Masarautar Isra’ila
Ƙarshen Mulkin Yerobowam na Biyu
809 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
25 Shi ne ya maido da iyakokin Isra’ila daga Lebo Hamat zuwa Tekun Araba, bisa ga maganar Ubangiji, Allah na Isra’ila, da ya yi ta bakin bawansa Yunana ɗan Amittai, annabi daga Gat-Hefer.
26 Ubangiji ya ga irin muguwar wahalar da ta shafi kowa a Isra’ila, ko bawa ko ’yantacce, babu mai taimakonsu. 27 Da yake kuma Ubangiji bai ce zai shafe sunan Isra’ila daga fuskar duniya ba, sai ya cece su ta hannun Yerobowam ɗan Yowash.
Hosiya Ya Yi Annabci ga Isra’ila 801 kafin haihuwar Almasihu
Roƙon farko na Hosiya ga ƙabilu goma.
1 Maganar Ubangiji da ta zo wa Hosiya ɗan Beyeri a zamanin mulkin Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, sarakunan Yahuda, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yowash sarkin Isra’ila.
2 Sa’ad da Ubangiji ya fara magana ta wurin Hosiya, Ubangiji ya ce masa, “Ka tafi, ka auro wa kanka mazinaciya da ’ya’yan da aka haifa ta hanyar rashin aminci, domin ƙasar tana da laifin mummunan zina ta wurin rabuwa da Ubangiji.” 3 Saboda haka sai ya auri Gomer ’yar Dibilayim, ta kuwa yi ciki ta haifi ɗa namiji.
4 Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba shi suna Yezireyel, domin ba da daɗewa ba zan hukunta gidan Yehu saboda kisan da aka yi a Yezireyel, zan kuma kawo ƙarshen mulkin Isra’ila. 5 A wannan rana zan karye ƙarfin Isra’ila a Kwarin Yezireyel.”
6 Gomer ta sāke ɗauki ciki ta kuma haifi ’ya mace. Sai Ubangiji ya ce wa Hosiya, “Ka ba ta suna, Lo-Ruhama, gama ba zan ƙara nuna wa gidan Isra’ila ƙauna ba, har da zan gafarta musu. 7 Duk da haka zan nuna ƙauna ga gidan Yahuda; zan kuma cece su, ba da baka, takobi ko yaƙi ba, ko ta wurin dawakai, ko masu hawan dawakai ba, sai ko ta wurin Ubangiji Allahnsu.”
8 Bayan ta yaye Lo-Ruhama, sai Gomer ta sāke haifi wani ɗa namiji. 9 Sai Ubangiji ya ce, “Ka ba shi suna Lo-Ammi, gama ku ba mutanena ba ne, ni kuma ba Allahnku ba ne.
10 “Duk da haka Isra’ilawa za su zama kamar yashi a bakin teku, da ba za a iya aunawa ko a ƙirga ba. A inda aka ce musu, ‘Ku ba mutanena ba ne,’ za a kira su ‘’ya’yan Allah mai rai.’ 11 Mutanen Yahuda da mutanen Isra’ila za su sāke haɗu su zama ɗaya, za su kuma naɗa shugaba guda su kuma fita daga ƙasar, gama ranar za tă zama mai girma wa Yezireyel.
2:1 “Ka ce da ’yan’uwanka maza, ‘Mutanena,’ ka kuma ce da ’yan’uwanka mata, ‘Ƙaunatacciyata.’
2 “Ka tsawata wa mahaifiyarka, ka tsawata mata,
gama ita ba matata ba ce,
ni kuma ba mijinta ba ne.
Ku roƙe ta tă daina karuwancinta
da kuma rashin aminci a tsakanin nononta.
3 In ba haka ba zai tuɓe ta tsirara
in bar ta kamar yadda take a ranar da aka haife ta;
zan sa ta zama kamar hamada,
in mayar da ita busasshiyar ƙasar,
in kashe ta da ƙishirwa.
4 Ba zan nuna wa ’ya’yanta ƙaunata ba,
domin su ’ya’yan zina ne.
5 Mahaifiyarsu ta yi rashin aminci
ta kuma ɗauki cikinsu ta wurin yi abin kunya.
Ta ce, ‘Zan bi kwartayena,
waɗanda suke ba ni abinci da ruwa,
ulu nawa da lilina, mai nawa da kuma abin sha na.’
6 Saboda haka zai tare hanyarta da ƙaya;
zan yi mata katanga don kada tă sami hanya.
7 Za tă bi kwartayenta amma ba za tă kama su ba;
za tă neme su amma ba za tă same su ba.
