An Bugi Uzziya da Kuturta
787 ko 765 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
16 Amma bayan Uzziya ya zama mai iko, sai ɗaga kai ya kai shi ga fāɗuwa. Bai yi aminci ga Ubangiji Allahnsa ba, ya kuma shiga haikalin Ubangiji don yă ƙone turare a bagaden turare. 17 Azariya firist tare da waɗansu firistoci tamanin na Ubangiji masu ƙarfin hali suka bi shi ciki. 18 Suka kalubalance shi suka ce, “Ba daidai ba ne, Uzziya, ka ƙone turare ga Ubangiji. Wannan aikin firistoci zuriyar Haruna ne, waɗanda aka tsarkake don ƙone turare. Ka bar wuri mai tsarki, gama ka kasance marar aminci; kuma Ubangiji Allah ba zai girmama ka ba.”
19 Uzziya wanda yake da farantin wuta a hannunsa a shirye don ƙone turare, ya husata. Yayinda yake fushi da firistocin a gabansu a gaban bagaden turare a haikalin Ubangiji, sai kuturta ta faso a goshinsa. 20 Sa’ad da Azariya babban firist da dukan sauran firistoci suka dube shi, sai suka ga cewa yana da kuturta a goshinsa, saboda haka suka gaggauta tunkuɗa shi waje nan da nan. Tabbatacce, shi kansa ma ya yi marmari yă bar wurin domin Ubangiji ya buge shi.
21 Sarki Uzziya ya kasance da kuturta har ranar mutuwarsa. Ya zauna a gidan da aka ware, da kuturci, aka kuma ware shi daga haikalin Ubangiji. Yotam ɗansa ya lura da fadan ya kuma yi mulkin mutanen ƙasar.
An Naɗa Ishaya Annabi 758 kafin haihuwar Almasihu
1 Wahayi game da Yahuda da Urushalima wanda Ishaya ɗan Amoz ya gani a zamanin da Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, suka yi mulkin Yahuda.
1 A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali. 2 A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi. 3 Suna kiran juna,
“Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne;
duniya ta cika da ɗaukakarsa.”
4 Da jin ƙarar muryoyinsu madogarai da madogaran ƙofa suka girgiza, haikali kuma ya cika da hayaƙi.
5 Sai na tā da murya na ce, “Kaitona! Na shiga uku! Gama ni mutum ne mai leɓuna marar tsarki, kuma ina raye a cikin mutane masu leɓuna marasa tsarki, idanuna kuma sun ga Sarki, Ubangiji Maɗaukaki.”
6 Sai ɗaya daga cikin serafofin ya yi firiya zuwa wurina tare da garwashi mai wuta a hannunsa, wanda ya ɗiba da arautaki daga bagade. 7 Da shi ne ya taɓa bakina ya ce, “Duba, wannan ya taɓa leɓunanka, yanzu fa an kawar da laifofinka, an kuma gafarta maka zunubanka.”
8 Sa’an nan na ji muryar Ubangiji tana cewa, “Wa zan aika? Wa zai tafi mana?”
Sai na ce, “Ga ni! Ka aike ni!”
9 Ya ce, “Je ka ka faɗa wa wannan mutane,
“ ‘Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba;
Kome yawan dubar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.’
10 Ka sa zuciyar mutanen nan ta dushe;
kunnuwansu su kurunce,
idanunsu kuma su makance.
In ba haka ba za su iya gani da idanunsu,
su ji da kunnuwansu,
su fahimta da zuciyarsu,
su kuma juyo a kuma warkar da su.”
11 Sa’an nan na ce, “Har yaushe, ya Ubangiji?”
Ya kuma amsa,
“Sai an lalatar da biranen
ba kowa a ciki,
sai an mai da gidaje kangwaye
ƙasa kuma ta zama kango ba amfani,
12 sai lokacin da Ubangiji ya kori kowa
aka kuma yashe ƙasar gaba ɗaya.
