Amos Ya Yi Annabci a Kan Al’ummai da Isra’ila

Amos ya sanar da hukunci a kan al’ummai maƙwabta, da kuma a kan Isra’ila da Yahuda.

793 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Amos 1–4

1 Kalmomin Amos, ɗaya daga cikin makiyayan Tekowa, abubuwan da ya gani game da Isra’ila shekaru biyu kafin a yi girgizar ƙasa, a lokacin da Uzziya yake sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yowash kuma yake sarkin Isra’ila.

2 Ya ce,

“Ubangiji ya yi ruri daga Sihiyona

ya kuma yi tsawa daga Urushalima;

wuraren kiwo duk sun bushe,

dutsen Karmel kuma ya yi yaushi.”

3 Ga abin da Ubangiji ya ce,

“Saboda zunubai uku na Damaskus,

har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.

Domin sun ci zalunci Gileyad

zalunci mai tsanani,

4 zan sa wuta a gidan Hazayel,

da za tă ƙona kagarun Ben-Hadad.

5 Zan kakkarye ƙofofin Bet-Damaskus;

zan hallaka sarkin da yake cikin Kwarin Awen

da kuma mai riƙe da sandar mulkin Bet-Eden.

Mutanen Aram za su je bauta a ƙasar Kir,”

in ji Ubangiji.

6 Ga abin da Ubangiji ya ce,

“Saboda zunubai uku na Gaza,

har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.

Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya

sun sayar wa Edom,

7 Zan aika da wuta a katangar Gaza

ta ƙone duk kagarunta.

8 Zan hallaka sarkin Ashdod

da kuma mai riƙe da sandar mulki na Ashkelon.

Zan hukunta Ekron,

har sai dukan Filistiyawa sun mutu,”

in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

9 Ga abin da Ubangiji ya ce,

“Saboda zunubai uku na Taya,

har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.

Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun kai su bauta a Edom,

ba su kula da yarjejjeniyar da aka yi ta zama kamar ’yan’uwa ba,

10 zan aika da wuta a Taya,

da za tă ƙone kagarunta.”

11 Ga abin da Ubangiji ya ce,

“Saboda zunubai uku na Edom,

har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba.

Don ya fafari ɗan’uwansa da takobi,

babu tausayi,

domin ya ci gaba da fusata

bai yarda yă huce daga fushinsa ba.

12 Zan aika wuta a Teman

da za tă ƙone kagarun Bozra.”

13 Ga abin da Ubangiji ya ce,

“Saboda zunubai uku na Ammon,

har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba.

Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu

don kawai yă ƙwace ƙasar.

14 Zan sa wuta a katangar Rabba

da za tă ƙone kagarunta

za a yi kururuwa a ranar yaƙi,

faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri.

15 Sarkinta zai je bauta,

shi da ma’aikatansa,”

in ji Ubangiji.

2:1 Ga abin da Ubangiji ya ce,

“Saboda zunubai uku na Mowab,

har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.

Gama ya ƙone ƙasusuwan sarkin Edom

suka zama sai ka ce toka.

2 Zan sa wuta a Mowab

da za tă ƙone kagarun Keriyot

Mowab za tă gangara cikin hayaniya mai girma

cikin kururuwar yaƙi da kuma ƙarar ƙaho.

3 Zan hallaka mai mulkinta

zan kuma kashe shugabanninta.”

4 Ga abin da Ubangiji ya ce,

“Saboda zunubai uku na Yahuda,

har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.

Gama sun ƙi bin dokar Ubangiji

ba su kuma yi biyayya da ƙa’idodinsa ba,

domin allolin ƙarya sun ruɗe su,

allolin da kakanninsu suka bauta.

5 Zan sa wuta a Yahuda

da za tă ƙone kagarun Urushalima.”

6 Ga abin da Ubangiji ya ce,

“Saboda zunubai uku na Isra’ila,

har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.

Don sun sayar da adalai waɗanda

suka kāsa biyan bashinsu.

