Wa'azi a Kan Dutse
Wa'azi a kan Dutse: gata da abubuwan da ake bukata a mulkin Almasihu, da ma'aunin adalci na Kiristi.
Wani wuri mai shimfiɗa a kan dutse, ba da nisa da Kafarnahum ba
27 zuwa 29 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Mattiyu 5:1–8:1
Wurin da Masu Sauraro
5:1 Ganin taron mutane, sai ya hau kan gefen dutse ya zauna.
Almajiransa kuwa suka zo wurinsa, 2 sai ya fara koya musu.
Yana cewa,
Albarku da Kaitai
Gabatarwa: albarku da kaitai, gatan waɗanda suke ƙarƙashin mulkin Almasihu.
3 “Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu,
gama mulkin sama nasu ne.
4 Masu albarka ne waɗanda suke makoki,
gama za a yi musu ta’aziyya.
5 Masu albarka ne waɗanda suke masu tawali’u,
gama za su gāji duniya.
6 Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci,
gama za a ƙosar da su.
7 Masu albarka ne waɗanda suke masu jinƙai,
gama za a nuna musu jinƙai.
8 Masu albarka ne waɗanda suke masu tsabtar zuciya,
gama za su ga Allah.
9 Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci,
gama za a kira su ’ya’yan Allah.
10 Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci,
gama mulkin sama nasu ne.
11 “Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni.
12 Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.
Ma'aunin Adalci na Kiristi
Jigon wa’azin: ma’aunin adalci na Kiristi, sabanin na malaman Attaura da Farisiyawa.
13 “Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.
14 “Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa. 15 Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida. 16 Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.
17 “Kada ku yi tsammani na zo ne domin in kawar da Doka ko kuma Annabawa; ban zo domin in kawar da su ba ne, sai dai domin in ciccika su. 18 Gaskiya nake gaya muku, kafin sama da ƙasa sun shuɗe, babu ko ɗan wasali, babu wani ɗigo ta kowace hanya da zai ɓace daga Dokar, sai an cika kome. 19 Duk wanda ya karya ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta na umarnan nan, ya kuma koya wa waɗansu su yi haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a mulkin sama. Amma duk wanda ya aikata, ya kuma koyar da waɗannan umarnai, za a kira shi mai girma a cikin mulkin sama. 20 Gama ina faɗa muku cewa in dai adalcinku bai fi na Farisiyawa da na malaman dokoki ba, faufau, ba za ku shiga mulkin sama ba.
Ƙa’idodin ɗabi’a na Kiristi sun fi koyarwar malaman Attaura
Koyarwar Kiristi game da ɗabi’a ta fi ta malaman Attaura (duka Tsohon Alkawari da dokokin baka), a fannoni ko misalai shida: kisan kai, zina, saki, rantsuwa, ramuwar gayya, da ƙaunar abokan gāba.
21 “Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai; kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’ 22 Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘Raka,’ za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.
23 “Saboda haka, in kana cikin ba da baikonka a kan bagade, a can kuwa ka tuna cewa ɗan’uwanka yana riƙe da kai a zuci, 24 sai ka bar baikonka a can gaban bagade. Ka je ka shirya tukuna da ɗan’uwanka; sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.
25 “Ka yi hanzari ka shirya al’amura da maƙiyinka wanda yake ƙararka a kotu. Ka yi haka, tun kana tare da shi a kan hanya, in ba haka ba, zai miƙa ka ga alƙali, alƙali kuma yă miƙa ka ga ɗan sanda, mai yiwuwa kuwa a jefa ka a kurkuku. 26 Gaskiya nake gaya maka, ba za ka fita ba, sai ka biya kobo na ƙarshe.
27 “Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’ 28 Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa. 29 In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta. 30 In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.
31 “An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yă ba ta takardar saki.’ 32 Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.
33 “Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutane a dā, ‘Kada ka karya alkawarinka, sai dai ka cika alkawaran da ka yi wa Ubangiji.’ 34 Amma ina gaya muku, Kada ku yi rantsuwa sam, ko da sama, domin kursiyin Allah ne; 35 ko da ƙasa, domin matashin ƙafafunsa ne; ko kuma da Urushalima, domin birnin Babban Sarki ne. 36 Kada kuma ka rantse da kanka, domin ba za ka iya mai da ko gashi ɗaya yă zama fari ko baƙi ba. 37 Abin da ya kamata ku ce kawai, shi ne, I, ko A’a. Abin da ya wuce haka kuwa daga wurin Mugun nan yake.
