Ku Yi Biyayya ga Masu Mulki, Ku Biya Haraji, Kada Ku Ci Bashin Komai Sai Ƙauna
Yahudawa, a matsayinsu na zaɓaɓɓun mutanen Allah, sun ƙi yin biyayya ko biyan haraji ga masu mulkin da ba na ƙasarsu ba ne, waɗanda kuma suke tsammani ba Allah ne ya naɗa su musamman ba. Bulus ya umarce su su miƙa kai ga dukan hukumomin gwamnati, domin kowane iko, na Yahuda da na arna duk ɗaya, Allah ne ya ƙaddara shi kuma ya kafa shi. Waɗanda suke tsayayya wa abin da Allah ya kafa suna jawo wa kansu hukunci. Gwamnati mai adalci tana kawo amfani. Masu mulki, a matsayin masu hidimar Allah, suna da iko su kāre masu nagarta kuma su ba su lada, su kuma hukunta masu aikata mugunta a matsayin bayin Allah. Saboda haka miƙa kai ya zama dole, ba don tsoron hukunci a duniya kaɗai ba, amma saboda lamiri kuma. An kuma umarce su su biya haraji. Da yake za a ɗauki dukan masu mulkin gwamnati a matsayin masu hidimar kulawar Allah, waɗanda suke ba da kansu ga ayyukan matsayinsu, dole ne su ba kowa girmamawar da ta dace da ofishinsa da matsayinsa, ko da mutumin da kansa bai cancanta ba. Su kasance masu adalci wajen biyan dukan basussukansu, don kada su ci bashin kome ga kowa sai ƙaunar juna, wadda take cika dukan umarnan Dokar da suka shafi maƙwabtanmu.
58 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Dole kowa yă yi biyayya ga masu mulki, gama babu wani iko sai ko in Allah ya yarda. Duk hukumomin da muke su, naɗin Allah ne. 2 Saboda haka, duk wanda ya yi tawaye ga hukuma yana yin tawaye da abin da Allah ya naɗa ne, waɗanda kuwa suke aikata haka, za su jawo wa kansu hukunci. 3 Gama masu mulki ba abin tsoro ba ne ga waɗanda suke yin abin da yake daidai, sai dai ga waɗanda suke aikata laifi. Kana so ka rabu da jin tsoron wanda yake mulki? To, sai ka aikata abin da yake daidai, zai kuwa yabe ka. 4 Gama shi bawan Allah ne don kyautata rayuwarka. Amma in ka aikata mugunta, to, sai ka ji tsoro, don ba a banza ne shugaba yake ɗaukan takobinsa ba. Shi fa bawan Allah ne, ta wurinsa ne fushin Allah yakan hukunta masu laifi. 5 Saboda haka, dole a yi biyayya ga hukumomi, ba don gudun horo kawai ba amma don lamirinku.
6 Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, gama hukumomin nan bayin Allah ne, waɗanda suke ba da dukan lokacinsu don aikin shugabanci. 7 Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma.
8 Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan. 9 Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” 10 Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce.
Ku Farka daga Barcin Zunubi
Lallai masu tuba daga cikin Romawa sun san sosai cewa wannan lokacin bishara ne, tun da haske ya fara haskakawa. Saboda haka Bulus ya yi kira gare su su farka daga barcin zunubi, domin sun fi fahimtar madawwamin ceton da bishara take kawowa da wajibai da take bukata fiye da lokacin da suka fara ba da gaskiya. Ya kwatanta duhun duniyar arna da daren da ya kusa ƙarewa, bishara kuma da hasken rana mai ɗaukaka da take biye da shi. Saboda haka ya roƙi Al’ummai su tuɓe tufafin da aka yi ayyukan duhu a cikinsu, su kuma sa kayan yaƙi, ko tufafi, na haske: su bar dukan tsofaffin halayensu da hanyoyinsu na zunubi, su kuma yafa Ubangiji Yesu Kiristi, wato su karɓi bishararsa, su bi misalinsa, su nemi abubuwan sama, kada kuma su tanadar wa halin mutuntaka abin da zai biya sha’awoyinsa.
