Melkizedek, Misalin Kiristi
Bulus ya koma ga batunsa na fifikon aikin firist na Kiristi a kan na Haruna, yana ƙoƙarin kai su ga kamala cikin zurfafan asirai na bishara ta wurin kwatanta Melkizedek da Kiristi (Farawa 14:18). Ya nuna cewa Melkizedek ba shi da uba ko uwa: ba a rubuta asalinsa da zuriyarsa ba, kuma ba a ambaci ƙarshen ko farkon rayuwarsa ko aikin firist nasa ba. Saboda haka, kamar na Ɗan Allah, ana iya ɗaukar aikin firist nasa a matsayin mai dawwama har abada. Saboda matsayinsa mafi girma, Ibrahim, shugaban kakannin kakanni, ya ba shi zakka. Allah ya naɗa firistoci su karɓi zakka daga ’yan’uwansu Lawiyawa, ba domin sun fito daga zuriya mafi ɗaukaka ba, sai dai a matsayin rabon da zai biya bukatunsu (Lissafi 18:24–31). Amma Melkizedek, wanda ba na iyalin Haruna ba ne, ya karɓi zakka daga Ibrahim a matsayinsa na firist na kowa. A matsayinsa na wakilin Kiristi, babban firist na dukan ’yan Adam, ya albarkaci wanda aka yi wa alkawuran, yana nuna a gaba wanda ta wurinsa za a cika su, kuma ta wannan aiki ya nuna fifikonsa a matsayin sarki da kuma firist. A ƙarƙashin Dokar Yahudawa, ana biyan zakka ga mutanen da mutuwa take ɗauke su, waɗanda kuma ake ta maye gurbinsu. Amma a tsarin zamanin kakannin kakanni, wanda yake da rai marar ƙarewa ne ya karɓi zakka (Zabura 110:4), don haka aikinsa na firist ba ya canzawa. Lawi, wanda aka umarta ya karɓi zakka, ya biya zakka kuma ya sami albarka daga Melkizedek ta wurin Ibrahim, domin har yanzu yana cikin ƙugun ubansa.
62 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Wannan Melkizedek sarkin Salem ne da kuma firist na Allah Mafi Ɗaukaka. Shi ne ya sadu da Ibrahim ya albarkace shi sa’ad da Ibrahim ya dawowa daga cin nasara a bisa sarakuna, 2 Ibrahim kuwa ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome. Ma’anar sunan Melkizedek ita ce, “sarkin adalci.” Amma da yake Salem yana nufin “salama,” shi kuma “Sarkin salama” ne. 3 Ba shi da mahaifi ko mahaifiya, ba shi da asali, ba shi da farko ko ƙarshe, shi dai kamar Ɗan Allah ne kuma firist ne har abada.
4 Ku dubi irin girman da Melkizedek mana. Ko kakanmu Ibrahim ma ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na ganima! 5 Yanzu doka ta umarci zuriyar Lawi waɗanda suka zama firistoci su karɓi kashi ɗaya bisa goma daga wurin mutane, wato, ’yan’uwansu, ko da yake ’yan’uwansu zuriyar Ibrahim ne. 6 Ko da yake Melkizedek ba daga zuriyar Lawi ba ne, duk da haka Ibrahim ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na abin da yake da shi, Melkizedek kuwa ya sa masa albarka, shi da aka yi wa alkawura. 7 Kowa ya sani cewa na gaba shi yake sa wa na baya albarka. 8 Firistoci ake ba wa kashi ɗaya bisa goma na abin da mutane suke samu. Amma dukan firistoci sukan mutu, sai dai Melkizedek, kuma nassi ya ce yana da rai. 9 Ana ma iya cewa zuriyar Lawi, mai karɓar kashi ɗaya bisa goma daga mutane, ya ba da kashi ɗaya bisa goma ta wurin Ibrahim, 10 wannan ya kasance haka domin an haifi Lawi daga baya a iyalin Ibrahim wanda ya ba wa Melkizedek kashi ɗaya bisa goma.
