Ku Yi Koyi da Allah Ku Yi Rayuwa Kamar ’Ya’yan Haske
Bulus ya ci gaba da ƙarfafa su game da yadda za su yi rayuwa, ya kuma sāke yi musu gargaɗi game da mugayen motsin zuciya waɗanda za su iya ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai ko su sa su rasa shi. Ya hana fushi a kowane irin salo, ya kuma ƙarfafa su su yi wa juna alheri su taimaki juna, su zama masu tausayi, suna gafarta laifofi da zarar an amince da su, kamar yadda Allah ta wurin Kiristi ya gafarta musu. Su yi koyi da Allah cikin waɗannan abubuwa a matsayin ’ya’yansa ƙaunatattu, kowane aikinsu a rayuwa yana fitowa daga ƙaunar juna, saboda mafificiyar ƙaunar Kiristi, wanda ya ba da kansa hadayar zunubi da hadayar kafara ga Allah dominmu. Domin ya ƙara bayyana abin da yake nufi, ya kuma nuna cewa ƙaunar da yake ƙarfafa su gare ta mai tsabta ce kuma mai alheri, nan take Bulus ya hana fasikanci da kowane irin ƙazanta da ƙarfi (waɗanda Afisawa marasa tuba suka fi tsunduma cikinsu), tare da kowane irin rashin kunya cikin tunani ko magana, domin ba su dace da halin Kirista ba, wanda yake bukatar kalmomin yabo da godiya. Bulus ya gargaɗi Afisawa kada masana falsafarsu su yaudare su a waɗannan al’amura, domin su ne manyan masu inganta irin waɗannan munanan ayyuka. Lalle hukuncin Allah zai zo musu, saboda haka kada su yi tarayya cikin halayensu kamar yadda suke yi a dā. Sa’ad da suke cikin duhu sun aikata irin waɗannan mugayen abubuwa; amma yanzu da suka zo ga hasken bisharar Kiristi, ana bukatar su yi rayuwa kamar ’ya’yan haske, cikin ayyukan Ruhu, suna tabbatar da abin da yake faranta wa Allah rai ta wurin halayensu. Kada su yi tarayya ko kaɗan da arna cikin bautarsu, amma su tsawata musu saboda bukukuwan asirinsu, waɗanda ake yi cikin duhu da ɓoye, waɗanda ko ambatonsu abin kunya ne. Haske yana fallasa tsananin zunubin dukan ayyukan duhu. Saboda haka, da yake bishara tana hukunta waɗannan bukukuwan asiri, tana kuma nuna musu muguntarsu, bisharar da kanta haske ce, wadda take kiran dukan waɗanda suke cikin duhu su farka su karɓi haskenta.
61 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
31 Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. 32 Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.
5:1 Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ’ya’ya, 2 ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.
3 Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba. 4 Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana, ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya. 5 Ku dai tabbata, ba wani mai fasikanci, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah. 6 Kada wani yă ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya. 7 Saboda haka kada ku haɗa kai da su.
8 Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar ’ya’yan haske 9 (domin amfanin haske ya ƙunshi nagarta, adalci, da kuma gaskiya) 10 ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji. 11 Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su. 12 Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye. 13 Duk abin da aka kawo a gaban haske ana iya ganinsa, kuma duk abin da aka haskaka yakan zama haske. 14 Shi ya sa aka ce,
“Ka farka, ya kai mai barci,
ka tashi daga matattu,
Kiristi kuwa zai haskaka ka.”
A Cika Ku da Ruhu, Ba da Ruwan Inabi Ba
Bulus yana ƙarfafa Afisawa, a matsayinsu na ’ya’yan haske, su yi tafiyarsu a hankali bisa ƙa’idoji da koyarwar bishara, ba bisa hanyar Al’ummai marasa hikima ba, amma kamar waɗanda aka koya wa hikima ta gaskiya, suna amfani da lokacin da suke da shi yadda ya kamata domin su iya maido da wani abu daga cikin abin da aka rasa; gama gwaje-gwaje da tsanantawar da ke kewaye da su suna jefa rayukansu da ’yancinsu cikin haɗari. Da yake nuni ga asirtattun bukukuwan bautar Bakus, ya umarce su kada su zama wawaye ko su zama kamar mahaukata, amma su san aikinsu sosai don su iya yin sa, domin kada su bugu da ruwan inabi a waɗannan bukukuwan arna, abin da ke kaiwa ga lalata. Idan suna son yin farin ciki, to su cika da Ruhun Allah; kuma maimakon waƙoƙin ƙazanta da zunubi, su haɗa kai wajen rera zabura da waƙoƙin yabo na ruhaniya, ba da leɓunansu kaɗai ba amma da zukatansu, suna gode wa Allah a kowane hali ta wurin sunan Yesu Kiristi mai iko. A al’amuran da ba na daidai ba ne kuma ba na kuskure ba ne, kowa ya miƙa kai ya kuma janye ra’ayinsa, domin kada a dagula zaman lafiyar jama’a, suna tunawa kullum cewa Allah ya umarce su su ƙaunaci juna.
