Amos Ya Yi Annabci a Kan Al’ummai da Isra’ila (continued)

Amos ya sanar da hukunci a kan al’ummai maƙwabta, da kuma a kan Isra’ila da Yahuda.

793 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Amos 5:1–7:9

1 Ku ji wannan magana, ya gidan Isra’ila, ina makokin nan dominku.

2 “Budurwa Isra’ila ta fāɗi,

ba za tă ƙara tashi ba,

an yashe ta a ƙasarta,

ba wanda zai ɗaga ta.”

3 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce,

“Birnin da ta fitar da masu ƙarfi dubbai don Isra’ila

guda ɗari kaɗai za su dawo;

garin da ya fitar da masu ƙarfi ɗari kuwa

goma kaɗai za su dawo.”

4 Ga abin da Ubangiji ya ce wa gidan Isra’ila.

“Ku neme ni ku rayu;

5 kada ku nemi Betel,

kada ku je Gilgal,

kada ku yi tafiya zuwa Beyersheba.

Gama ba shakka Gilgal za tă tafi bauta,

za a kuwa mai da Betel ba kome ba.”

6 Ku nemi Ubangiji ku kuma rayu,

ko kuwa zai ratsa yă share gidan Yusuf kamar wuta;

zai cinye

Betel kuwa ba zai sami wanda zai kashe ta ba.

7 Ku ne masu mai da gaskiya ta koma ɗaci

ku kuma zubar da adalci.

8 (Shi wanda ya yi Taurarin nan da ake ce Kaza da ’Ya’yanta da kuma Mai Farauta da Kare,

wanda ya mai da duhu ya zama haske

ya kuma baƙanta rana ta zama dare,

yakan kwashe ruwan teku

ya zubar a ƙasa,

Ubangiji ne sunansa,

9 yakan kawo hallaka a mafaka mai ƙarfi

yakan kuma mai da birnin mai katanga ya zama kufai).

10 Ba ku son mai yin gaskiya a ɗakin shari’a

kuna ƙin mai faɗar gaskiya.

11 Kuna matsa wa matalauta

kuna sa su dole su ba ku hatsi.

Saboda haka, ko da yake kun gina gidajen duwatsu,

ba za ku zauna a cikinsu ba;

ko da yake kun nome gonaki masu kyau,

ba za ku sha ruwan inabinsu ba.

12 Gama na san yawan laifofinku

da kuma girman zunubanku.

Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci

kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa.

13 Saboda haka mai hankali yakan yi shiru a lokuta kamar haka,

gama lokutan mugaye ne.

14 Ku yi nagarta, ba mugunta ba;

don ku rayu

sa’an nan Ubangiji Allah Maɗaukaki zai kasance da ku,

kamar yadda kuka ce zai yi.

15 Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta;

ku dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunan shari’a.

Mai yiwuwa Ubangiji Allah Maɗaukaki zai ji tausayin

raguwar Yusuf.

16 Saboda haka ga abin da Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa,

“Za a yi kururuwa a dukan tituna

a kuma yi kuka don azaba a dukan wuraren da jama’a sukan taru.

Za a yi kira ga manoma su yi kuka

masu makoki kuma su yi kuka.

17 Za a yi kuka a dukan gonakin inabi,

gama zan ratsa a cikinku,”

in ji Ubangiji.

18 Kaitonku masu son

ganin ranar Ubangiji!

Don me kuke son ganin ranar Ubangiji?

Za a duhunta ranan nan, ba haske ba.

19 Za ku zama kamar mutanen da suka guje wa zaki

sai suka fāɗa a hannun beyar,

ko kuma kamar wanda ya shiga gida

ya dāfa hannu a bango

sai maciji ya sare shi.

20 Ashe, ranar Ubangiji ba duhu ba ce, a maimakon haske,

duhu wuluk, ba tare da ko ɗan haske ba.

21 “Na ƙi, ina kuma ƙyamar bukukkuwanku na addini;

ba na son ganin tarurrukanku.

22 Ko da kun kawo mini hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na hatsi,

ba zan karɓa ba.

Ko da kun kawo zaɓaɓɓun hadayu na zumunta,

ba zan ɗauke su a bakin kome ba.

23 Ku tashi daga nan da surutan waƙoƙinku!

Ba zan saurari kaɗe-kaɗe da bushe bushenku ba.

24 Amma bari gaskiya ta kwararo kamar kogi,

adalci kuma kamar rafin da ba ya taɓa bushewa!

25 “Kun kawo mini hadayu da sadakoki

shekaru arba’in a cikin jeji, ya ku gidan Isra’ila?

