Yowel Ya Annabta Kifar da Yahuda (continued)

Sa’ad da Uzziya ya ƙara yawan sojojinsa, Yowel ya annabta cewa wata rana rundunar baƙi za ta kifar da masarautar Yahuda.

wajen 787 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Yowel 2–3

1 Ku busa ƙaho a cikin Sihiyona;

ku yi karar amo a tsaunina mai tsarki.

Bari dukan mazaunan ƙasar su yi rawan jiki,

gama ranar Ubangiji tana zuwa.

Tana gab da faruwa

2 rana ce ta baƙin duhu ƙirin,

ranar gizagizai ce baƙi ƙirin.

Babbar rundunar mayaƙa mai ƙarfi tana zuwa

kamar ketowar alfijir a kan duwatsu

yadda ba a taɓa ganin irinta ba,

ba kuwa za a ƙara ganin irinta ba har tsararraki masu zuwa.

3 A gabansu wuta tana ci,

a bayansu ga harshen wuta yana ci,

A gabansu ƙasa ta yi kamar gonar Eden,

a bayansu kuma jeji ne wofi,

babu abin da ya kuɓuce musu.

4 Suna da kamannin dawakai;

suna gudu kamar dokin yaƙi.

5 Da motsi kamar na kekunan yaƙi

sun tsallake ƙwanƙolin duwatsu,

kamar ƙarar harshen wuta mai cin tattaka,

kamar runduna mai ƙarfi wadda ta ja dāgār yaƙi.

6 Da ganinsu, al’ummai sun kamu da azaba;

kowace fuska ta yanƙwane.

7 Sukan auka kamar jarumawa;

sukan hau katanga kamar sojoji.

Kowa yana takawa bisa ga tsari,

ba mai kaucewa.

8 Ba sa turin juna,

kowane yakan miƙe gaba.

Sukan kutsa cikin abokan gāba

ba mai tsai da su.

9 Sukan ruga cikin birni,

suna gudu a kan katanga.

Sukan hau gidaje,

sukan shiga ta tagogi kamar ɓarayi.

10 A gabansu duniya takan girgiza,

sararin sama kuma yakan jijjigu,

rana da wata su yi duhu,

taurari kuma ba sa ba da haske.

11 Ubangiji ya yi tsawa

wa shugaban mayaƙansa;

sojojinsa sun fi a ƙirge

masu ƙarfi ne kuma su waɗanda suke biyayya da umarninsa.

Ranar Ubangiji da girma take;

mai banrazana.

Wa zai iya jure mata?

12 “Ko yanzu”, in ji Ubangiji,

“Ku juyo gare ni da dukan zuciyarku,

da azumi da kuka da makoki.”

13 Ku kyakkece zuciyarku

ba rigunanku ba.

Ku juyo ga Ubangiji Allahnku,

gama shi mai alheri ne mai tausayi kuma

mai jinkirin fushi da yawan ƙauna,

yakan kuma janye daga aika da bala’i.

14 Wa ya sani? Ko zai juya yă kuma ji tausayi

yă sa mana albarka

ta wurin hadaya ta gari da hadaya ta sha

wa Ubangiji Allahnku.

15 A busa ƙaho a Sihiyona,

a yi shelar azumi mai tsarki,

a kira tsarkakan taro.

16 A tattara mutane;

ku tsarkake taron;

ku kawo dattawa wuri ɗaya;

ku kuma tara yara,

da waɗanda suke shan mama.

Bari ango yă bar ɗakinsa

amarya kuma lolokinta.

17 Bari firistocin da suke yin hidima a gaban Ubangiji,

su yi kuka tsakanin filin haikali da bagade.

Bari su ce, “Ka cece mutanenka, ya Ubangiji.

Kada ka bar gādonka yă zama abin dariya,

da abin ba’a a cikin al’ummai.

Me zai sa a ce a cikin mutane, ‘Ina Allahnsu yake?’ ”

18 Ta haka Ubangiji zai yi kishin ƙasarsa

yă kuma ji tausayin mutanensa.

19 Ubangiji zai amsa musu ya ce,

“Ina aika da hatsi, sabon ruwan inabi, da mai,

isashe da zai ƙosar da ku sosai;

ba kuma zan ƙara maishe ku

abin dariya ga al’ummai ba.

20 “Zan kori sojojin arewa nesa da ku,

in tura su cikin busasshiyar ƙasa marar amfani kuma,

kuma da sawunsu na gaba zan tura su zuwa gabashin teku

da kuma sawunsu na baya tura su zuwa yammanci a Bahar Rum.

Warinsu kuma zai bazu;

ɗoyinsu zai tashi.”

Tabbatacce ya yi al’amura masu girma.

21 Kada ki ji tsoro, ya ƙasa;

ki yi murna ki kuma yi farin ciki.

Tabbatacce Ubangiji ya yi abubuwa masu girma.

22 Kada ku ji tsoro, ya ku namun jeji,

gama wuraren kiwo sun yi kore shar.

Itatuwa suna ba da ’ya’yansu;

itacen ɓaure da na inabi suna ba da amfaninsu.

23 Ku yi murna, ya ku mutanen Sihiyona,

ku yi farin ciki cikin Ubangiji Allahnku,

gama ya ba ku

ruwan bazara cikin adalci.

Yakan aika muku yayyafi a yalwace,

na bazara da na kaka, kamar dā.