15 Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16 Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne. 17 Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji. 18 Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19 Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20 Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.
21 Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi.
Mata da Mazaje, Kiristi da Ikilisiya
Daga maganar yadda mutane suke miƙa kai ga juna, Bulus ya ci gaba da ƙara bayyana aikinsu a cikin dangantaka ta kusa ta rayuwa. Ya ƙarfafa mata su miƙa kai ga mazajensu bisa tsarin Allah, gama miji shi ne kai, ko mai mulkin matarsa, kamar yadda Kiristi yake kai, ko mai mulkin jikinsa, wato ikilisiya. Kamar yadda Kiristi yake amfani da ikonsa bisa ikilisiya domin kiyaye ta da kāre ta, haka miji zai biya bukatun matarsa ya kuma kāre ta; kuma kamar yadda ikilisiya take ƙarƙashin Kiristi, haka ake bukatar mata ta yi wa mijinta biyayya. Ya ƙarfafa mazaje su ƙaunaci matansu kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci amaryarsa, wato ikilisiya; kuma domin ya nuna irin sadaukarwar wannan ƙauna, ya jero dukan abin da Kiristi ya yi da wahalar da ya sha saboda ikilisiya, domin ya shirya ta don kansa, tsarkakakkiya kuma cikakkiya. Sai ya kira dukan mazaje su ƙaunaci matansu haka nan, su kuma nuna irin wannan ƙauna mai ƙwazo da kulawa da lafiyarsu ta ruhaniya kamar yadda Kiristi ya yi wa jikinsa, wato ikilisiya. Sa’an nan, da yake magana game da iyayenmu na farko, ya bayyana cewa, tun da mace tana zama jiki ɗaya da mijinta ta wurin aure, wannan dalili ne na halitta da zai sa ya ƙaunace ta ya kuma kula da ita, kamar yadda Ubangiji yake ciyar da jikinsa, wato ikilisiya, wadda mutane suke gaɓoɓinta. Kuma kamar yadda auren Adamu yake wakiltar haɗin kai na har abada tsakanin Kiristi da masu bi, waɗanda saboda su ya bar Ubansa, haka nan mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa ya haɗu da matarsa yadda ba za a raba su ba. Haɗin kan ruhaniya tsakanin Kiristi da ikilisiyarsa babban asiri ne. Amma tun da Allah ne ya kafa aure, kowane mutum ya ƙaunaci matarsa a matsayin wani ɓangare na kansa, ita kuma mata ta tabbata tana ɗaukar mijinta a matsayin shugabanta da wanda yake bisa ta.
22 Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi. 23 Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa. 24 To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.
25 Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta. 26 Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa. 27 Kiristi ya yi haka don yă miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma mai tsarki, marar aibi, marar tabo, da kuma marar lahani. 28 Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne. 29 Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yă ciyar da shi, yă kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya, 30 gama mu gaɓoɓin jikinsa ne. 31 “Saboda haka mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su biyun su zama jiki ɗaya.” 32 Wannan babban asiri ne, amma na ɗauke shi a matsayin kwatanci ne na Kiristi da ikkilisiya. 33 Duk da haka, dole kowannenku yă ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar tă yi biyayya ga mijinta.
’Ya’ya da Iyaye, Masu Hidima da Iyayengiji
An umarci ’ya’ya su yi wa iyayensu biyayya, domin iyayen sun cancanci godiyarsu da ƙaunarsu. Wannan biyayya ce ga umarnin da Allah ya ba Musa, wanda Allah ya haɗa da alkawarin albarkun duniya domin ƙarin ƙarfafawa. Ubanni su kula kada su tsokani ’ya’yansu har su kai su ga rashin biyayya da fushi ta wurin tsananin da ya wuce kima, amma su yi musu gyara, su kuma rene su tun suna ƙanana cikin horo da ƙa’idoji da koyarwar bishara. An umarci masu hidima na kowane matsayi su yi wa iyayengijinsu biyayya a dukan al’amuran duniya, su kuma kula kada su ɓata musu rai, saboda sanin wajibinsu ga Kiristi. Kada masu hidima su gamsu da yin aikinsu kawai sa’ad da idanun iyayengijinsu suke kansu, kamar dai suna neman samun tagomashin mutane, amma su yi shi don biyayya ga nufin Allah, suna cika ayyukan matsayinsu da farin ciki a matsayin masu hidimar Kiristi, ba masu hidimar mutane kaɗai ba, suna sane cewa za su karɓi ladansu daga wurin Ubangiji. Ya ƙarfafa iyayengiji su bi da masu hidimarsu da irin wannan sanin ya kamata da aminci, bisa waɗannan ƙa’idojin addini, suna kauce wa yi musu hukunci, suna sane cewa dole ne su ba Ubangijinsu da ke sama lissafi, wanda ba zai nuna son kai wajen hukunta halittunsa ba, ko da wane irin bambanci ne yake tsakaninsu a nan.
1 Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. 2 Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, 3 don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”
4 Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.