11 Ku yi wannan domin kun san irin zamanin da kuke ciki. Lokaci ya yi da za ku farka daga barcinku, don cetonmu ya yi kusa yanzu fiye da lokacin da muka fara ba da gaskiya. 12 Dare fa ya kusan ƙarewa; gari kuma yana gab da wayewa. Saboda haka bari mu kawar da ayyukan duhu mu kuma yafa kayan yaƙi na haske. 13 Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba. 14 A maimakon haka, ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Kiristi, kada kuma ku yi tunani game da yadda za ku gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka.
Abinci, Ranaku Masu Tsarki, da Masu Rauni Cikin Bangaskiya
Masu tuba daga al’ummar Yahuda a Roma sun ɗauka cewa ya kamata a ci gaba da kiyaye bambancin abincin da Musa ya umarta da kuma ranaku masu tsarki da ya keɓe, har a zamanin Kirista. Bulus ya yi kira ga Al’ummai, waɗanda suka fi fahimta, su karɓi waɗannan masu tuba daga al’ummar Yahuda waɗanda suke da raunin bangaskiya a wannan fanni da alheri, kada kuma su yi gardama a kan waɗannan al’amura. An roƙi Yahudawa da Al’ummai kada su raina ko su hukunta juna, domin Allah ya karɓi Ba’al’umme wanda yake cin kowane irin abinci ba tare da bambantawa ba cikin ikilisiyarsa. A ranar shari’a kuma zai tabbatar da, ko ya kuɓutar da, duk waɗanda suka yi aiki bisa ga lamirinsu a kan waɗannan al’amura marasa muhimmanci. Kada mutane su rayu domin kansu, amma domin Kiristi. Kada su hukunta juna, domin Allah zai yi mana shari’a duka, kuma gare shi kaɗai dole ne mu ba da lissafi.
1 Ku karɓi wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, amma fa kada ku hukunta shi a kan abubuwan da ake da shakka a kai ba. 2 Bangaskiyar mutum ta yarda masa yă ci kome, amma wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, yakan ci kayan lambu ne kawai. 3 Mutumin da yake cin kowane irin abinci, kada yă rena wanda ba ya cin, wanda kuma ba ya cin kowane irin abinci, kada yă ga laifin mutumin da yake ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi. 4 Kai wane ne har da za ka ga laifin bawan wani? Ko bawan yă yi aiki mai kyau, ko yă kāsa, ai, wannan ruwan maigidansa ne. Za a ma tsai da shi, domin Ubangiji yana da ikon tsai da shi.
5 Wani yakan ɗauki wata rana da daraja fiye da sauran ranaku; wani kuma yana ganin dukan ranakun ɗaya ne. Ya kamata kowa yă kasance da tabbaci a cikin zuciyarsa. 6 Wannan mai ɗaukan rana ɗaya da muhimmanci fiye da sauran, yana yin haka ne ga Ubangiji. Wannan mai cin nama, yana yin haka ne ga Ubangiji, gama yakan yi godiya ga Allah; wannan da ba ya ci kuwa, yana yin haka ne ga Ubangiji yana kuwa yin godiya ga Allah. 7 Gama ba waninmu da yake rayuwa wa kansa kaɗai, kuma ba waninmu da kan mutu don kansa kaɗai. 8 In muna rayuwa, muna rayuwa ne ga Ubangiji; in kuma muna mutuwa, muna mutuwa ne ga Ubangiji. Saboda haka, ko muna a raye ko muna a mace, mu na Ubangiji ne. 9 Saboda wannan ne Kiristi ya mutu, ya kuma sāke rayuwa domin yă zama Ubangiji na matattu da na masu rai.
