Almajiran Sun Tsinki Hatsi a Ranar Asabbaci
Wata gardama kuma game da Asabbaci da Farisiyawa, sa'ad da almajiran suka tsinki kawunan hatsi a gonaki.
Da alama a Galili a hanyar dawowa daga Urushalima
27 zuwa 29 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Mattiyu 12:1–8
12:1 A lokacin nan Yesu ya bi ta gonakin hatsi a ranar Asabbaci. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara kakkarya kan hatsi suna ci.
2 Sa’ad da Farisiyawa suka ga wannan, sai suka ce masa, “Duba! Almajiranka suna yin abin da doka ta hana a yi a ranar Asabbaci.”
3 Sai ya amsa ya ce, “Ba ku karanta abin da Dawuda ya yi ba ne sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa?
4 Ya shiga gidan Allah, da shi da abokan tafiyarsa suka ci keɓaɓɓen burodin, wanda doka ta hana su yi, sai firistoci kaɗai. 5 Ko kuwa ba ku karanta a Doka cewa a ranar Asabbaci firistoci sukan karya dokar Asabbaci duk da haka ba da yin wani laifi ba? 6 Ina faɗa muku cewa wani wanda ya fi haikali yana a nan.
7 Da a ce kun san abin da waɗannan kalmomi suke nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,’ da ba ku zargi marar laifi ba.
8 Gama Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabbaci.”
Markus 2:23–28
2:23 Wata ranar Asabbaci, Yesu yana ratsa gonakin hatsi, sai almajiransa da suke tafiya tare da shi, suka fara kakkarya waɗansu kan hatsi.
24 Farisiyawa suka ce masa, “Duba, me ya sa suke yin abin da doka ta hana a yi, a ranar Asabbaci?”
25 Ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba, sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa, suna kuma cikin bukata?
26 Ya shiga gidan Allah a zamanin Abiyatar babban firist, ya ci keɓaɓɓen burodin nan, ya kuma ba wa abokan tafiyarsa abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka?”
27 Sai ya ce musu, “An yi Asabbaci saboda mutum ne, ba mutum saboda Asabbaci ba.
28 Don haka, Ɗan Mutum Ubangiji ne, har ma da na Asabbaci.”
Luka 6:1–5
6:1 A wata ranar Asabbaci, Yesu yana bi ta gonakin hatsi, sai almajiran suka fara kakkarya kan hatsi suna murjewa a hannuwansu suna ci.
2 Sai waɗansu Farisiyawa suka ce, “Me ya sa kuke yin abin da doka ta hana yi a ranar Asabbaci?”
3 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi, sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa ba?
4 Ya shiga gidan Allah, ya ɗauki keɓaɓɓen burodi, sa’an nan ya ci abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka. Ya kuma ba wa abokan tafiyarsa?”
5 Sai Yesu ya ce musu, “Ai, Ɗan Mutum ne Ubangijin Asabbaci.”
Yesu Ya Warkar da Shanyayyen Hannu a Ranar Asabbaci
Gardama ta uku game da Asabbaci da Farisiyawa, a kan warkar da wani mutum mai shanyayyen hannu a wata majami'a.
A Galili
Mattiyu 12:9–14
12:9 Da ya ci gaba daga wurin, sai ya shiga majami’arsu, 10 a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?”
11 Ya ce musu, “In waninku yana da tunkiya, ta kuma fāɗa a rami ran Asabbaci, ba zai cire ta daga ramin ba?
12 Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja! Saboda haka ya dace a aikata alheri ran Asabbaci.”
13 Sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙa hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye, kamar dai ɗayan.
14 Amma Farisiyawa suka fita suka ƙulla shawara yadda za su kashe Yesu.
Markus 3:1–6
3:1 Wani lokaci, da ya sāke shiga majami’a, sai ga wani mutum mai shanyayyen hannu.
2 Waɗansu daga cikin mutane suna neman dalilin zargin Yesu, sai suka zuba masa ido, su ga ko zai warkar da shi a ranar Asabbaci.
3 Yesu ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.”
4 Sai Yesu ya tambaye su ya ce, “Me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri, ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a yi kisa?” Amma suka yi shiru.
5 Sai ya kalle su da fushi, don taurin zuciyarsu ya ɓata masa rai sosai. Sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.
6 Sai Farisiyawa suka fita, suka fara ƙulla shawara da mutanen Hiridus yadda za su kashe Yesu.
Luka 6:6–11
6:6 A wata ranar Asabbaci kuma, Yesu ya shiga majami’a yana koyarwa. To, a nan kuwa akwai wani mutumin da hannun damansa ya shanye.
7 Farisiyawa da malaman dokoki suka zuba wa Yesu ido, su ga ko zai warkar a ranar Asabbaci, don su sami dalilin zarginsa.
8 Amma Yesu ya san abin da suke tunani. Sai ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, “Tashi ka tsaya a gaban kowa.” Sai ya tashi ya tsaya.
9 Yesu ya ce musu, “Ina tambayarku, me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a hallaka shi?”
10 Sai ya kalle su duka, sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙe, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.
11 Amma Farisiyawa da malaman Doka suka fusata, suka fara tattauna da junansu a kan abin da za su yi wa Yesu.