Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Ayuba 26

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ayuba

1 Sai Ayuba ya amsa,

2 “Yadda ka taimaki marar ƙarfi!

Yadda ka ceci marar ƙarfi!

3 Ka ba marar hikima shawara!

Ka nuna kana da ilimi sosai.

4 Wane ne ya taimake ka ka yi waɗannan maganganu?

Kuma ruhun wane ne ya yi magana ta bakinka?

5 “Matattu suna cikin azaba, waɗanda suke ƙarƙashin ruwaye

da dukan mazauna cikin ruwaye.

6 Mutuwa tsirara take a gaban Allah;

haka kuma hallaka take a buɗe.

7 Ya shimfiɗa arewancin sararin sama a sarari;

ya rataye duniya ba a jikin wani abu ba.

8 Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa,

duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba.

9 Ya rufe fuskar wata,

ya shimfiɗa gizagizai a kan shi,

10 ya zāna iyakar fuskar ruwa

a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske.

11 Madogaran sama sun girgiza,

saboda tsawatawarsa.

12 Da ikonsa ya kwantar da teku;

da hikimarsa ya hallaka dodon ruwan nan Rahab.

13 Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau

da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu.

14 Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa.

Kaɗan kawai muke ji game da shi!

Wane ne kuwa yake iya gane tsawar ikonsa?”

Ayuba 26