Hidimar Bulus ga Al’ummai da Shirye-shiryensa

Yanzu da Bulus ya gama sassan wasiƙarsa da suka shafi koyarwa da aikatawa, ya fi mai da hankali ga Al’ummai. Ya gamsu cewa suna cike da nagarta da sanin nufin Allah gare su har suna iya gargaɗar juna. Duk da haka ya rubuta musu da ƙarfin zuciya saboda matsayinsa na manzo, wanda ya karɓa daga Allah domin juyowar Al’ummai zuwa ga bangaskiya, waɗanda yanzu yake miƙa wa Allah a matsayin hadaya karɓaɓɓiya. Yana alfahari da nasarar hidimarsa, Kiristi yana aiki tare da shi yana kuma tabbatar da koyarwarsa da aikensa da manyan alamu da abubuwan banmamaki, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki. Tsananin marmarinsa na yin wa’azin bishara inda ba a riga an san ta ba ya hana shi ziyartar Roma, inda aka riga aka dasa ta. Amma yanzu, da ba shi da sauran abin yi, yana sa ran ganinsu a kan hanyarsa ta zuwa Sifen, ya kuma ji daɗin kasancewa tare da su a kan hanyarsa ta zuwa can. Ya ambaci shirin tafiyarsa zuwa Urushalima domin kai gudummawar Al’ummai da ya juyo da su ga waɗanda suka juyo daga Yahudanci a Urushalima, yana fatan ta haka ya sulhunta su da juna: tun da Al’ummai sun san al’amuran ruhaniya ta wurin Yahudawa, wajibi ne su saka musu da abubuwan duniya. Ya sake cewa yana nufin ya ziyarce su bayan ya kai gudummawar, yana kawo kyaututtuka da albarkun bisharar Kiristi. Ya roƙe su su yi addu’a da ƙwazo domin a cece shi daga Yahudawa marasa ba da gaskiya waɗanda suke neman halaka shi, kuma gudummawarsa ta zama karɓaɓɓiya ga Yahudawa Kiristoci. Ya ƙare da fatansa na ganinsu, domin a ƙarfafa su da shi ta wurin raba baiwar ruhaniya, da kuma albarkarsa.

58 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Romawa 15:14–33

14 Ni kaina na tabbata, ’yan’uwana, cewa ku kanku kuna cike da kirki, cikakku cikin sani da kuma ƙwararru don yin wa juna gargaɗi. 15 Na rubuta muku gabagadi a kan waɗansu batuttuwa, don in sāke tuna muku su, saboda alherin da Allah ya ba ni 16 in zama mai hidimar Kiristi Yesu ga Al’ummai da aikin firist na yin shelar bisharar Allah, don Al’ummai su zama hadaya mai karɓuwa ga Allah, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki.

17 Saboda haka ina taƙama cikin Kiristi Yesu a cikin hidimata ga Allah. 18 Ba zan yi karambani in faɗi kome ba sai dai abin da Kiristi ya aikata ta wurina a jagorantar da Al’ummai su yi biyayya ga Allah ta wurin abin da na faɗa da kuma aikata 19 ta wurin ikon alamu da ayyukan banmamaki, da kuma ikon Ruhun Allah. Ta haka daga Urushalima har yă zuwa kewayen Illirikum, na yi wa’azin bisharar Kiristi. 20 Labudda, burina shi ne in yi wa’azin bishara inda ba a san Kiristi ba, don kada yă zama ina gini ne a kan tushen da wani ya kafa. 21 Sai dai kamar yadda yake a rubuce,

“Waɗanda ba a faɗa musu labarinsa ba za su gani,

waɗanda kuma ba su ji ba za su fahimta.”