Sabon Aikin Firist Yana Nufin Sabuwar Shari’a
Bulus ya nuna cewa Shari’a da tsarin firistoci na Lawi ba su kai matsayin wani tsarin firistoci na dabam da ya maye gurbinsu ba. Tsarin firistoci na Lawi bai iya cim ma kamala, wato manufar da aka kafa shi dominta ba: gafarar zunubi ta wurin isasshiyar hadayar kafara. Saboda haka aka yi alkawarin wani firist, bisa tsarin firistancin Melkizedek na asali, wanda shi kansa alama ce ta abin da zai zo (shekaru 400 kafin Shari’a), ba bisa tsarin Haruna ba. Idan aka canja tsarin firistoci, dole ne a canja shari’ar da aka kafa shi a kanta. Gama Kiristi, wanda ake faɗin waɗannan abubuwa a kansa (Zabura 110:4), na kabilar Yahuda ne, wadda ba ta da ikon yin hidima a bagaden Yahudawa. Kuma ya fi bayyana cewa za a canja Shari’a da tsarin firistoci duka, tun da an annabta cewa wani firist zai bayyana mai kama da Melkizedek. Ba a naɗa shi bisa Shari’a wadda ta dace da halin mutum na jiki kuma take kaiwa ga mutuwa ba, sai dai bisa ikon wani tsarin da ya fi kamala, wanda yake alkawarin firistanci da rai marasa ƙarewa, kamar yadda Allah da kansa ya bayyana.
11 Ko da yake Dokar Musa ta ce dole firistoci su kasance zuriyar Lawi, waɗannan firistoci ba su iya sa wani yă zama cikakke ba. Saboda akwai bukata wani firist kamar Melkizedek ya zo, a maimakon wani daga iyalin Haruna. 12 Gama in aka canja yadda ake zaɓan firist, dole a canja Dokar ita ma. 13 Mutumin da muke wannan zance a kai, ai, shi na wata kabila ce dabam, wadda ba wani daga kabilar da ya taɓa yin hidima a bagade. 14 Kowa ya san cewa Ubangijinmu ya fito ne daga zuriyar Yahuda ne, kuma Musa bai taɓa ce firistoci za su fito daga wannan kabila ba. 15 Canjin nan a Dokar Allah ya ƙara fitowa fili da wani firist dabam wanda yake kamar Melkizedek ya bayyana. 16 Ya zama firist ne ba saboda ya cika wata ƙa’ida ta zama zuriyar Lawi ba, sai dai bisa ga ikon ran da ba a iya hallakawa. 17 Gama nassi ya ce,
“Kai firist ne na har abada,
bisa ga tsarin Melkizedek.”
Firistanci da Aka Tabbatar da Rantsuwa
Bulus ya bayyana cewa an kawar da tsohuwar shari’ar da ta shafi firistanci, domin tana da rauni kuma ba ta da amfani wajen fansar mutum. Shari’ar Musa ba ta sa kowa ya zama cikakke ba. Amma kawo bege mafi kyau da tsarin firistoci mafi kyau ya kammala Shari’a ya kuma cika ta, yana kuma ba kowa damar kusantar bagaden Allah ta wurin hadayar Kiristi, ba babban firist kaɗai ba. An keɓe firistancin Kiristi da rantsuwa, don a nuna cewa ba zai canja ba, kuma ya fi tsarin firistocin da aka kafa ba tare da rantsuwa ba, na ɗan lokaci kaɗai, wanda za a canja yadda Allah ya ga dama. Ta wurin wannan rantsuwa mai tsanani, Yesu ya zama mai lamuni, ko mai ɗaukar alhakin, alkawarin da ya fi na Musa, wanda yake da firistoci da yawa domin mutuwa tana kawar da su. Amma firistancin Kiristi, wanda aka tabbatar da rantsuwa, ba zai koma hannun wani magaji ba, domin yana rayuwa har abada.
18 Ta haka aka kawar da ƙa’ida marar ƙarfi da kuma marar amfani 19 (gama doka ba tă mai da wani abu cikakke ba), yanzu kuwa bege mafi kyau ya ɗauki matsayinta. Ta haka kuma muka matso kusa da Allah.