10 Kai kuwa, don me kake ganin laifin ɗan’uwanka? Ko kuma don me kake rena ɗan’uwanka? Gama duk za mu tsaya a gaban kujerar shari’ar Allah. 11 A rubuce yake cewa,
“ ‘Muddin ina raye,’ in ji Ubangiji,
‘kowace gwiwa za tă durƙusa a gabana;
kowane harshe kuma zai furta wa Allah.’ ”
12 Don haka kowannenmu zai ba da lissafin kansa ga Allah.
Kada Ku Sa Ɗan’uwa Mafi Rauni Ya Yi Tuntuɓe
Da yake dukanmu za mu ba da lissafin ayyukanmu, Bulus ya roƙi masu tuba daga cikin Romawa su daina hukunta juna, su kuma mai da hankali sosai kada su ba ɗan’uwa mai rauni dalilin yin tuntuɓe ko faɗuwa. Gama ko da yake babu abincin da yake marar tsarki a kansa, ga duk wanda yake ɗaukarsa marar tsarki, marar tsarki ne. Saboda haka su lura kada misalinsu ya hallaka wani wanda Kiristi ya mutu dominsa, kada kuma kyakkyawan ’yancin da suke morewa ya zama sanadin mugunta. Gama mulkin Allah ba batun ci da sha ba ne, amma na tsarki, salama ta ruhaniya, da farin ciki. Su bauta wa Kiristi ta bin hanyar da za ta inganta salama da gina juna, kada su yi kasadar lalata nagartar wani ta wurin biye wa sha’awar cin abincinsu. Waɗanda suka kai ga ingantacciyar fahimtar bangaskiya game da abinci da ranaku kada su nuna ta domin cutar da wasu. Lallai mai albarka ne wanda ba ya jawo wa kansa hukunci ta yin abubuwan da a kansu halal ne. Duk wanda ya gaskata cewa wasu abinci haram ne bisa ga Dokar Musa, ya yi zunubi idan ya ci su, domin yana yin abin da ya gaskata haram ne, ta haka kuma yana karya lamirinsa.
13 Saboda haka bari mu daina ba wa juna laifi. A maimakon, sai kowa yă yi niyya ba zai sa dutsen tuntuɓe ko abin sa fāɗuwa a hanyar ɗan’uwansa ba. 14 A matsayina na mai bin Ubangiji Yesu na tabbata ƙwarai cewa babu abincin da yake marar tsabta don kansa. Amma in wani ya ɗauka wani abu marar tsabta ne, to, a gare shi marar tsabta ne. 15 In kana ɓata wa ɗan’uwanka zuciya saboda abincin da kake ci, ba halin ƙauna kake nunawa ba ke nan. Kada abincin da kake ci yă zama hanyar lalatar da ɗan’uwanka wanda Kiristi ya mutu dominsa. 16 Kada ka bar abin da ka ɗauka a matsayi kyakkyawa yă zama abin zargi ga waɗansu. 17 Gama mulkin Allah ba batun ci da sha ba ne, sai dai na adalci, salama, da kuma farin ciki cikin Ruhu Mai Tsarki, 18 duk kuwa wanda yake bauta wa Kiristi a haka yana faranta wa Allah rai ne, yardajje kuma ga mutane.
19 Saboda haka sai mu yi iya ƙoƙari mu aikata abin da zai kawo salama da kuma ingantawa ga juna. 20 Kada ku lalatar da aikin Allah saboda abinci. Dukan abinci mai tsabta ne, sai dai ba daidai ba ne mutum yă ci abin da zai sa wani yă yi tuntuɓe. 21 Ya fi kyau kada ka ci nama ko ka sha ruwan inabi ko kuma ka yi wani abin da zai sa ɗan’uwanka yă fāɗi.
22 Bari duk ra’ayin da kake da shi game da wannan sha’ani yă kasance tsakaninka da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa ba tă ba shi laifi game da abin da shi da kansa ya ɗauka cewa daidai ne ba. 23 Amma wanda yake da shakka yakan jawo wa kansa hukunci ne in ya ci, domin yana ci ne ba bisa ga bangaskiya ba; kuma duk abin da bai zo daga bangaskiya ba zunubi ne.