38 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ido domin ido, haƙori kuma domin haƙori.’ 39 Amma ina gaya muku, Kada ku yi tsayayya da mugun mutum. In wani ya mare ka a kumatun dama, juya masa ɗayan ma. 40 In kuma wani yana so yă yi ƙararka yă ƙwace rigarka, to, ba shi mayafinka ma. 41 In wani ya tilasta ka yin tafiya mil ɗaya, to, tafi tare da shi mil biyu. 42 Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka.
43 “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka.’
44 Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a,
45 don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci.
46 In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba?
47 In kuwa kuna gai da ’yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba?
48 Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.
Adalci na gaskiya sabanin munafunci na riya
Aikata adalci na gaskiya, sabanin munafunci na riya na Farisiyawa, kamar a ba wa mabukata, addu’a, da azumi.
6:1 “Ku yi hankali kada ku nuna ‘ayyukanku na adalci’ a gaban mutane, don su gani. In kuka yi haka, ba za ku sami lada daga wurin Ubanku da yake cikin sama ba.
2 “Saboda haka sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yi shelarsa, yadda munafukai suke yi a majami’u da kuma kan tituna, don mutane su yabe su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. 3 Amma sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yarda hannun hagunka yă ma san abin da hannun damarka yake yi, 4 don bayarwarka ta zama a ɓoye. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.
5 “Sa’ad da kuma kuke addu’a, kada ku zama kamar munafukai, gama sun cika son yin addu’a a tsaye a cikin majami’u da kuma a bakin titi, don mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. 6 Amma sa’ad da kake addu’a, sai ka shiga ɗakinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu’a ga Ubanka wanda ba a gani. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka. 7 Sa’ad da kuma kuke addu’a, kada ku yi ta maimaita magana, kamar marasa sanin Allah, domin suna tsammani za a ji su saboda yawan maganarsu. 8 Kada ku zama kamar su, gama Ubanku ya san abin da kuke bukata kafin ma ku roƙe shi.
9 “To, ga yadda ya kamata ku yi addu’a.
“ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama,
a tsarkake sunanka,
10 mulkinka yă zo
a aikata nufinka a duniya
kamar yadda ake yi a sama.
11 Ka ba mu yau abincin yininmu.
12 Ka gafarta mana laifofinmu,
kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi.
13 Kada ka bari a kai mu cikin jarraba,
amma ka cece mu daga mugun nan. ’
14 Gama in kuna yafe wa mutane sa’ad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku. 15 Amma in ba kwa yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku ma ba zai gafarta muku zunubanku ba.
16 “Sa’ad da kuma kuna azumi, kada ku ɓata fuska, yadda munafukai suke yi. Sukan ɓata fuskokinsu domin su nuna wa mutane cewa suna azumi. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. 17 Amma sa’ad da kana azumi, ka shafa wa kanka mai, ka wanke fuskarka, 18 domin kada mutane su ga alama cewa kana azumi, sai dai Ubanka kaɗai wanda ba a gani; Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.
Miƙa kai ga Allah da zuciya ɗaya
Miƙa kai ga Allah da zuciya ɗaya, sabanin manufofin duniya da damuwoyinta.
19 “Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata. 20 Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata. 21 Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za tă kasance.
22 “Ido shi ne fitilar jiki. In idanunka suna da kyau, dukan jikinka zai cika da haske. 23 Amma in idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma zai cika da duhu. To, in hasken da yake a cikinka duhu ne, duhun ya wuce misali ke nan!
24 “Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai yă ƙi ɗaya, yă ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yă yi aminci ga ɗaya, sa’an nan yă rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah, ku kuma bauta wa kuɗi gaba ɗaya.”
25 “Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? 26 Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba? 27 Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya?
28 “Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa. 29 Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba. 30 In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya? 31 Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’ 32 Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu. 33 Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa. 34 Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.
