Sashe na 10: Mulkin Uzziya
Masarautar Yahuda
Farkon Mulkin Uzziya da Wadatarsa
810 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Sai dukan mutanen Yahuda suka ɗauki Uzziya wanda yake da shekara goma sha shida da haihuwa, suka naɗa shi sarki a madadin mahaifinsa Amaziya. 2 Shi ne wanda ya sāke gina Elot ya kuma mai da shi ga Yahuda bayan Amaziya ya huta tare da kakanninsa.
3 Uzziya yana da shekara goma sha shida sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyu. Sunan mahaifiyarsa Yekoliya ce; ita daga Urushalima ce. 4 Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar dai yadda mahaifinsa Amaziya ya yi.
1 A shekara ta ashirin da bakwai ta mulkin Yerobowam sarkin Isra’ila, Azariya ɗan Amaziya, sarkin Yahuda ya fara mulki.
5 Ya nemi Allah a kwanakin Zakariya, wanda ya koyar da shi a tsoron Allah. Muddin ya nemi Ubangiji, Allah ya ba shi nasara.
6 Ya yi yaƙi da Filistiyawa ya kuma rushe katangar Gat, Yabne da kuma Ashdod. Sa’an nan ya sāke gina garuruwa kusa da Ashdod da sauran wurare a cikin Filistiyawa. 7 Allah ya taimake shi a kan Filistiyawa da kuma a kan Larabawa waɗanda suke zama a Gur-Ba’al da kuma a kan Meyunawa. 8 Ammonawa suka kawo haraji wa Uzziya, sunan da ya yi kuwa ya bazu har iyakar Masar, domin ya zama mai iko sosai.
9 Uzziya ya gina hasumiyoyi a Urushalima a Ƙofar Kusurwa, a Ƙofar Kwari da kuma a kusurwar katanga, ya kuma yi musu katanga. 10 Ya gina hasumiyoyi a hamada ya kuma haƙa rijiyoyi masu yawa, gama yana da dabbobi masu yawa a gindin duwatsu da kuma a kwari. Yana da mutane masu yin masa aiki a gonakinsa da gonakin inabinsa a tuddai da kuma a ƙasashe masu dausayi, gama yana son noma.
11 Uzziya ya kasance da gogaggun mayaƙa, a shirye su fito ɓangarori-ɓangarori bisa ga yawansu yadda Yehiyel magatakarda, da Ma’asehiya jarumi, suka karkasa su bisa ga umarnin Hananiya, ɗaya daga cikin fadawa. 12 Yawan shugabannin iyali a bisa jarumawa sun kai 2,600. 13 A ƙarƙashin shugabancinsu akwai mayaƙa 307,500 horarru don yaƙi, mayaƙa masu ƙarfi don su taimaki sarki a kan abokan gābansa. 14 Uzziya ya tanada garkuwoyi, māsu, hulunan kwano, kayan sulke, baka da majajjawa don mayaƙan gaba ɗaya. 15 A Urushalima ya yi na’urori da gwanaye suka sarrafa don amfani a hasumiyoyi da kuma a kusurwar kāriya don harbin kibiyoyi da jefan manyan duwatsu. Sunansa ya bazu ko’ina, gama ya sami taimako sosai har ya zama mai iko.
Yowel Ya Annabta Kifar da Yahuda wajen 787 kafin haihuwar Almasihu
Sa’ad da Uzziya ya ƙara yawan sojojinsa, Yowel ya annabta cewa wata rana rundunar baƙi za ta kifar da masarautar Yahuda.
1 Maganar Ubangiji wadda ta zo wurin Yowel ɗan Fetuwel.
2 Ku ji wannan, ku dattawa,
ku kasa kunne, dukan waɗanda suke zaune a ƙasar.
Ko wani abu makamancin haka ya taɓa faruwa a kwanakinku
ko a kwanakin kakanninku?
3 Ku faɗa wa ’ya’yanku,
bari kuma ’ya’yanku su faɗa wa ’ya’yansu,
’ya’yansu kuma su faɗa wa tsara ta gaba.
4 Abin da ɗango ya bari
fāri masu girma sun cinye;
abin da fāri masu girma suka bari,
burduduwa ta cinye;
abin da burduduwa ta bari sauran kwari sun cinye.
5 Ku farka, ku bugaggu, ku yi kuka!
Ku yi kuka da ƙarfi, ku dukan mashayan ruwan inabi;
ku yi kuka mai ƙarfi saboda sabon ruwan inabi,
gama an riga an ƙwace ta daga leɓunanku.
6 Wata al’umma ta mamaye ƙasata,
tana da ƙarfi ba ta kuma ƙidayuwa;
tana da haƙoran zaki,
da zagar zakanya.
7 Ta mayar da kuringar inabina kango
ta kuma lalatar da itatuwan ɓaurena.
Ta ɓamɓare bayansu duka
ta kuma jefar da su
ta bar rassansu fari fat.
8 Ku yi makoki kamar budurwa
a cikin tsummoki
tana baƙin ciki domin mijinta na ƙuruciyarta.
9 Hadayun hatsi da hadayun sha
an yanke su daga gidan Ubangiji.
Firistoci suna makoki,
su waɗanda suke yi wa Ubangiji hidima.
10 Filaye sun zama marasa amfani,
ƙasa ta bushe;
an lalatar da hatsi,
sabon ruwan inabin ya bushe,
mai kuma ba amfani.
11 Ku fid da zuciya, ku manoma,
ku yi ihu, ku masu noma inabi;
ku yi baƙin ciki saboda alkama da sha’ir,
saboda an lalata girbin filaye.
12 Kuringar inabin ta bushe
itacen ɓaure kuma ya yi yaushi,
’ya’yan rumman, itacen dabino da itacen gawasa,
dukan itatuwan filaye, sun bushe.
Tabbatacce farin cikin ’yan adam
ya bushe.
13 Ku sa tsummoki, ya firistoci, ku yi makoki;
ku yi ihu, ku da kuke yin hidima a gaban bagade.
Zo, ku kwana saye da tsummoki,
ku waɗanda kuke yi wa Allahna hidima,
gama an yanke hadayun hatsi da hadayun sha
daga gidan Allahnku.
14 Ku yi shelar azumi mai tsarki;
ku kira tsarkakan taro.
Ku kira dattawa
da kuma dukan mazaunan ƙasar
zuwa gidan Ubangiji Allahnku,
ku kuma yi kuka ga Ubangiji.
15 Kaito saboda wannan rana!
Gama ranar Ubangiji ta kusa,
za tă zo kamar hallaka daga wurin Maɗaukaki.
16 Ba a yanke abinci
a idanunmu,
farin ciki da kuma murna
daga gidan Allahnmu ba?
17 Iri suna ta yanƙwanewa
a busasshiyar ƙasa
Ɗakunan ajiya sun lalace,
an rurrushe rumbunan hatsin,
gama hatsi ya ƙare.
18 Ji yadda dabbobi suke nishi!
Garkunan shanu sun ruɗe
saboda ba su da ciyawa,
har garkunan tumaki ma suna shan wahala.
19 A gare ka, ya Ubangiji, nake kira,
gama wuta ta cinye wurin kiwo
harshen wuta kuma ya ƙone dukan itatuwan jeji.
20 Har ma namun jeji suna haki gare ka;
rafuffuka sun bushe
wuta kuma ta cinye wurin kiwo a jeji.