Sashe na 14: Tashin Kiristi daga Matattu da Hawansa zuwa Sama

Tashin Kiristi daga matattu, bayyanarsa, da hawansa zuwa sama.

A cikin kwana arba'in, tun daga Lahadin da ta biyo bayan mutuwar Kiristi. Lokacin bazara na shekara ta 30 Miladiyya (ko 29). Yahudiya da Galili

Matan Sun Ziyarci Kabarin Yesu

Golgota da Betani. Asabar bayan la'asar da farkon yamma bisa lissafinmu

Suna sa ido a kan kabarin a ƙarshen Asabbaci (Asabar bayan azahar bisa lissafinmu), kuma suna sayen kayan ƙanshi bayan Asabbaci (bayan ƙarfe 6 na yammacin Asabar), a ranar farko ta mako.

30 ko 29 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Mattiyu 28:1

28:1 Bayan ranar Asabbaci, da sassafe, a ranar farko ta mako, Maryamu Magdalin tare da ɗaya Maryamun, suka je don su ga kabarin.

Markus 16:1

16:1 Da Asabbaci ya wuce, sai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub, da kuma Salome suka sayi kayan ƙanshi domin su je su shafa wa jikin Yesu.

Mala'ika Ya Mirgine Dutsen

An yi girgizar ƙasa, mala'ika ya mirgine dutsen, kuma masu tsaron Romawa sun firgita.

A Lahadi kafin fitowar rana

Mattiyu 28:2–4

28:2 Sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa. Don wani mala’ikan Ubangiji ya sauka daga sama, ya je kabarin, ya gungurar da dutsen, ya kuma zauna a kai. 3 Kamanninsa yana kama da walƙiya, tufafinsa kuma fari fat kamar dusan ƙanƙara. 4 Masu gadin kabarin kuma suka ji tsoro ƙwarai, suka yi rawan jiki, suka zama kamar matattu.

Mala'iku Sun Faɗa wa Matan Game da Kabarin da Babu Kowa a Cikinsa

Matan sun ziyarci kabarin Yesu wajen fitowar rana a safiyar Lahadi, kuma mala'iku sun ba su saƙon game da kabarin da babu kowa a cikinsa.

Golgota. Da sassafe a Lahadi

Mattiyu 28:5–8

28:5 Mala’ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na san cewa kuna neman Yesu wanda aka gicciye ne. 6 Ai, ba ya nan, ya tashi kamar yadda ya faɗa. Ku zo ku ga inda ya kwanta.

7 Sai ku tafi da sauri ku gaya wa almajiransa cewa, ‘Ya tashi daga matattu, ya kuma ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi.’ Ga shi na faɗa muku.”

8 Sai matan suka bar kabarin da hanzari, da tsoro, sai dai cike da farin ciki, suka tafi a guje don su gaya wa almajiransa.

Markus 16:2–8

16:2 A ranar farko ta mako, da sassafe, bayan fitowar rana, suna kan hanyarsu zuwa kabarin ke nan, 3 sai suka tambaye juna suka ce, “Wane ne zai gungura mana dutsen daga bakin kabarin?”

4 Amma da suka ɗaga kai, sai suka ga cewa, an riga an gungura dutsen. Dutsen kuwa babba ne.

5 Da suna shiga cikin kabarin, sai suka ga wani saurayi sanye da farar riga, yana zaune a hannun dama, sai suka firgita.

6 Ya ce, “Kada ku firgita. Kuna neman Yesu Banazare wanda aka gicciye ne. Ya tashi! Ba ya nan. Ku dubi inda aka kwantar da shi.

7 Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa da kuma Bitrus cewa, ‘Ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.’ ”

8 Da rawan jiki da kuma ruɗewa, matan suka fita a guje daga kabarin. Ba su kuwa gaya wa kowa ba, don suna tsoro.

Luka 24:1–8

24:1 Da sassafe a ranar farko ta mako, matan suka je kabarin, da kayan ƙanshin da suka shirya.

2 Suka iske an riga an gungurar da dutsen daga bakin kabarin. 3 Amma da suka shiga ciki, ba su iske jikin Ubangiji Yesu ba. 4 Yayinda suna cikin tunani a kan wannan, nan take, ga waɗansu mutum biyu tsaye kusa da su, sanye da kaya masu ƙyalli, kamar walƙiya.

5 A cikin tsoro, matan suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa, amma mutanen suka ce musu, “Me ya sa kuke neman mai rai a cikin matattu?

6 Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili cewa, 7 ‘Dole a ba da Ɗan Mutum ga hannun masu zunubi, a kuma gicciye shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.’ ” 8 Sai suka tuna da maganarsa.

Yohanna 20:1

20:1 Da sassafe a ranar farko ta mako, tun da sauran duhu, Maryamu Magdalin ta tafi kabarin ta kuwa tarar an kawar da dutsen daga bakin kabarin.

Bitrus da Yohanna Sun Ziyarci Kabarin da Babu Kowa a Cikinsa

Maryamu Magdalin da sauran matan sun ba manzanni labari, kuma Bitrus da Yohanna sun ziyarci kabarin da babu kowa a cikinsa.

Luka 24:9–12

24:9 Da suka dawo daga kabarin, sai suka faɗa wa Sha Ɗayan nan da sauransu, dukan waɗannan abubuwa. 10 Matan da suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa su ne, Maryamu Magdalin, da Yowanna, da Maryamu uwar Yaƙub, da waɗansu da suke tare da su.

11 Amma ba su gaskata matan ba, domin sun ɗauki kalmominsu wani zancen banza ne.

12 Duk da haka, Bitrus ya tashi a guje zuwa kabarin. Da ya sunkuya, sai ya ga ƙyallayen lilin kaɗai a kwance. Sai ya koma yana tunani a ransa, a kan abin da ya faru.

Yohanna 20:2–10

20:2 Sai ta zo da gudu wajen Siman Bitrus da ɗayan almajirin, wanda Yesu yake ƙauna, ta ce, “Sun ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuma san inda suka sa shi ba!”

3 Sai Bitrus da almajirin nan suka nufi kabarin.

4 Dukansu biyu suna gudu, amma ɗayan almajirin ya tsere wa Bitrus ya kuma fara kai kabarin. 5 Ya sunkuya ya duba ciki ya ga ƙyallayen lilin ne kwance a can amma bai shiga ba. 6 Sa’an nan Siman Bitrus, wanda yake bayansa, ya iso ya kuwa wuce cikin kabarin. Ya ga ƙyallayen lilin kwance a can, 7 haka ma zanen binnewar da aka naɗe kan Yesu da shi. Zanen a naɗe yake shi kaɗai, a keɓe da lilin ɗin. 8 A ƙarshe sai almajirin nan, wanda ya kai kabarin da farko, shi ma ya shiga. Ya gani ya kuma gaskata. 9 (Har yanzu ba su fahimci Nassin nan da ya ce lalle ne Yesu yă tashi daga matattu ba.) 10 Sai almajiran suka koma zuwa inda suke zama.