Sa’an nan za tă ce,
‘Zan koma ga mijina na fari,
gama dā ya fi mini yadda nake a yanzu.’
8 Ba ta yarda cewa ni ne
wanda ya ba ta hatsi, sabon ruwan inabi da mai ba,
wanda ya jibge mata azurfa da zinariya,
waɗanda suka yi amfani wa Ba’al ba.
9 “Saboda haka zan ƙwace hatsina sa’ad da ya nuna,
da sabon ruwan inabina sa’ad da ya ƙosa.
Zan karɓe ulu nawa da lilina,
da take niyya ta rufe tsiraicinta.
10 Saboda haka yanzu zan buɗe tsiraicinta
a idanun kwartayenta;
ba wani da zai ƙwace ta daga hannuwana.
11 Zan tsayar da dukan bukukkuwarta,
bukukkuwarta na shekara-shekara, da kuma kiyaye bikin Sababbin Wata nata,
kwanakin Asabbacinta, dukan ƙayyadaddun bukukkuwarta.
12 Zan lalatar da inabinta da kuma itatuwan ɓaurenta,
waɗanda take cewa su ne abin da kwartayenta suka biya;
zan mayar da su kurmi,
namun jeji kuwa za su ci su.
13 Zan hukunta ta saboda kwanakin
da ta ƙone turare wa Ba’al;
ta yi wa kanta ado da zobai da duwatsu masu daraja,
ta bi kwartayenta,
amma ta manta da ni,”
in ji Ubangiji.
14 “Saboda haka yanzu zan rarrashe ta;
zan bishe ta zuwa hamada
in kuma yi mata magana a hankali.
15 A can zan mayar mata da gonakin inabinta,
zan kuma sa Kwarin Akor yă zama ƙofar bege.
A can za tă rera kamar a kwanakin ƙuruciyarta,
kamar a lokacin da ta fita daga Masar.
16 “A waccan rana,” in ji Ubangiji,
“za ki ce da ni ‘mijina’;
ba za ki ƙara ce ni ‘maigidana’ ba.
17 Zan cire sunayen Ba’al daga leɓunanta;
ba za a ƙara kira sunayensu ba.
18 A waccan rana zan yi alkawari dominsu
da namun jeji da kuma tsuntsayen sararin sama
da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa.
Baka da takobi da yaƙi
zan sa su ƙare a ƙasar,
domin duk su zauna lafiya.
19 Zan ɗaura aure da ke har abada;
zan ɗaura aure da yake cikin adalci da gaskiya,
cikin ƙauna da jinƙai.
20 Zan ɗaura aure da yake cikin aminci
za ki kuwa yarda cewa ni ne Ubangiji.
21 “A waccan rana zan amsa,” in ji Ubangiji,
“zan amsa wa sararin sama,
za su kuwa amsa wa ƙasa;
22 ƙasa kuma za tă amsa wa hatsi,
sabon ruwan inabi da kuma mai,
su kuma za su amsa wa Yezireyel.
23 Zan dasa ta wa kaina a ƙasar;
zan shuka ƙaunata ga wanda na ce ‘Ba ƙaunatacciyata ba.’
Zan faɗa wa waɗanda a ce ‘Ba mutanena ba,’ ‘Ku mutanena ne’;
za su kuwa ce, ‘Kai ne Allahna.’ ”
3:1 Ubangiji ya ce mini, “Ka tafi, ka sāke nuna wa matarka ƙauna, ko da yake wani yana son ta, ita kuma mazinaciya ce. Ka ƙaunace ta yadda Ubangiji yake ƙaunar Isra’ilawa, ko da yake sun juya ga waɗansu alloli suna kuma ƙauna wainar zabibi mai tsarki.”
2 Ta haka na saye ta da shekel goma sha biyar na azurfa da kuma wajen buhu na sha’ir. 3 Sai na faɗa mata, “Za ki zauna tare da ni kwanaki masu yawa; kada ki yi karuwanci ko ki yi abuta da wani namiji, ni kuwa zan zauna tare da ke.”
4 Gama Isra’ilawa za su yi kwanaki masu yawa ba tare da sarki ko shugaba ba, babu hadaya ko keɓaɓɓun duwatsu, babu efod ko gunki. 5 Daga baya Isra’ilawa za su dawo su nemi Ubangiji Allahnsu da kuma Dawuda sarkinsu. Za su je da rawan jiki wajen Ubangiji da kuma ga albarkunsa a kwanakin ƙarshe.