22 Wannan ne ya sa sau da yawa aka hana ni zuwa wurinku.

23 Amma yanzu da babu sauran wurin da ya rage mini in yi aiki a waɗannan yankuna, da yake kuma shekaru masu yawa ina da marmari in gan ku, 24 ina shirin yin haka in na tafi Sifen. Ina fata in ziyarce ku yayinda nake wucewa don ku raka ni can, bayan na ji daɗin zama tare da ku na ɗan lokaci. 25 Yanzu kam, ina hanyata zuwa Urushalima don in kai gudummawa ga tsarkaka a can. 26 Gama Makidoniya da Akayya sun ji daɗin yin gudummawa domin matalautan da suke cikin tsarkakan da suke a Urushalima. 27 Sun kuwa ji daɗin yin haka, gama ya zama kamar bashi ne a gare su. Da yake Al’ummai sun sami rabo cikin albarkun ruhaniyar Yahudawa, ya zama musu kamar bashi su ma su taimaki Yahudawa da albarkunsu na kayan duniya. 28 Saboda haka in na kammala wannan aiki na kuma tabbata cewa sun karɓi wannan amfani, zan tafi Sifen in kuma ziyarce ku a hanyata. 29 Na san cewa sa’ad da na zo wurinku, zan zo ne cikin yalwar albarkar Kiristi.

30 Ina roƙonku ’yan’uwa, saboda Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma saboda ƙaunar Ruhu, ku haɗa kai tare da ni cikin famata ta wurin yin addu’a ga Allah saboda ni. 31 Ku yi addu’a don in kuɓuta daga hannun marasa bi a Yahudiya don kuma gudummawar da nake kaiwa Urushalima ta zama abar karɓa ga tsarkaka a can, 32 don da yardar Allah, in iso wurinku da farin ciki in kuma wartsake tare da ku. 33 Allah na salama yă kasance tare da ku duka. Amin.

Bulus Ya Yaba wa Fibi Ya Kuma Gai da Abokansa

Bulus ya yaba wa Fibi, wadda ta kai wannan wasiƙa, yana roƙon Kiristocin Roma su taimake ta. Ya gai da Akwila da Firiskila, waɗanda ya yaba musu sosai, da kuma ikilisiyar da take taruwa a gidansu. Ya gai da abokansa Kiristoci da yawa waɗanda yanzu suka zauna a Roma, waɗanda wataƙila shi ne ya juyo da wasunsu zuwa ga bangaskiya.

Romawa 16:1–16

1 Ina gabatar muku da ’yar’uwarmu Fibi, baranyar ikkilisiya a Kenkireya. 2 Ina roƙonku ku karɓe ta a cikin Ubangiji yadda ya dace a karɓi tsarkaka a kuma ba ta kowane irin taimakon da take bukata daga wurinku, gama ta zama mai taimako ƙwarai ga mutane masu yawa, haɗe da ni ma.

3 Ku gai da Firiskila da Akwila, abokan aikina cikin Kiristi Yesu. 4 Sun yi kasai da ransu saboda ni. Ba ni kaɗai nake musu godiya ba amma har ma da dukan ikkilisiyoyin Al’ummai.

5 Ku kuma gai da ikkilisiyar da take haɗuwa a gidansu.

Ku gai da ƙaunataccen abokina Efenetus, wanda ya zama na farko a karɓar Kiristi a lardin Asiya.

6 Ku gai da Maryamu wadda ta yi muku aiki tuƙuru.

7 Ku gai da Anduronikus da Yuniyas, dangina waɗanda aka daure a kurkuku tare da ni. Su fitattu ne sosai a cikin manzanni, sun riga ni zama masu bin Kiristi.

8 Ku gai da Amfiliyatus, ƙaunataccena a cikin Ubangiji.

9 Ku gai da Urbanus, abokin aikinmu cikin Kiristi, da kuma ƙaunataccen abokina Sitakis.

10 Ku gai da Afelles wanda amincinsa cikin Kiristi tabbatacce ne.

Ku gai da iyalin gidan Aristobulus.

11 Ku gai da ɗan’uwana, Hirodiyon.

Ku gai da iyalin gidan Narkissus da suke cikin Ubangiji.

12 Ku gai da Tiryifena da Tiryifosa, matan nan da suke aiki tuƙuru cikin Ubangiji.

Ku gai da ƙaunatacciyata Fersis, wata matan da ta yi aiki tuƙuru cikin Ubangiji.