13 Ko da yake kashi ɗaya bisa goma zai ragu a ƙasar,
za tă sāke zama kango.
Amma kamar yadda katambiri da itacen oak
sukan bar kututturai sa’ad da aka yanke su,
haka iri mai tsarkin nan zai zama kututture a ƙasar mai tsarki.”
1 Ga abin da Ishaya ɗan Amoz ya gani game da Yahuda da Urushalima.
2 A kwanaki masu zuwa
za a kafa dutsen haikalin Ubangiji
a matsayin babba cikin duwatsu;
za a daga shi bisa tuddai,
kuma dukan al’ummai za su bumbunto zuwa gare shi.
3 Mutane da yawa za su zo su ce,
“Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji,
zuwa gidan Allah na Yaƙub.
Zai koya mana hanyoyinsa,
domin mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.”
Dokar za tă fito daga Sihiyona,
maganar Ubangiji daga Urushalima.
4 Zai shari’anta tsakanin al’ummai
zai kuma sulhunta faɗar mutane masu yawa.
Za su mai da takubansu su zama garemani
māsunsu su zama wuƙaƙen askin itatuwa.
Al’umma ba za tă ƙara ɗauki takobi a kan al’umma ba,
ba kuwa za su ƙara yin horarwar yaƙi.
5 Ki zo, ya gidan Yaƙub,
bari mu yi tafiya a hasken Ubangiji.
6 Ka rabu da mutanenka,
gidan Yaƙub.
Sun cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas;
suna yin duba kamar Filistiyawa
suna tafa hannuwa tare da marasa sanin Allah.
7 Ƙasarsu ta cika da azurfa da zinariya;
dukiyarsu kuma ba iyaka.
Ƙasarsu ta cika da dawakai;
kekunan yaƙinsu kuma ba iyaka.
8 Ƙasarsu ta cika da gumaka;
sukan rusuna ga aikin hannuwansu,
ga abin da yatsotsinsu suka yi.
9 Saboda an jawo mutum ƙasa
aka kuma ƙasƙantar da ɗan adam,
kada ku gafarta musu.
10 Ku tafi cikin duwatsu,
ku ɓuya cikin ƙasa
daga razanar Ubangiji
da kuma darajar ɗaukakarsa!
11 Za a ƙasƙantar da mai girman kai
za a kuma lalatar da fariyar masu ɗaga kai;
Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana.
12 Ubangiji Maɗaukaki yana da rana ajiye
domin dukan masu girman kai da masu fariya
domin dukan waɗanda aka ɗaukaka
(zai kuwa ƙasƙantar da su),
13 domin dukan al’ul na Lebanon, masu tsayi da masu fariya,
da kuma dukan itatuwan oak na Bashan,
14 domin dukan dogayen duwatsu
da kuma tuddai masu tsayi,
15 domin kowace doguwar hasumiya
da kowace katanga mai ƙarfi,
16 domin kowane jirgin ruwan kasuwanci
da kuma jirgi mafi girma mafi kyau.
17 Za a jawo mai girman kai ƙasa
a kuma ƙasƙantar da mai ɗaga kai;
Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana,
18 za a kuma kawar da gumaka ƙaƙaf.
19 Mutane za su gudu zuwa kogwannin duwatsu
da kuma ramummuka a ƙasa
daga razanar Ubangiji
da kuma darajar ɗaukakarsa,
sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.
20 A wannan rana mutane za su zubar wa
jaba da jamage
gumakansu na azurfa da gumakansu na zinariya
da suka yi don su bauta musu.
21 Za su gudu zuwa kogwannin duwatsu
da kuma zuwa tsagaggun duwatsu
daga razanar Ubangiji
da kuma darajar ɗaukakarsa,
sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.
22 Ku daina dogara ga mutum,
wanda numfashi ne kawai yake da shi a hancinsa.
Wace daraja gare shi?