20 Ba kuwa da rashin rantsuwa aka yi haka ba. Waɗansu sun zama firistocin ba tare da wata rantsuwa ba, 21 shi wannan ya zama firist ta wurin rantsuwar da Allah ya yi da ya ce masa,
“Ubangiji ya rantse,
ba kuwa zai canja zuciyarsa ba,
‘Kai firist ne na har abada.’ ”
22 Saboda wannan rantsuwa, Yesu ya zama tabbacin alkawari mafi kyau.
23 To, akwai waɗannan firistoci da yawa, da yake mutuwa ta hana su cin gaba da aikin zaman firist; 24 amma Yesu ba zai mutu ba, don haka zai zama firist har abada.
Kiristi Yana Iya Ceto Sarai
Bulus ya nuna abin da wannan hujja take nufi: tun da firistancin Kiristi ba ya canjawa, kuma Kiristi yana rayuwa cikin jiki har abada, yana iya ceton waɗanda suke zuwa wurin Allah sarai ta wurin matsayinsa na matsakanci da roƙon da yake yi a madadinsu. Irin wannan babban firist ne ya dace da mutum: mai tsarki da jinƙai, wanda babu wani rauni na zunubi da ya ƙazantar da shi, wanda aka keɓe daga masu zunubi da al’amuran duniya, aka kuma ɗaukaka shi sama da dukan mala’ikun Allah. Ba kamar firistocin Yahudawa ba, bai bukaci ya miƙa hadaya kowace rana domin zunubansa, sa’an nan domin zunuban mutane ba. Bai miƙa hadaya domin kansa ba, sai dai domin mutane, sau ɗaya, a kan gicciye. Gama Shari’a, wadda ba cikakkiya ba ce, tana naɗa mutanen da ba cikakku ba su zama manyan firistoci, saboda haka suna bukatar maimaita hadayu. Amma maganar rantsuwar (Zabura 110), wadda ta zo shekaru ɗari biyar bayan ba da Shari’a, ta naɗa Ɗan ya zama babban firist har abada, kuma ta wurinta aka soke firistancin Shari’a. A duk wannan bayani, Bulus ya kammala da cewa waɗanda suka kauce daga Kiristanci suka koma Yahudanci sun bar abin da yake cikakke zuwa abin da ba cikakke ba, sun kuma bar abin da yake dawwama har abada zuwa abin da a yanzu aka kawar.
25 Saboda haka ya iya ba da ceto gaba ɗaya ga masu zuwa wurin Allah ta wurinsa, gama kullum a raye yake saboda yă yi roƙo dominsu.
26 Irin wannan babban firist ne muke bukata, shi mai tsarki ne, marar aibi, mai tsabta, ba kamar mu masu zunubi ba sam. An ɗaukaka shi fiye da kome a sama. 27 Ba ya bukata yă yi ta miƙa hadayu kowace rana saboda zunubansa, sa’an nan saboda zunuban mutane kamar sauran firistoci. Ya miƙa hadaya sau ɗaya tak, sa’ad da ya miƙa kansa. 28 Gama doka takan naɗa babban firist a cikin mutane masu kāsawa; amma rantsuwar da ta zo bayan dokar, ta naɗa Ɗan, wanda aka mai da shi cikakke har abada.
Kiristi Yana Hidima a Alfarwa ta Gaske
Bulus ya tabbatar cewa babban abin da duk tattaunawarsa take nufi shi ne wannan: Kiristoci suna da babban firist mai girma, wanda aka ɗaukaka zuwa kursiyin Allah, mai hidima a ainihin wurare masu tsarki na alfarwa ta gaske, wato sammai, waɗanda Allah ya kafa, ba mutum ba kamar alfarwar Yahudawa. Kuma tun da kowane babban firist yana miƙa kyautai da hadayu kowace rana a duniya, dole Kiristi ma, a matsayinsa na babban firist, ya kasance da wata hadayar da zai miƙa a sama. A duniya ba zai iya yin hidimar firist ba, domin zuriyar Haruna ce aka naɗa don miƙa kyautai bisa Shari’a a haikalin Yahudawa. Hidimarsu inuwa ce ko kwafin hidimar Kiristi a sama, kamar yadda alfarwar kanta ta kasance misalin abubuwan da suke cikin sammai (Ibraniyawa 9:23) waɗanda aka nuna wa Musa a kan dutse.
