Yesu Ya Bayyana ga Maryamu Magdalin
Yesu ya bayyana ga Maryamu Magdalin kuma ya ba ta saƙo zuwa ga almajiran.
An ambaci bayyana sau biyar a ranar tashinsa daga matattu, da ƙarin sau biyar daga baya, a cikin kwana arba'in. Bayyana sau biyar a wannan rana su ne (1) ga Maryamu Magdalin (Yohanna da Markus); (2) ga sauran matan (Mattiyu); (3) ga mutum biyun da suke zuwa Emmawus; (4) ga Siman Bitrus (Luka 24:34); (5) ga manzanni goma da wasu.
Urushalima. Ranar farko ta mako (Lahadi)
30 ko 29 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Markus 16:9–11
16:9 Da Yesu ya tashi daga matattu da safe, a ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magdalin, wadda ya fitar da aljanu bakwai daga cikinta.
10 Ta je ta gaya wa waɗanda dā suke tare da shi, waɗanda kuma suke makoki da kuka. 11 Da suka ji cewa Yesu yana da rai, har ma ta gan shi, ba su gaskata ba.
Yohanna 20:11–18
20:11 Maryamu kuwa ta tsaya a bakin kabarin daga waje tana kuka. Da tana cikin kuka, sai ta sunkuya ta leƙa cikin kabarin, 12 sai ta ga waɗansu mala’iku biyu saye da fararen tufafi, zaune a inda dā gawar Yesu take, ɗaya wajen kai ɗayan kuma wajen ƙafafu.
13 Suka tambaye ta cewa, “Mace, don me kike kuka?”
Ta ce, “Sun ɗauke Ubangijina, ban kuma san inda suka ajiye shi ba.”
14 Da ta faɗin haka, sai ta juya ta ga Yesu tsaye, sai dai ba tă gane cewa Yesu ne ba.
15 Sai ya ce, “Mace, don me kike kuka? Wa kike nema?”
Ta yi tsammani shi ne mai aikin lambun, sai ta ce, “Ranka yă daɗe, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka ajiye shi, in je in ɗauke shi.”
16 Yesu ya ce mata, “Maryamu.”
Sai ta juya wajensa ta ɗaga murya ta ce da Arameyanci, “Rabboni!” (Wanda yake nufin “Malam”).
17 Yesu ya ce, “Kada ki riƙe ni, gama ban riga na koma wajen Uba tukuna ba. A maimako, ki tafi wajen ’yan’uwana ki gaya musu, ‘Ina komawa wajen Ubana da Ubanku, wajen Allahna da kuma Allahnku.’ ”
18 Sai Maryamu Magdalin ta wajen almajiran da labari cewa, “Na ga Ubangiji!” Ta kuma gaya musu cewa ya faɗa mata waɗannan abubuwa.
Yesu Ya Bayyana ga Sauran Matan
Urushalima. Lahadi ranar farko ta mako
Mattiyu 28:9–10
28:9 Kwaram, sai ga Yesu ya gamu da su ya ce, “Gaisuwa.” Sai suka zo kusa da shi, suka rungumi ƙafafunsa, suka yi masa sujada. 10 Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ku tafi ku gaya wa ’yan’uwana, su tafi Galili. A can za su gan ni.”
Wasu Masu Tsaro Sun Ba Shugabannin Yahudawa Labari
Mattiyu 28:11–15
28:11 Yayinda matan nan suna cikin tafiya, sai waɗansu daga cikin masu gadin suka shiga gari, suka ba wa manyan firistoci labarin duk abin da ya faru. 12 Da manyan firistoci da dattawa suka taru, sai suka ƙulla wata dabara, suka ba wa sojojin kuɗi mai yawa. 13 Suka ce musu, “Ku, za ku ce, ‘Almajiransa ne sun zo da dare suka sace shi, lokacin da muke barci.’ 14 In wannan labari ya kai kunnen gwamna, za mu lallashe shi, mu kuma kāre ku daga duk wata wahala.” 15 Sai sojojin suka karɓi kuɗin, suka kuma yi kamar yadda aka umarce su. Wannan labarin kuwa shi ne ake bazawa ko’ina a cikin Yahudawa, har yă zuwa yau.
Yesu Ya Bayyana ga Almajirai Biyu a Hanyar Zuwa Emmawus
Yesu ya bayyana ga almajirai biyu (Kiliyobas da wani) a hanyar zuwa Emmawus.
Lahadi bayan azahar
Markus 16:12–13
16:12 Daga baya Yesu ya bayyana a wani kamanni dabam ga biyunsu, yayinda suke tafiya ƙauye. 13 Waɗannan kuwa suka koma suka shaida wa sauran, amma su ma ba su gaskata ba.
Luka 24:13–32
24:13 A wannan rana kuma, biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani ƙauye, da ake kira Emmawus, da suke kusan mil bakwai daga Urushalima. 14 Suna magana da juna a kan dukan abubuwan da suka faru. 15 Da suna magana, kuma suna tattauna waɗannan abubuwa da junansu, sai Yesu da kansa ya zo yana tafiya tare da su. 16 Amma ba a ba su ikon gane shi ba.
17 Sai ya tambaye, su ya ce, “Mene ne kuke tattaunawa da juna a cikin tafiyarku?”
Suka tsaya shiru, da damuwa a fuskarsu. 18 Ɗaya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai baƙo ne a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, a cikin kwanakin nan ba?”
19 Sai ya yi tambaya, “Waɗanne abubuwa?”
Suka amsa suka ce, “Game da Yesu Banazare. Shi annabi ne, mai iko ne kuma cikin ayyukansa da maganarsa, a gaban Allah da kuma dukan mutane. 20 Manyan firistoci da masu mulkinmu sun ba da shi a yi masa hukuncin mutuwa, suka kuwa gicciye shi. 21 Amma da, muna sa zuciya cewa, shi ne wanda zai fanshi Isra’ila. Bugu da ƙari kuma yau kwana uku ke nan tun da wannan abin ya faru. 22 Har wa yau, waɗansu daga cikin matanmu sun ba mu mamaki. Sun je kabarin da sassafen nan, 23 amma ba su sami jikinsa ba. Sun dawo sun faɗa mana cewa, sun ga wahayi na mala’iku, da suka ce yana da rai. 24 Sa’an nan, waɗansu abokanmu suka je kabarin, suka kuma tarar da kome kamar yadda matan suka faɗa, amma shi, ba su gan shi ba.”
25 Sai ya ce musu, “Ashe, ku marasa azanci ne, masu nauyin zuciyar gaskata, da dukan abin da annabawa suka faɗa! 26 Ai, dole Kiristi yă sha waɗannan wahalolin, kafin yă shiga ɗaukakarsa. 27 Sai ya fara bayyana musu daga Musa da dukan Annabawa, abin da dukan Nassi ya faɗa a kansa.”
28 Da suka yi kusa da ƙauyen da za su, sai Yesu ya yi kamar zai ci gaba. 29 Amma suka matsa masa suka ce, “Sauka wurinmu, don dare ya kusa, rana ta kusa fāɗuwa.” Sai ya sauka wurinsu.
30 Da ya zauna a tebur tare da su, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya ya fara ba su. 31 Sa’an nan idanunsu suka buɗe, suka gane shi. Sai ya ɓace musu. 32 Suka tambayi juna, “Ashe, shi ya sa zukatanmu suka kuna a cikinmu, sa’ad da yake magana da mu a hanya, yana bayyana mana Nassi.”