Yesu Ya Koyar da Taron Jama'a Masu Yawa Ya Kuma Warkar da Su a Bakin Teku
Yesu ya koyar da taron jama'a masu yawa ya kuma warkar da su a bakin Tekun Galili.
A nan muna ganin Kiristi yana zaɓar manzanni goma sha biyu yana kuma yi musu da taron jama'a Wa'azi a kan Dutse.
27 zuwa 29 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Mattiyu 12:15–21
12:15 Da ya gane wannan, sai Yesu ya janye daga wurin. Da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da dukan masu ciwonsu,
16 yana jan musu kunne kada su faɗa wa kowa akan ko shi wane ne. 17 Wannan kuwa domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya ne cewa,
18 “Ga bawana da na zaɓa,
ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi;
zan sa Ruhuna a kansa,
zai kuma yi shelar adalci ga al’ummai.
19 Ba zai yi faɗa ko yă ɗaga murya ba,
ba kuwa wanda zai ji muryarsa a kan tituna.
20 Kyauron da ya tanƙwasa ba zai karye shi ba.
Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba,
sai ya jagoranci adalci zuwa ga nasara.
21 Cikin sunansa al’ummai za su dogara.”
Markus 3:7–12
3:7 Yesu da almajiransa suka janye zuwa tafkin, taro mai yawa kuwa daga Galili ya bi shi. 8 Mutane da yawa daga Yahudiya, da Urushalima, da Edom, da kuma yankunan da suke ƙetaren Urdun, da kewayen Taya, da Sidon suka zo wurinsa, don sun ji dukan abubuwan da yake yi. 9 Saboda taron, sai ya ce wa almajiransa su shirya masa ƙaramin jirgin ruwa, don kada mutane su matse shi.
10 Gama ya warkar da mutane da yawa, masu cututtuka suka yi ta ƙoƙarin zuwa gaba, don su taɓa shi. 11 Duk sa’ad da mugayen ruhohi suka gan shi, sai fāɗi a gabansa, su ɗaga murya, su ce, “Kai Ɗan Allah ne.”
12 Amma yakan tsawata musu, kada su shaida ko wane ne shi.
Yesu Ya Zaɓi Manzanni Goma Sha Biyu
Bayan ya shafe dare yana addu'a, Yesu ya zaɓi manzanni goma sha biyu.
Markus 3:13–19
3:13 Yesu ya hau gefen wani dutse, ya kira waɗanda yake so, suka kuma zo wurinsa.
14 Ya naɗa sha biyu, ya kira su manzanni don su kasance tare da shi, domin kuma yă aike su yin wa’azi, 15 don kuma su sami ikon fitar da aljanu.
16 Ga sha biyun da ya naɗa.
Siman (wanda ya ba shi suna Bitrus);
17 Yaƙub ɗan Zebedi da kuma ɗan’uwansa Yohanna (ga waɗannan kuwa ya sa musu suna Buwarnajis, wato, “’ya’yan tsawa”);
18 Andarawus,
Filibus,
Bartolomeyu,
Mattiyu,
Toma,
Yaƙub ɗan Alfayus,
Taddayus,
Siman wanda ake kira Zilot,
19 da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.
Luka 6:12–16
6:12 Wata rana, a cikin kwanakin nan, Yesu ya je wani dutse domin yă yi addu’a, ya kuma kwana yana addu’a ga Allah.
13 Da gari ya waye, sai ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya zaɓi guda goma sha biyu daga cikinsu, waɗanda ya kira su, Manzanni.
14 Siman (wanda ya kira Bitrus), ɗan’uwansa Andarawus,
Yaƙub,
Yohanna,
Filibus,
Bartolomeyu,
15 Mattiyu,
Toma,
Yaƙub ɗan Alfayus,
Siman wanda ake kira Zilot,
16 Yahuda ɗan Yaƙub,
da kuma Yahuda Iskariyot, wanda ya bashe Yesu.