1 Abin da muke magana a nan shi ne, muna da irin wannan babban firist, wanda ya zauna a hannun dama na kursiyin Maɗaukaki a sama, 2 wanda yake hidima a cikin wuri mai tsarki, tabanakul na gaskiya wanda Ubangiji ne ya kafa, ba mutum ba.
3 Da yake dole kowane babban firist da aka naɗa yă miƙa baye-baye da hadayu, haka ma wannan ya bukaci yă kasance da abin da zai miƙa. 4 Da a ce yana a duniya ne, da bai zama firist ba, domin a nan akwai mutanen da doka ta naɗa don su miƙa baye-baye. 5 Suna hidima a cikin tsattsarkan wuri wanda yake hoto da kuma siffar abin da yake cikin sama. Shi ya sa aka gargaɗi Musa sa’ad da yana dab da gina tabanakul cewa, “Ka lura fa, ka yi kome daidai bisa ga zānen da aka nuna maka a kan dutsen.”
Sabon Alkawari Ya Maye Gurbin Tsohon
Bulus ya tabbatar cewa tsarin firistoci na Kiristoci ya fi na Lawi daraja, domin an kafa shi a kan alkawuran da suka fi kyau. Ta wurin albarkun duniya na ɗan lokaci, tsohon alkawari ya kasance alamar albarkun ruhaniya na har abada da sabon alkawari zai kawo. Da ba na ɗan lokaci ba ne, kuma da ba shi da nakasa, da ba a bukaci wani ba. Allah da kansa ya nuna yadda tsohon alkawari bai iya cim ma manufarsa ba, da yadda sabon ya fi shi, sa’ad da ya tsauta wa Yahudawa ta wurin annabi Irmiya (Irmiya 31:31–34). Za a rubuta sabon alkawari a zukatan mutane, yana mulkin ayyukansu, ba a kan dutse kamar tsohon ba. Maimakon a keɓe iyali ɗaya don koya wa ’yan’uwansu (Maimaitawar Shari’a 6:7), kowa zai cancanci zama malami, don koyar da gafarar zunubai da mugunta ta wurin bangaskiya cikin jinin Kiristi da hadayarsa. Ta wurin yin alkawarin sabon alkawari, Allah ya mai da na farkon tsoho. Kuma abin da ya zama marar amfani, ya kuma tsufa, yana dab da ɓacewa, ko ya daina kasancewa.
6 Amma hidimar da Yesu ya karɓa tana da fifiko a kan tasu, kamar yadda alkawarin da shi ne yake matsakanci ya fi na dā fifiko nesa, an kuma kafa shi a kan alkawura mafi kyau.
7 Gama da a ce alkawari na fari ba shi da wani laifi, da ba sai an sāke neman wani ba. 8 Amma Allah ya sami mutane da laifi ya ce,
“Ina gaya muku lokaci yana zuwa,
sa’ad da zan yi sabon alkawari
da gidan Isra’ila
da kuma gidan Yahuda.
9 Ba zai zama kamar irin alkawarin
da na yi da kakanni-kakanninsu
sa’ad da na kama hannunsu
don in fitar da su daga Masar ba,
domin ba su yi aminci da alkawarina ba,
sai na juya musu baya,
in ji Ubangiji.
10 Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila,
bayan lokacin nan,
in ji Ubangiji.
Zan sa dokokina a cikin zukatansu,
in kuma rubuta su a kan zukatansu.
Zan zama Allahnsu,
su kuwa za su zama mutanena.
11 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba,
balle mutum yă ce wa ɗan’uwansa, ‘Ka san Ubangiji,’
domin dukansu za su san ni,
daga ƙaraminsu zuwa babba.
