Sashe na 5: Yohanna Mai Baftisma Ya Fara Hidimarsa

Wataƙila watanni shida, a shekara ta 25 bayan haihuwar Kiristi. A jejin Yahudiya da gefen Urdun

Lokacin Farawa

25 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Markus 1:1

1:1 Farkon bishara game da Yesu Kiristi, Ɗan Allah.

Luka 3:1–2

3:1 A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tiberiyus, a lokacin Buntus Bilatus ne gwamnar Yahudiya, Hiridus kuma yana sarautar Galili, ɗan’uwansa Filibus yana sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiline.  2 A lokacin ne Annas da Kayifas suke manyan firistoci. Sai maganar Allah ta zo wa Yohanna, ɗan Zakariya a hamada.

Saƙon da Manzon

Mattiyu 3:1–6

3:1 A waɗancan kwanaki, Yohanna Mai Baftisma ya zo, yana wa’azi a Hamadan Yahudiya

2 yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”

3 Wannan shi ne wanda aka yi maganarsa ta wurin annabi Ishaya cewa,

“Ga murya mai kira a hamada tana cewa,

‘Ku shirya wa Ubangiji hanya,

ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”

4 Tufafin Yohanna kuwa an yi su da gashin raƙumi ne, yana kuma daure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fāri ne da zumar jeji. 5 Mutane suka zo wurinsa daga Urushalima da dukan Yahudiya da kuma dukan yankin Urdun.

6 Suna furta zunubansu, ya kuma yi musu baftisma a Kogin Urdun.

Markus 1:2–6

1:2 An rubuta a cikin littafin annabi Ishaya cewa,

“Zan aika da ɗan aikena yă sha gabanka,

wanda zai shirya hanyarka,”

3 “muryar mai kira a hamada tana cewa,

‘Ku shirya wa Ubangiji hanya,

ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”

4 Ta haka Yohanna ya zo, yana baftisma a yankin hamada, yana kuma wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai. 5 Dukan ƙauyukan Yahudiya da dukan mutanen Urushalima suka fiffito zuwa wurinsa. Suna furta zunubansu, ya kuwa yi musu baftisma a Kogin Urdun.

6 Yohanna ya sa tufafin gashin raƙumi, ya kuma yi ɗamara da fata. Abincinsa fāri ne da kuma zumar jeji.

Luka 3:3–6

3:3 Ya zaga dukan ƙasar da take kewaye da Urdun, yana wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai.

4 Kamar yadda yake a rubuce a littafin annabi Ishaya.

“Muryar mai kira a hamada,

‘Ku shirya wa Ubangiji hanya,

ku miƙe hanyoyi dominsa.

5 Za a cike kowane kwari,

a farfashe kowane dutse da kowane tudu.

Za a miƙe hanyoyin da suka karkace,

a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul.

6 Dukan ’yan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’ ”

Misalin Wa'azin Yohanna Mai Baftisma

Mattiyu 3:7–10

3:7 Amma da Yohanna ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa inda yake yin baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?

8 Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. 9 Kada ma ku yi tunani a ranku cewa, ‘Ai, Ibrahim ne mahaifinmu.’ Ina gaya muku cewa Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim daga cikin duwatsun nan.

10 An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.

Luka 3:7–14

3:7 Yohanna ya ce wa taron da suke zuwa domin yă yi musu baftisma, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku, ku guje wa fushin nan mai zuwa?

8 Ku yi ayyukan da suka dace da tuba. Kada ma ku yi tunani za ku iya ce wa kanku, ‘Ai, muna da mahaifinmu Ibrahim.’ Ina gaya muku cewa daga cikin duwatsun nan Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim.

9 An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.”

10 Sai taron suka tambaye shi, suka ce “Me za mu yi ke nan?”

11 Ya amsa ya ce, “Ya kamata, mutumin da yake da riguna biyu, yă raba da wanda ba shi da riga, mai abinci kuma yă yi haka.”

12 Masu karɓar haraji ma suka zo, domin a yi musu baftisma. Suka yi tambaya, suka ce “Malam, me ya kamata mu yi?”

13 Ya ce musu, “Kada ku karɓa fiye da abin da aka ce a karɓa.”

14 Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?”

Sai ya amsa ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.”

Yohanna Ya Bayyana Almasihu Kafin Ya Gan Shi

Magabacin nan, Yohanna Mai Baftisma, ya bayyana Almasihu kafin ya gan shi.

Mattiyu 3:11–12

3:11 “Ina muku baftisma da ruwa domin tuba. Amma wani yana zuwa a bayana wanda ya fi ni iko, wanda ko takalmansa ma ban isa in ɗauka ba. Zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta.

12 Yana riƙe da matankaɗinsa, zai tankaɗe hatsinsa, yă kuma tattara alkamarsa a cikin rumbu, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”

Markus 1:7–8

1:7 Wannan kuwa shi ne saƙonsa, “A bayana, wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban kuwa isa in sunkuya in kunce igiyar takalmansa ba.

8 Ina muku baftisma da ruwa, amma shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”

Luka 3:15–18

3:15 Mutane suka zuba ido, suna kuma tunani a zuciyarsu, ko Yohanna ne Kiristi wanda ake sauraron zuwansa.

16 Yohanna ya amsa musu duka ya ce, “Ina muku baftisma da ruwa. Amma wani wanda ya fi ni iko yana zuwa, ban ma isa in kunce igiyar takalmansa ba. Shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da wuta kuma. 17 Matankaɗinsa yana a hannunsa don yă tankaɗe sussukarsa ya kuma tattara alkama cikin rumbunsa, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.” 18 Da kalmomi masu yawa Yohanna ya yi wa mutane gargaɗi, ya kuma yi musu wa’azin bishara.