24 Masussukai za su cika da hatsi;

randuna za su cika da sabon ruwan inabi da mai suna zuba.

25 “Zan mayar muku da abin da fāra suka ci a waɗannan shekaru

waɗanda ɗango da fāra masu gaigayewa,

da kuma sauran fāra da tarin fāra

babban mayaƙan da na aika don su fāɗa muku.

26 Za ku sami a wadace ku ci, har sai kun ƙoshi,

za ku kuma yabi sunan Ubangiji Allahnku,

wanda ya yi muku ayyukan banmamaki;

mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.

27 Sa’an nan za ku sani ina cikin Isra’ila,

cewa ni ne Ubangiji Allahnku,

babu wani kuma;

mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.

28 “Daga baya kuma,

zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane.

’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci,

tsofaffinku za su yi mafarkai,

matasanku za su ga wahayoyi.

29 Har ma a bisan bayina, maza da mata,

zan zuba Ruhuna a kwanakin nan.

30 Zan nuna abubuwan banmamaki a cikin sammai

da kuma a kan duniya,

za a ga jini da wuta da murtukewar hayaƙi.

31 Rana za tă duhunta

wata kuma yă zama jini

kafin isowar babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji.

32 Amma dukan waɗanda suka nemi

Ubangiji za su tsira.

Kamar yadda Ubangiji ya ce,

gama a Dutsen Sihiyona da Urushalima

akwai ceto,

a cikin waɗannan da Ubangiji ya kira.

3:1 “A waɗancan kwanaki da kuma a wancan lokaci,

sa’ad da zan maido da arzikin Yahuda da Urushalima,

2 zan tattara dukan al’ummai

in kuma kawo su Kwarin Yehoshafat

Can zan yi musu shari’a

game da gādona, mutanena Isra’ila,

gama sun warwatsar da mutanena a cikin al’ummai

sun kuma raba ƙasata.

3 Sun jefa ƙuri’a a kan mutanena

suna kuma sayar da yara maza don karuwanci,

sun sayar da ’yan matan domin ruwan inabi

wanda za su sha.

4 “Yanzu mene ne damuwarku da ni, ya Taya da Sidon da kuma dukan mazaunan yankunan Filistiya? Kuna ƙoƙari ku sāka mini don abin da na yi ne? In kuna sāka mini ne, to, da gaggawa zan mayar muku da sakayya a kanku. 5 Gama kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe dukiyata mafi kyau kun kai cikin haikalinku. 6 Kun sayar da mutanen Yahuda da na Urushalima ga mutanen Hellenawa, don ku aika da su nesa da ƙasarsu.

7 “Duba, zan dawo da su daga wuraren da kuka sayar da su, in kuma yi muku abin da kuka yi musu. 8 Zan sayar da ’ya’yanku maza da mata ga mutanen Yahuda, su kuma za su sayar da su ga mutanen Sabenawa, al’umma da take nesa da ku.” Ubangiji ya faɗa.

9 Ku yi shelar wannan ga al’ummai.

Ku yi shirin yaƙi!

Ku tā da jarumawa!

Bari mayaƙa su ja kusa su kai hari.

10 Ku bubbuge garemaninku su zama takuba

da kuma laujenku su zama māsu.

Bari raunana su ce,

“Ni mai ƙarfi ne!”

11 Ku gaggauta, dukanku al’ummai daga kowane ɓangare,

ku tattaru a can.

Ka sauko da mayaƙanka, ya Ubangiji!

12 “Bari a tā da dukan al’ummai;

bari su kutsa zuwa Kwarin Yehoshafat

gama a can zan zauna

in shari’anta dukan al’ummai daga kowane ɓangare.

13 Ku fito da lauje,

gama girbi ya nuna.

Ku zo, ku tattaka inabin,

gama wurin matsewar ruwan inabi ya cika

randunan tarawa kuma sun cika har suna zuba,

muguntarsu da girma take!”

14 Dubun dubbai

suna a cikin kwarin yanke shawara!

Gama ranar Ubangiji ta yi kusa

a cikin kwarin yanke shawara.

15 Za a duhunta rana da wata,

taurari kuma ba za su ba da haske ba.

16 Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona

tsawa kuma daga Urushalima;

duniya da sararin sama za su yi rawan jiki.

Amma Ubangiji zai zama mafakar mutanensa,

mafaka ga mutanensa Isra’ila.

17 “Sa’an nan za ku san cewa ni, Ubangiji Allahnku,

ina zaune a Sihiyona, dutsena mai tsarki.

Urushalima za tă zama mai tsarki;

baƙi ba za su ƙara mamaye ta ba.

18 “A wannan rana duwatsu za su ɗiga da sabon ruwan inabi,

tuddai kuma za su malmalo madara;

dukan rafuffukan Yahuda za su yi ta gudano da ruwa.

Maɓulɓula kuma za tă fito daga gidan Ubangiji

haka ma ruwa a kwarin itatuwan ƙirya.

19 Amma Masar za tă zama kango,

Edom kuma hamada marar amfani,

saboda kama-karyar da aka yi wa mutanen Yahuda,

a ƙasar da aka zub da jinin marasa laifi.

20 Za a zauna a Yahuda har abada

Urushalima kuma daga tsara zuwa tsara.

21 Alhakin jininsu, wanda ban gafarta ba,

zan gafarta.”

Ubangiji yana zama a Sihiyona!