Neman laifi, ko hukunta wasu
7:1 “Kada ku ba wa kowa laifi, don kada a ba ku laifi ku ma. 2 Gama da irin shari’ar da kuka yi wa waɗansu, da ita za a shari’anta ku. Mudun da kuka yi awo da shi, da shi za a yi muku.
3 “Don me kake duban ɗan tsinken da yake idon ɗan’uwanka, alhali kuwa ga gungume a naka ido?
4 Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Bari in cire maka ɗan tsinken nan daga idonka,’ alhali kuwa a kowane lokaci akwai gungume a naka ido? 5 Kai munafuki, fara cire gungumen da yake idonka, a sa’an nan ne za ka iya gani sosai yadda za ka cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka.
6 “Kada ku ba karnuka abin da yake mai tsarki; kada kuma ku jefa wa aladu lu’ulu’anku. In kuka yi haka za su tattake su, sa’an nan su juyo su jijji muku ciwo.
Addu’a da ƙa’idar zinariya
7 “Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. 8 Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.
9 “Wane ne a cikinku in ɗansa ya roƙe shi burodi, sai yă ba shi dutse? 10 Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yă ba shi maciji? 11 In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba!
12 Saboda haka, duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Doka da koyarwar Annabawa sun ƙunsa.
Wa’azin ya ƙare da labaran misali masu matuƙar tasiri
Kammalawar wa’azin: darasin adalcin mutum, wanda aka jaddada ta hanyar labaran misali masu matuƙar tasiri.
13 “Ku shiga ta matsattsiyar ƙofa. Gama ƙofar zuwa hallaka faɗaɗɗiya ce mai sauƙin bi kuma, masu shiga ta cikinta kuwa suna da yawa. 14 Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne.
15 “Ku yi hankali da annabawan ƙarya. Sukan zo muku da kamannin tumaki, amma daga ciki mugayen kyarketai ne. 16 Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya? 17 Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da ’ya’ya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.
18 Itace mai kyau ba ya ba da munanan ’ya’ya, haka kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.
19 Duk itacen da ba ya ba da ’ya’ya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta.
20 Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.”
21 “Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama. 22 Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’ 23 Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’
24 “Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse.
25 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse.
26 Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. 27 Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”
28 Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai taron mutanen suka yi mamakin koyarwarsa, 29 domin ya koyar kamar wani wanda yake da iko, ba kamar malamansu na dokoki ba.
8:1 Da ya sauko daga dutsen, sai taron mutane mai yawan gaske suka bi shi.
Luka 6:17–30, 32–42, 31, 43–49
Wurin da Masu Sauraro
6:17 Sai ya sauko tare da su, ya tsaya a wani fili. A can, akwai taro mai yawa na almajiransa, da kuma mutane masu yawan gaske daga ko’ina a Yahudiya, Urushalima da kuma Taya da Sidon da suke bakin teku, 18 waɗanda suka zo domin su ji shi, a kuma warkar da cututtukansu. Waɗanda suke fama da mugayen ruhohi kuwa aka warkar da su. 19 Kuma dukan mutane suka yi ƙoƙari su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.
Albarku da Kaitai
Gabatarwa: albarku da kaitai, gatan waɗanda suke ƙarƙashin mulkin Almasihu.
20 Da ya dubi almajiransa, sai ya ce,
“Masu albarka ne ku da kuke matalauta,
gama mulkin Allah naku ne.
21 Masu albarka ne ku da kuke jin yunwa yanzu,
gama za ku ƙoshi.
Masu albarka ne ku da kuke kuka yanzu,
gama za ku yi dariya.
22 Masu albarka ne sa’ad da mutane suka ƙi ku,
suka ware ku, suka zage ku,
suna ce da ku mugaye,
saboda Ɗan Mutum.
23 “Ku yi farin ciki a wannan rana, ku kuma yi tsalle don murna, saboda ladarku yana da yawa a sama. Gama haka kakanninsu suka yi wa annabawa.
24 “Amma kaitonku da kuke da arziki,
gama kun riga kun sami ta’aziyyarku.
25 Kaitonku da kuke ƙosassu yanzu,
gama za ku zauna da yunwa.
Kaitonku da kuke dariya yanzu,
gama za ku yi makoki da kuka.