Sun kuma sayar da matalauta

waɗanda bashinsu bai ma kai ko kuɗin bi-labi ba.

7 Sun tattake kawunan matalauta

kamar yadda suke taka laka

suka kuma danne wa marasa galihu gaskiya.

Uba da ɗa su na kwana da yarinya guda,

suna kuma ɓata sunana mai tsarki.

8 Suna kwanciya kurkusa da kowane bagade

a kan tufafin da suka karɓe jingina.

A gidajen allolinsu

sukan sha ruwan inabin da suka karɓo daga wurin waɗanda suka ci wa tara.

9 “Na hallaka mutumin Amoriyawa a gabansu,

ko da yake ya yi dogo kamar itacen al’ul

kuma mai ƙarfi kamar itacen oak.

Na hallaka ’ya’yan itatuwansa daga sama,

da kuma jijiyoyinsa daga ƙasa.

10 Na fitar da ku daga ƙasar Masar,

na kuma bishe ku tsawon shekaru arba’in a cikin hamada

don in ba ku ƙasar Amoriyawa.

11 “Na kuma tā da annabawa daga cikin ’ya’yanku maza

waɗansu kuma su zama keɓaɓɓu daga cikin samarinku.

Ba haka ba ne, mutanen Isra’ila?”

In ji Ubangiji.

12 “Amma kuka sa keɓaɓɓun suka sha ruwan inabi

kuka kuma umarci annabawa kada su yi annabci.

13 “Saboda haka, yanzu zan murƙushe ku

kamar yadda amalanke yakan murƙushe sa’ad da aka yi masa labtun hatsi.

14 Masu gudu da sauri ba za su tsira ba,

masu ƙarfi ba za su iya yin amfani da ƙarfinsu ba,

jarumi kuma ba zai iya ceton ransa ba.

15 ’Yan baka ba za su iya dāgewa ba,

masu saurin gudu ba za su tsira ba

mahayin dawakai kuma ba zai tsere da ransa ba.

16 Ko jarumawa mafi jaruntaka

za su gudu tsirara a ranan nan,”

in ji Ubangiji.

3:1 Ku ji wannan maganar da Ubangiji ya yi game da ku, ya ku jama’ar Isra’ila, a kan dukan iyalin da na fitar daga Masar.

2 “Ku ne kaɗai na zaɓa

cikin dukan al’umman duniya;

saboda haka zan hukunta ku

saboda dukan zunubanku.”

3 Mutum biyu za su iya yin tafiya tare

in ba su yarda su yi haka ba?

4 Zaki yakan yi ruri a jeji

in bai sami kama nama ba?

Zai yi gurnani a cikin kogonsa

in bai kama kome ba?

5 Tsuntsu yakan fāɗa a tarko a ƙasa

inda ba a sa tarko ba,

ko tarko yakan zargu daga ƙasa

in ba abin da ya taɓa shi?

6 Idan aka busa ƙaho a ciki birni

mutane ba sa yin rawar jiki?

Sa’ad da bala’i ya auko wa birni,

ba Ubangiji ne ya sa a kawo shi ba?

7 Ba shakka, Ubangiji Mai Iko Duka ba ya yin wani abu

ba tare da ya sanar wa bayinsa annabawa ba.

8 Zaki ya yi ruri,

wa ba zai tsorata ba?

Ubangiji Mai Iko Duka ya yi magana,

wa ba zai yi annabci ba?

9 Ku yi shela ga kagarun Ashdod

da kuma ga kagarun Masar.

“Ku tara kanku a tuddan Samariya;

ku ga rashin jituwar da take a cikinta,

da kuma zaluncin da ake yi a cikin mutanenta.”

10 “Ba su ma san yadda za su yi abin da yake daidai ba,”

in ji Ubangiji,

“sun ɓoye ganima da abubuwan da suka washe a cikin kagarunsu.”

11 Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce,

“Abokin gāba zai ƙwace ƙasar,

zai saukar da mafakarku,

zai washe kagarunku.”