26 Kun ɗaga masujadar sarkinku,

siffofin gumakanku,

tauraron allahnku,

wanda kuka yi wa kanku.

27 Saboda haka zan tura ku zaman bauta gaba da Damaskus,”

in ji Ubangiji, wanda sunansa ne Allah Mai Iko.

6:1 Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona,

da ku waɗanda kuke ji zama a Dutsen Samariya lafiya ne,

ku manyan mutanen ƙasar da take sananniya,

waɗanda mutanen Isra’ila suke zuwa!

2 Ku je Kalne ku dube ta;

ku wuce daga can zuwa Hamat-rabba,

sa’an nan ku gangara zuwa Gat a Filistiya.

Sun fi masarautunku biyu ne?

Ƙasarsu ta fi taku girma?

3 Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannan muguwar rana

kuna kuma jawo mulkin tashin hankali kusa.

4 Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwa

kuna mimmiƙe a kan kujerunku.

Kuna cin naman ƙibabbun raguna

da na ƙosassun ’yan maruƙa.

5 Kuna kaɗa molayenku yadda Dawuda ya yi

kuna ƙirƙiro waƙoƙi a kan kayan kaɗe-kaɗe.

6 Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi

kuna kuma shafa mai mafi kyau,

amma ba kwa baƙin ciki game da kangon da Yusuf ya zama.

7 Saboda haka za ku zama na farkon da za su tafi zaman bauta;

bukukkuwanku da shagulgulanku za su ƙare.

8 Ubangiji Mai Iko Duka da kansa ya rantse, Ubangiji Allah Maɗaukaki ya furta,

“Ina ƙyamar girman kan Yaƙub,

ba na kuma son kagarunsa;

zan ba da birnin

da duk abin da yake cikinta.”

9 Ko da mutum goma ne suka ragu a gida guda, su ma za su mutu. 10 In kuma wani dangi ya shiga don yă fitar da gawawwakin yă ƙone ya kuwa tambayi wani wanda yake ɓoye a can, yana cewa, “Akwai wani tare da kai?” Ya kuwa ce, “Babu,” sai yă ce, “Kul! Kada mu ambaci sunan Ubangiji.”

11 Gama Ubangiji ya ba da umarni,

zai kuma ragargaza babban gidan nan kucu-kucu

ƙaramin gidan kuwa zai yi rugu-rugu da shi.

12 Dawakai sukan yi gudu a kan duwatsu?

Wani yana iya yin noma a teku da shanun noma?

Amma ga shi kun mai da gaskiya ta zama dafi

amfanin adalci kuma ya zama ɗaci,

13 ku da kuke murna saboda an ci Lo Debar da yaƙi

kuka kuma ce, “Ba da ƙarfinmu ne muka ƙwace Karnayim ba?”

14 Gama Ubangiji Allah Maɗaukaki ya ce,

“Zan sa wata ƙasa ta tayar muku, ya ku gidan Isra’ila,

wadda za tă matsa muku tun

daga Lebo Hamat zuwa kwarin Araba.”

7:1 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji yana shirya cincirindon fāri bayan da aka ƙarasa yankan rabon hatsin da yake na sarki, hatsi na biyu kuma yake tohuwa. 2 Sa’ad da suka cinye kome, sai na yi kira, na ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, ka gafarta! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”

3 Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa.

“Wannan ba zai faru ba,” in ji Ubangiji.

4 Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya nuna mini. Ubangiji Mai Iko Duka yana shirin hukunta da wuta; wutar ta ƙone teku ta kuma ƙone ƙasa. 5 Sai na yi kira, na ce, “Ubangiji Mai Iko Duka, ina roƙonka ka dakata! Ta yaya Yaƙub zai tsira? Ga shi ɗan ƙarami ne!”

6 Saboda haka sai Ubangiji ya dakatar da nufinsa.

“Wannan ma ba zai faru ba,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

7 Ga abin da ya nuna mini. Ubangiji yana tsaye kusa da bangon da aka gina, bisa ga awon igiyar gwada gini, da kuma magwaji a hannunsa. 8 Sai Ubangiji ya tambaye ni, “Me kake gani, Amos?”

Sai na amsa, “Igiyar gwada gini.”

Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Duba, zan sa igiyan nan a cikin mutanena Isra’ila; ba zan ƙara barinsu ba.

9 “Za a hallakar da wuraren sujada na Ishaku

kuma tsarkakan wurare na Isra’ila za su zama kango;

da takobina zan tayar wa gidan Yerobowam.”