26 Kaitonku sa’ad da dukan mutane suna magana mai kyau a kanku,
gama haka kakanninsu suka yi da annabawan ƙarya.
Ƙa’idodin ɗabi’a na Kiristi sun fi koyarwar malaman Attaura
Koyarwar Kiristi game da ɗabi’a ta fi ta malaman Attaura (duka Tsohon Alkawari da dokokin baka), a fannoni ko misalai shida: kisan kai, zina, saki, rantsuwa, ramuwar gayya, da ƙaunar abokan gāba.
27 “Amma ina faɗa muku, ku da kuke ji na, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku yi wa masu ƙinku alheri.
28 Ku albarkaci waɗanda suke la’anta ku, ku kuma yi wa waɗanda suke wulaƙanta ku addu’a. 29 In wani ya mare ka a wannan kumatu, juya masa ɗayan ma, in wani ya ƙwace maka babban riga, kada ma ka hana masa ’yar cikin ma. 30 Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema yă mayar maka.
32 “In kana ƙaunar masu ƙaunarka ne kawai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma suna ƙaunar waɗanda suke ƙaunarsu.
33 In kuma kana yin alheri ga masu yi maka ne kaɗai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma suna yin haka.
34 In kana ba da bashi ga mutanen da za su iya biyan ka ne kawai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma, suna ba da bashi ga masu zunubi, da fata za a biya su tsab. 35 Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ’ya’yan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye. 36 Ku zama masu jinƙai, kamar yadda Ubanku mai jinƙai ne.
Neman laifi, ko hukunta wasu
37 “Kada ku ɗora wa wani, ku ma ba za a ɗora muku ba. Kada ku yanke wa wani hukunci, ku ma ba za a yanke muku ba. Ku gafarta, ku ma za a gafarta muku. 38 Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yă yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku.”
39 Ya kuma faɗa musu wannan misali cewa, “Makaho yana iya jagoran makaho ne? Ba sai dukansu biyu su fāɗa a rami ba? 40 Ɗalibi bai fi malaminsa ba, sai dai kowane ɗalibi wanda ya sami cikakkiyar koyarwa, zai zama kamar malaminsa.
41 “Don me kake duban ɗan tsinke da yake idon ɗan’uwanka, amma ba ka kula da gungumen da yake a naka ido ba?
42 Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Ɗan’uwa, bari in cire maka ɗan tsinke da yake idonka,’ alhali kuwa, kai kanka ka kāsa ganin gungumen da yake a naka ido? Kai munafuki! Ka fara cire gungumen daga idonka, sa’an nan za ka iya gani sosai, ka kuma cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka.”
Addu’a da ƙa’idar zinariya
31 Ka yi wa waɗansu abin da kai kake so su yi maka.
Wa’azin ya ƙare da labaran misali masu matuƙar tasiri
Kammalawar wa’azin: darasin adalcin mutum, wanda aka jaddada ta hanyar labaran misali masu matuƙar tasiri.
43 “Ba itace mai kyau da yake ba da munanan ’ya’ya. Mummunan itace kuma ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.
44 Kowane itace da irin ’ya’yansa ne ake saninsa. Mutane ba sa tsinke ’ya’yan ɓaure daga ƙaya, ko kuwa ’ya’yan inabi daga sarƙaƙƙiya.
45 Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne.”
46 “Don me kuke ce da ni, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ amma ba kwa yin abin da na faɗa?
47 Zan nuna muku kwatancin mutumin da yakan zo wurina, yă ji kalmomina, yă kuma aikata.
48 Yana kama da mutumin da ya gina gida, wanda ya haƙa ƙasa da zurfi, sa’an nan ya kafa tushen ginin a kan dutse. Da ambaliyar ruwa ta taso, ƙarfin ruwa kuwa ya buga gidan, wannan bai jijjiga shi ba, domin an yi masa tushen gini na ainihi.
49 Amma wanda yakan ji kalmomina, ba ya kuma aikata su, yana kama da mutumin da ya gina gida a ƙasa, ba tare da ya kafa tushen gini ba. A sa’ad da ƙarfin ruwa ya buga gidan, sai gidan yă rushe, mummunar rushewa kuwa.”