12 Ga abin da Ubangiji ya ce,

“Kamar yadda makiyayi yakan ceci daga bakin zaki

ƙasusuwa ƙafafu biyu kawai ko kunne ɗaya,

haka za a ceci Isra’ilawa,

masu zama a Samariya

da kan gado kawai

da kuma a ɗan ƙyalle a kan dogayen kujerunsu.”

13 “Ku ji wannan ku kuma yi wa gidan Yaƙub gargaɗi,” in ji Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki.

14 “A ranar da zan hukunta Isra’ila saboda zunubanta,

zan hallaka bagadan Betel;

za a yayyanka ƙahonin bagadan

za su fāɗa ƙasa

15 Zan rushe gidan rani

da na damina;

gidajen da aka yi musu ado da hauren giwa za a rushe su

haka ma duk za a rurrushe manyan gidaje,”

in ji Ubangiji.

4:1 Ku kasa kunne ga wannan, ya ku shanun Bashan a kan Dutsen Samariya,

ku matan da kuke cin zalin matalauta, kuke kuma danne matalauta,

kuna kuma ce wa mazanku, “Ku kawo mana abin sha!”

2 Ubangiji Mai Iko Duka ya rantse da tsarkinsa.

“Tabbatacce lokaci yana zuwa

da za a jawo ku da ƙugiyoyi,

na ƙarshenku za a kama da ƙugiyar kifi.

3 Dukanku za ku wuce ta kai tsaye

ta inda katangar ta tsage,

za a jefar da ku a Harmon,”

in ji Ubangiji.

4 “Ku tafi Betel ku yi ta aikata zunubi;

ku je Gilgal ku ƙara yin zunubi.

Ku kawo hadayunku kowace safiya,

zakkarku kowace shekara uku.

5 Ku ƙona burodinku mai yisti kamar hadaya ta godiya,

ku yi fariya game da hadayunku na yarda rai,

ku yi taƙama game da su, ya ku Isra’ilawa,

gama abin da kuke jin daɗin aikata ke nan,”

in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

6 “Na bar ku da yunwa a kowace birni,

da kuma rashin abinci a kowane gari,

duk da haka ba ku juyo gare ni ba,”

in ji Ubangiji.

7 “Na kuma hana muku ruwan sama

tun shuke-shuken suna wata uku kafin lokacin girbi.

Na sa aka yi ruwan sama a wani gari,

sai na hana a yi a wani gari.

Wata gona ta sami ruwan sama;

wata gona kuma ta bushe.

8 Mutane suna tangaɗi daga gari zuwa gari suna neman ruwa

amma ba su sami isashen ruwan sha ba,

duk da haka ba ku juyo gare ni ba,”

in ji Ubangiji.

9 “Sau da yawa na ɓata gonakinku

da fumfuna da kuma cuta.

Fāri suka cinye itatuwanku na inabi da na ɓaure, da na zaitun

duk da haka ba ku juyo gare ni ba,”

in ji Ubangiji.

10 “Na aiko muku annoba

yadda na yi a Masar.

Na karkashe samarinku da takobi,

tare da kamammun dawakanku.

Na cika hancinku da warin sansaninku,

duk da haka ba ku juyo gare ni ba”

in ji Ubangiji.

11 “Na hallaka waɗansunku

kamar yadda na hallaka Sodom da Gomorra.

Kuna kama da itace mai cin wutar da na cire daga cikin wuta,

duk da haka ba ku juyo gare ni ba,”

in ji Ubangiji.

12 “Saboda haka ga abin da zan yi da ku, ya Isra’ila,

don kuwa zan yi muku haka,

sai ku yi shirin gamuwa da Allahnku, ya Isra’ila.”

13 Shi wanda ya yi duwatsu,

ya halicci iska,

ya kuma bayyana wa mutum tunaninsa,

shi wanda ya juya safiya ta zama duhu

yana takawa a wurare masu tsawo na duniya,

Ubangiji Allah Maɗaukaki ne sunansa.