13 Ku gai da Rufus zaɓaɓɓe cikin Ubangiji, da kuma mahaifiyarsa, wadda ta zama kamar mahaifiya a gare ni.

14 Ku gai da Asinkiritus, Filegon, Hermes, Faturobas, Hermas da kuma ’yan’uwan da suke tare da su.

15 Ku gai da Filologus, Yuliya, Nereyus da ’yar’uwarsa, da kuma Olimfas da dukan tsarkakan da suke tare da su.

16 Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki.

Dukan ikkilisiyoyin Kiristi suna gaishe ku.

Ku Guji Masu Haddasa Rarrabuwa

Bulus ya sake gargaɗe su su guji rarrabuwa da mutanen da suke haddasa ta. Irin waɗannan mutane ba sa bauta wa Kiristi ta wurin wa’azin koyarwarsa, domin ribar duniya kaɗai suke kwaɗayi; kuma da yake ba su da baiwar ruhaniya, suna ruɗar ko ɓatar da zukatan sababbin Kiristoci waɗanda ba sa zaton za a yaudare su, ta wurin zaƙin magana da yabo na yaudara. Yana farin ciki da biyayyarsu ta yanzu, yana kuma ƙarfafa su su ci gaba da rarrabe abin da yake mai kyau su kuma aikata shi, su zama masu tsarki, ko marasa laifi, game da mugunta: wato, su guji duk wata koyarwar ƙarya da dukan miyagun misalai. Ya annabta hallaka da za ta zo da sauri ga wakilan Shaiɗan waɗanda suke kawo rarrabuwa cikin ikilisiya, ya kuma ƙare da albarkarsa.

Romawa 16:17–20

17 Ina roƙonku, ’yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su. 18 Gama irin waɗannan mutane ba sa bautar Ubangijinmu Kiristi, sai dai cikinsu. Ta wurin yaudara da kuma daɗin baki, suna ruɗin marasa wayo. 19 Kowa ya riga ya ji game da biyayyarku, don haka ina cike da farin ciki game da ku; amma ina so ku zama masu hikima game da abin da yake nagari, ku kuma zama marasa laifi ga abin da yake mugu.

20 Allah na salama zai tattake Shaiɗan ba da daɗewa ba yă kuma sa shi a ƙarƙashin sawunku.

Alherin Ubangijinmu Yesu kuma yă kasance tare da ku.

Gaisuwa da Ɗaukaka ga Allah Makaɗaici Mai Hikima

A ƙarin bayanin da ya rubuta a ƙarshen wasiƙarsa, Bulus ya aika da gaisuwar mutane da dama da suke tare da shi. Ya taƙaita kome ta wurin ba Allah ɗaukaka, wanda shi kaɗai yake da ikon tabbatar da su cikin bangaskiyar gaskiya ga Kiristi ba tare da Dokar Musa ba. Wannan a dā asiri ne da aka ɓoye (ko da yake an riga an annabta kiran Al’ummai), amma yanzu an sanar da shi bisa ga umarnin Allah madawwami da aka bayyana wa Bulus, domin ta wurin wa’azinsa dukan al’ummai su san biyayyar bangaskiya, su ba da gaskiya su kuma yi biyayya. “Ɗaukaka ta tabbata har abada ga Allah makaɗaici mai hikima.”

Romawa 16:21–27

21 Timoti, abokin aikina, yana gai da ku, haka ma Lusiyus, Yason, da Sosifater, dangina.

22 Ni, Tertiyus, wanda ya rubuta wannan wasiƙa, ina gai da ku cikin Ubangiji.

23 Gayus, mai masauƙina, mai kuma saukar da dukan ’yan Ikkilisiya, yana gaishe ku.

Erastus, mai bi da ayyukan jama’ar gari, da kuma ɗan’uwanmu Kwartus, suna gaishe ku.

25 Ɗaukaka ta tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga wa’azin Yesu Kiristi, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun fil azal, 26 amma yanzu kuwa aka bayyana, aka kuma sanar ta wurin rubuce-rubucen annabawa bisa ga umarnin Allah madawwami, domin dukan al’ummai su gaskata su kuma yi masa biyayya 27 ɗaukaka ta tabbata har abada ga Allah, wanda shi ne kaɗai mai hikima ta wurin Yesu Kiristi! Amin.