12 Gama zan gafarta muguntarsu
ba zan kuma ƙara tuna da zunubansu ba.”
13 Ta wurin kira wannan alkawari “sabo,” ya mai da na farin tsoho ke nan; abin da yake tsoho yana kuma daɗa tsufa, zai shuɗe nan ba da daɗewa ba.
Alfarwar Alama Ce ta Abubuwa Mafi Kyau Masu Zuwa
Ta wurin yanayin alfarwar da hidimomin da ake yi a cikinta, Bulus ya nuna cewa su alamomi ne na wani abu mafi kyau da zai zo. Da wannan a zuciyarsa, ya tuna musu da kayayyakin da suke a ɓangaren alfarwar da yake wakiltar duniyar da ake gani, wanda ake kira Wuri Mai Tsarki (Fitowa 35:26–40), da kuma waɗanda aka sa a ɓangaren da yake bayan labule na biyu, wanda ake kira Wuri Mafi Tsarki. Da yake an tsara alfarwar haka bisa umarnin Allah, firistocin kullum suna yin hidimar Allah a ɓangarenta na farko, wanda yake nuna bautar da mutane suke miƙa wa Allah marar ganuwa a duniya. Babban firist yakan shiga ɓangaren na biyu rana ɗaya kaɗai a shekara, a can kuma ya miƙa jinin dabbar da aka yanka don hadaya saboda zunubansa da na mutane (Littafin Firistoci 16:14, 15). Ta wurin dukan wannan, Ruhu Mai Tsarki, wanda ya kafa wannan tsari, ya nuna cewa bautar alfarwar farko ba ta sanar da mutane hanyar shiga gaban Allah kai tsaye ba. Wannan misali ko inuwa ta abubuwan da za su zo tana nan har a zamanin Bulus, a hidimar haikali, inda ake miƙa kyautai da hadayun da ba su iya kawar da jin laifin zunubi daga zuciya ba, domin su alamomi ne kawai na tsarkin ruhaniya da ake bukata sa’ad da aka gyara bautar Allah ta wurin tsarin bishara.
1 Alkawarin farko ya ƙunshi ƙa’idodi don sujada da kuma tsattsarkan wuri a duniya. 2 An kafa tabanakul. A cikin ɗakinsa na farko akwai wurin ajiye fitila, tebur da kuma keɓaɓɓen burodi; an kira wannan Wuri Mai Tsarki. 3 Sa’an nan akwai labule, kuma a bayan labulen akwai ɗaki na biyu da ake kira Wuri Mafi Tsarki, 4 wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma akwatin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin akwatin alkawarin akwai tulun zinariya mai Manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari. 5 A bisa akwatin alkawarin kuwa akwai kerubobi na Ɗaukaka, waɗanda suka inuwantar da murfin kafara da fikafikansu. Sai dai ba za mu tattauna waɗannan abubuwa dalla-dalla a yanzu ba.
6 Sa’ad da aka shirya kome haka, sai firistoci suka shiga kullum cikin ɗaki na waje don su yi hidimarsu. 7 Amma babban firist ne kaɗai yakan shiga ɗaki na ciki-ciki, sau ɗaya tak a shekara, kuma sai da jini, wanda yakan miƙa domin zunubansa da kuma domin zunuban da mutane suka yi a cikin rashin sani. 8 Ta haka Ruhu Mai Tsarki ya nuna cewa ba a riga an bayyana hanyar shiga Wuri Mafi Tsarki ba tukuna, muddin tabanakul na fari yana nan tsaye. 9 Wannan ma yana da ma’ana wa mutane a yau. Ya nuna cewa ba za mu iya wanke lamirinmu ta wurin miƙa baye-baye da hadayu ba. 10 Waɗannan ƙa’idodi sun shafi sha’anin abinci da abin sha ne kawai da kuma ƙa’idodi tsarkake kanmu. Dokoki game da abubuwa na waje da ake amfani da su za su kasance ne sai lokacin ya yi da za a kawo abu mafi kyau.