Search Help

Search the whole Bible in your chosen Translation.

1. Find Verses Using Words

Examples:

Notes:

2. Find Verses Using Advanced Matching

Finds baptism, baptize, baptized, baptizing

Finds love, loved, loving

3. Find a passage

Opens John chapter 3.

Opens John 3, verses 16–17. A book name on its own, such as "John", searches for that word.

Hosiya 14

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Tuba don kawo albarka

1 Ku dawo, ya Isra’ila, ga Ubangiji Allahnku.

Zunubanku ne sun zama sanadin fāɗuwarku!

2 Ku ɗauki magana tare da ku

ku komo wurin Ubangiji.

Ku ce masa,

“Ka gafarta mana dukan zunubanmu

ka kuma karɓe mu da alheri,

don mu iya yabe ka da leɓunanmu.a

3 Assuriya ba za su iya cece mu ba;

ba za mu hau dawakan yaƙi ba.

Ba za mu ƙara ce, ‘Allolinmu’

wa abin da hannuwanmu suka yi ba,

gama a gare ka ne maraya yakan sami jinƙai.”

4 “Zan gyara ɓatancinsu

in kuma ƙaunace su a sake,

gama fushina ya juya daga gare su.

5 Zan zama kamar raɓa ga Isra’ila

zai yi fure kamar lili.

Kamar al’ul na Lebanon

zai sa saiwarsa zuwa ƙasa;

6 tohonsa za su yi girma.

Darajarsa za tă zama kamar itacen zaitun,

ƙanshinsa kamar al’ul na Lebanon.

7 Mutane za su sāke zauna a inuwarsa.

Zai haɓaka kamar ƙwayar hatsi.

Zai yi fure kamar kuringa,

zai zama sananne kamar ruwan inabi daga Lebanon.

8 Efraim zai ce, me kuma zai haɗa ni da gumaka?

Zan amsa masa in kuma lura da shi.

Ni kamar koren itacen fir ne;

amincinka yana fitowa daga gare ni ne.”

9 Wane ne yake da hikima? Zai gane waɗannan abubuwa.

Hanyoyin Ubangiji daidai ne;

masu adalci sukan yi tafiya a kansu,

amma ’yan tawaye sukan yi tuntuɓe a kansu.

Translator’s notes

  1. 14:2 (a): Ko kuwa miƙa leɓunanmu kamar hadayun bijimai

Hosiya 14