yi ba, sai dai don amfanin mutane da yawa, don su sami ceto.
11:1 Ku bi gurbina, kamar yadda ni nake bin gurbin Kiristi.
Bulus Ya Hana Mata Bayyana Ba Tare da Lulluɓi Ba
Bulus ya yabe su saboda kiyaye umarnansa. Ya bayyana yadda umarnan suke ta wurin nuna cewa dukan maza suna ƙarƙashin Kiristi, mace tana ƙarƙashin namiji, Kiristi kuma yana ƙarƙashin Allah. Da yake lulluɓi alama ce ta ƙaramin matsayi da biyayya, an hana mata bayyana ba tare da lulluɓi ba.
2 Ina yabonku saboda kuna tunawa da ni a cikin kowane abu, kuna kuma riƙe da koyarwar, yadda na ba ku. 3 To, ina so ku gane cewa shugaban kowane namiji Kiristi ne, shugaban mace namiji ne, shugaban Kiristi kuma Allah ne. 4 Kowane namijin da ya yi addu’a ko annabci da kansa a rufe ya jawo kunya wa kansa. 5 Duk macen da ta yi addu’a ko annabci da kanta a buɗe kuwa ta rena kanta, ya zama kamar an aske kanta ke nan. 6 In mace ba ta so tă rufe kanta, to, sai tă aske gashinta; in kuwa abin kunya ne mace tă yanke ko tă aske gashinta, to, sai tă rufe kanta.
7 Namiji kuwa bai kamata ya rufe kansa ba, da yake shi kamannin Allah ne, da kuma darajar Allah, amma mace dai, darajar namiji ne. 8 Gama namiji bai fito daga mace ba, sai dai mace ce ta fito daga namiji. 9 Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji. 10 Don haka, saboda wannan, da kuma saboda mala’iku, dole mace ta ɗaura wani abu a kanta. 11 Duk da haka a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, namiji kuma ba a rabe yake da mace ba. 12 Kamar yadda mace ta fito daga namiji, haka kuma aka haifi namiji ta wurin mace. Sai dai kowane abu daga Allah yake.
13 Ku kanku duba mana. Ya yi kyau mace tă yi addu’a ga Allah da kanta a buɗe? 14 Kai, yadda halitta take ma, ai, ta koya muku cewa in namiji yana da dogon gashi, abin kunya ne a gare shi, 15 amma in mace tana da dogon gashi, ai, daraja ce a gare ta. Gama an ba ta dogon gashi saboda rufe kanta ne. 16 In akwai mai gardama da wannan, to, mu dai ba mu da wata al’ada, haka ma ikkilisiyoyin Allah.
Bulus Ya Tsauta wa Rashin Tsari a Jibin Ubangiji
Bulus ya tsauta musu saboda rarrabuwarsu da ƙungiyoyi dabam-dabam da suke yi sa’ad da suka taru don bikin Jibin Ubangiji. Ba taruwa a wuri ɗaya kawai za su yi ba, dole su karɓi Jibin Ubangiji a matsayin jiki ɗaya, suna haɗa kai don tunawa da mutuwar Kiristi. Ya hukunta halinsu na kawo abinci cikin ikilisiya suna haɗa shi da Jibin Ubangiji, wanda yake ƙazantar da wannan farilla mai tsarki. Don gyara waɗannan abubuwa marasa tsari, Bulus ya ba da labarin yadda aka kafa Jibin Ubangiji, tare da umarnai na kiyaye shi yadda ya dace.
17 Game da umarnan nan dai, ban yaba muku ba, domin taruwarku ba ta kirki ba ce, ɓarna ce. 18 Da farko dai, na ji cewa sa’ad da kuka taru a matsayin ikkilisiya, akwai tsattsaguwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen. 19 Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku. 20 Sa’ad da kuka taru, ba Cimar Ubangiji kuke ci ba, 21 gama yayinda kuke ci, kowa yakan ci gaba ba tare da jiran wani ba. Wani yă zauna da yunwa, wani kuma yă bugu. 22 Kai, ba ku da gidajen da za ku ci ku sha ne? Ko dai kun rena ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma wulaƙanta waɗanda ba su da kome? Me zan ce muku? In yabe ku ne game da wannan? A’a, ko kaɗan!
23 Gama abin da na karɓa daga wurin Ubangiji shi ne nake ba ku. Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki burodi, 24 bayan ya yi godiya, sai ya kakkarya ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake dominku, ku yi wannan don tunawa da ni.” 25 Haka kuma bayan cimar, ya ɗauki kwaf, yana cewa, “Wannan kwaf ne sabon alkawari a jinina; ku yi wannan, a duk sa’ad da kuke sha, don tunawa da ni.” 26 Gama a duk sa’ad da kuke cin wannan burodi, kuke kuma sha daga wannan kwaf, kuna shelar mutuwar Ubangiji ne har yă dawo.
27 Saboda haka, duk wanda ya ci burodin ko ya sha daga kwaf na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulaƙanta jiki da jinin Ubangiji ke nan. 28 Dole kowa yă bincike kansa kafin yă ci burodin yă kuma sha daga kwaf ɗin. 29 Gama duk wanda ya ci ya kuma sha ba tare da fahimtar jikin Ubangiji ba, ya ci ya kuma sha wa kansa hukunci ne. 30 Shi ya sa da yawa a cikinku ba su da ƙarfi, suna kuma da rashin lafiya, waɗansunku kuma sun riga sun yi barci. 31 Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za mu shiga irin hukuncin nan ba. 32 Duk da haka sa’ad da Ubangiji ya hukunta mu, ana yin mana horo ne don kada a ƙarshe a hallaka mu tare da duniya.
33 Saboda haka ’yan’uwana, sa’ad da kuka taru don ci, ku jira juna. 34 In wani yana jin yunwa, sai yă ci abinci a gida, saboda in kuka taru kada yă jawo hukunci.
Sa’ad da na zo kuma zan ba da ƙarin umarnai.