Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Irmiya 47

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Saƙo game da Filistiyawa

1 Ga maganar Ubangiji da ta zo wa Irmiya annabi game da Filistiyawa kafin Fir’auna ya yaƙi Gaza.

2 Ga abin da Ubangiji yana cewa,

“Dubi yadda ruwaye suna tasowa a arewa;

za su zama kogi mai rigyawa.

Za su malala a ƙasa da kuma a kan kome da yake cikinta,

garuruwa da waɗanda suke zaune a cikinsu.

Mutane za su yi kuka;

dukan mazaunan ƙasar za su yi kururuwa

3 da jin motsin takawar kofatan dawakai,

da jin surutun kekunan yaƙin abokin gāba

da motsin ƙafafunsu.

Ubanni ba za su juye don su taimaki ’ya’yansu ba;

hannuwansu za su yi laƙwas.

4 Gama rana ta zo

da za a hallaka Filistiyawa

a kuma datse dukan waɗanda suka ragu

waɗanda za su iya taimakon Taya da Sidon.

Ubangiji yana gab da hallaka Filistiyawa,

raguwa daga bakin tekun Kaftor.

5 Gaza za tă aske kanta cikin baƙin ciki;

Ashkelon zai yi shiru.

Ya raguwar da suke zama a fili,

har yaushe za ku tsattsage kanku?

6 “Za ku yi kuka kuna cewa, ‘Wayyo, takobin Ubangiji

sai yaushe za ka huta?

Ka koma kubenka;

ka huta, ka yi shiru.’

7 Amma ta yaya zai huta

sa’ad da Ubangiji ya umarta,

sa’ad da ya umarta shi

don yă faɗa wa Ashkelon da kuma bakin teku?”

Irmiya 47