5 Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya. Ku nuna musu halin bangirma, kuna kuma yin musu biyayya cikin dukan abu, da zuciya ɗaya kamar ga Kiristi kuke yi. 6 Ku yi aiki sosai, ba don kawai ku gamshe su sa’ad da suke kallonku ba. Da yake ku bayin Kiristi ne, ku aikata nufin Allah da dukan zuciyarku. 7 Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba. 8 Gama kun san cewa Ubangiji zai ba da lada ga kowa gwargwadon kowane aiki nagarin da ya yi, ko shi bawa ne, ko ’yantacce.
9 Ku kuma masu bayi, dole ku bi da bayinku da kyau. Ku daina ba su tsoro. Ku tuna, ku da su, Maigida ɗaya kuke da shi a sama, kuma ba ya nuna bambanci.
Ku Sa Dukan Kayan Yaƙin Allah
Bayan ya koya wa Afisawa ayyukansu da sanin maɗaukakiyar kiransu, Bulus ya ƙare wasiƙarsa da ƙarfafa su kada su dogara ga ƙarfinsu wajen cika waɗannan ayyuka, amma su sami ƙarfin ruhaniya wanda Allah kaɗai zai iya bayarwa, su kuma dogara da shi. Su sa dukan kayan yaƙin Allah, wato alheran bishara, domin idan sun lulluɓe da su, su iya tsayayya da hare-hare da makircin Iblis na wayo. Gama yaƙinsu ba da lalacewar halittarmu kaɗai ba ne, ko kuma da mutane, amma da ruhohi masu iko waɗanda a dā suke zaune a masarautun sama, suka kuma fāɗi daga matsayinsu na sama: masu mulkin duhun da ya cika duniya, da rukunonin mugunta na ruhaniya mafi girman matsayi. Tun da suna da irin waɗannan abokan gāba da za su yi yaƙi da su, sai su ɗauki dukan kayan yaƙin Allah domin su iya tsayawa a ranar haɗari; kuma ya yi addu’a cewa, bayan sun yi duk abin da za su iya, a same su a ƙarshen yaƙinsu suna tsaye da nasara cikin sahunsu. Saboda haka, domin su shirya wannan fafatawa, su ɗaura ɗamarar bisharar gaskiya a kugunsu, wadda za ta ba su damar gano abokan gābansu na ruhaniya; su sa sulken ƙirji, wato ƙa’idar adalci, wanda zai kāre su daga hare-harensu; su kuma sa takalma a ƙafafunsu domin su kasance a shirye su fuskanci kowace wahala da za ta iya hana su shelar bisharar sulhu tsakanin Allah da mutum. Fiye da duka, su ɗauki garkuwar bangaskiya, wato tabbatacciyar gaskata koyarwa da alkawuran bishara, wadda za ta kāre su sarai daga dukan kibiyoyi masu harshen wuta, ko jarabobi masu kisa, na abokan gābansu, ta kuma ba su ikon dusashe su ko dakatar da su; su kuma ɗauki kwalkwalin ceto, wato begen samun cikakkiyar kuɓuta, su riƙe takobin ruhaniya a hannunsu, wato maganar Allah, wadda aka bayyana ta wurin Ruhunsa Mai Tsarki.
10 A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi. 11 Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. 12 Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. 13 Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge. 14 Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku, 15 shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku. 16 Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. 17 Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.
18 A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a. 19 Ku kuma yi addu’a domina, don duk sa’ad da na buɗe bakina, in sami kalmomi babu tsoro, don in sanar da asirin bishara, 20 wadda nake jakadanta cikin sarƙoƙi. Ku yi addu’a don in iya yin shelarta babu tsoro, yadda ya kamata in yi.
Bulus Ya Aika Tikikus Ya Kuma Sa Musu Albarka
Domin Afisawa su san halinsa da yanayinsa a Roma, kuma da alama sosai saboda bai so ya danƙa labarin waɗannan abubuwa ga rubutu ba, Bulus ya aika Tikikus tare da wasiƙarsa saboda wannan dalili, domin su ji daga gare shi yadda al’amuransu su biyun suke, kuma domin Tikikus ya ƙarfafa zukatansu da labarin taimakon da Allah yake ba Bulus cikin wahalar da yake ciki yanzu. Ya ƙare da addu’a mai ƙwazo domin ’yan’uwa su sami salama ta ruhaniya da ƙaunar juna, bisa bangaskiyar da ta fito daga Allah da Kiristi, ya kuma yi addu’a cewa alherinsa ya kasance ba tare da su kaɗai ba amma tare da dukan masu bi waɗanda suke ƙaunar Ubangiji Yesu Kiristi da zuciya ɗaya.
21 Tikikus, ƙaunataccen ɗan’uwa da kuma amintaccen bawa cikin Ubangiji, zai faɗa muku kome, domin ku ma ku san yadda nake, da kuma abin da nake yi. 22 Na aike shi gare ku musamman don wannan, domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa ku.
23 ’Yan’uwa, salama tare da ƙauna da kuma bangaskiya daga Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi su kasance tare da ku.
24 Alheri yă tabbata ga dukan masu ƙaunar Ubangiji Yesu Kiristi da ƙauna marar ƙarewa.