Ya Kamata Masu Ƙarfi Su Haƙura da Masu Rauni
Ana bukatar waɗanda suke da ƙarfi cikin bangaskiya musamman su haƙura da kasawar masu rauni, kada su nemi faranta wa kansu rai, amma su nemi gina maƙwabcinsu, kamar yadda Kiristi da kansa ya koyar ta misalinsa, wanda Nassi ya riga ya faɗa (Zabura 69:9). Bulus ya tabbatar musu cewa duk abin da aka rubuta game da wahalar Kiristi da ta tsarkaka a Tsohon Alkawari, an rubuta shi ne domin koyar da su, domin ta wurin Nassosi su sami bege ɗaya da ƙarfafawa ɗaya. Ya yi addu’a su bi misalin Kiristi wajen mu’amala da juna, domin ba tare da jayayya ba su haɗa kai wajen ɗaukaka Allah, su kuma karɓi juna, su yi zumunci da juna, kamar yadda Kiristi ya karɓi su duka biyu cikin ikilisiyarsa, domin ɗaukakar Allah Uba.
1 Mu da muke da ƙarfi ya kamata mu yi haƙuri da kāsawar marasa ƙarfi ba kawai mu gamshi kanmu ba. 2 Ya kamata kowannenmu yă faranta wa maƙwabcinsa rai don kyautata zamansa domin kuma yă gina shi. 3 Gama ko Kiristi ma bai gamshi kansa ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa, “Zage-zagen da waɗansu suka yi maka, duk sun fāɗo a kaina.” 4 Gama duk abin da aka rubuta a dā an rubuta ne domin yă koya mana, don ta wurin jimrewa da kuma ƙarfafawar Nassosi mu kasance da bege.
5 Bari Allah mai ba da haƙuri da kuma ƙarfafawa yă ba ku ruhun haɗinkai da juna yayinda kuke bin Kiristi Yesu, 6 don da zuciya ɗaya da kuma baki ɗaya kuke ɗaukaka Allah da kuma Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi.
7 Ta haka sai ku karɓi juna kamar yadda Kiristi ya karɓe ku, don a yabi Allah.
Al’ummai Ma Suna Ɗaukaka Allah Saboda Jinƙansa
A nan Bulus yana kama da wanda yake tunanin wata hujjar ƙin amincewa da wataƙila Yahudawa za su kawo game da karɓar Al’ummai cikin ikilisiyar Kiristi: cewa Kiristi bai yi musu wa’azi ba. Bulus ya tabbatar cewa an haifi Yesu Kiristi a matsayin Bayahude, kuma ya zama bawan masu kaciya domin ya cika alkawuran da aka yi wa kakanni yadda ya kamata. Ta haka Al’ummai ma za su sami dalilin ɗaukaka Allah saboda jinƙansa, kamar yadda annabawansu suka annabta; waɗannan annabce-annabce kuma sun tabbatar a sarari cewa tun daga farko Allah ya ƙudura ya mai da Al’ummai mutanensa kamar Yahudawa. Bulus yana addu’a cewa Allah, wanda ya ba Al’ummai wannan bege, ya cika su da dukan salama da farin ciki na ruhaniya ta wurin ba da gaskiya ga Yesu Kiristi, kuma dukan abin da suke bege da sa rai gare shi a cikinsa ya tabbata ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
8 Ina dai gaya muku cewa Kiristi ya zama bawan Yahudawa a madadin gaskiyar Allah, don yă tabbatar da alkawaran da aka yi wa kakannin kakanninmu 9 domin Al’ummai su ɗaukaka Allah saboda jinƙansa, kamar yadda yake a rubuce,
“Saboda haka zan yabe ka a cikin Al’ummai;
zan rera waƙoƙi ga sunanka.”
10 Ya kuma ce,
“Ku yi farin ciki, ya Al’ummai, tare da mutanensa.”
11 Da kuma,
“Ku yabi Ubangiji, dukanku Al’ummai,
ku kuma rera masa yabo, dukanku mutanen duniya.”
12 Kuma Ishaya ya ce,
“Tushen Yesse zai tsiro,
wanda zai taso yă yi mulkin al’ummai;
al’ummai za su sa bege a gare shi.”
13 Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.