An Kai Yesu Masar kuma An Kashe Yaran Betlehem
An kai yaron nan Yesu Masar, kuma an kashe yaran da suke Betlehem.
Wataƙila shekara ta 5 kafin haihuwar Kiristi
5 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Mattiyu 2:13–18
2:13 Bayan sun tafi, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku gudu zuwa Masar. Ku zauna a can sai na gaya muku, gama Hiridus zai nemi yaron don yă kashe.”
14 Sai Yusuf ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa da dad dare suka tafi Masar, 15 inda ya zauna har sai da Hiridus ya mutu. Ta haka kuwa aka cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kira ɗana.”
16 Da Hiridus ya gane cewa Masanan nan sun yi masa wayo, sai ya husata ƙwarai, ya yi umarni cewa a karkashe dukan ’yan yara maza da suke a Betlehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da ya sami labarin daga Masanan nan. 17 Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika, cewa,
18 “An ji murya a Rama,
tana kuka da makoki mai tsanani,
Rahila ce take kuka domin ’ya’yanta,
an kāsa ta’azantar da ita,
don ba su.”
An Kawo Yesu daga Masar zuwa Nazaret 4 kafin haihuwar Almasihu
Wataƙila shekara ta 4 kafin haihuwar Kiristi
Mattiyu 2:19–23
2:19 Bayan Hiridus ya mutu, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki a Masar,
20 ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa ku tafi ƙasar Isra’ila, domin waɗanda suke neman ran yaron sun mutu.”
21 Sai ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa suka tafi ƙasar Isra’ila. 22 Amma da ya ji Arkelawus ne yake mulki a Yahudiya a matsayin wanda ya gāji mahaifinsa Hiridus, sai ya ji tsoron zuwa can. Bayan an gargaɗe shi a mafarki, sai ya ratse zuwa gundumar Galili, 23 ya je ya zauna a wani garin da ake kira Nazaret. Ta haka aka cika abin da aka faɗa ta bakin annabawa cewa, “Za a ce da shi Banazare.”
Luka 2:39
2:39 Bayan da Yusuf da Maryamu suka gama yin dukan abubuwan da Dokar Ubangiji ta bukaci, sai suka koma Galili suka tafi Nazaret garinsu.
Yarintakar Yesu a Nazaret 4 kafin haihuwar Almasihu zuwa 7 bayan haihuwar Almasihu
Wataƙila daga shekara ta 4 kafin haihuwar Kiristi zuwa ta 7 bayan haihuwar Kiristi
Luka 2:40
2:40 Yaron kuwa ya yi girma ya yi ƙarfi; ya cika da hikima, alherin Allah kuwa yana bisansa.
Yaro Yesu Ya Ziyarci Urushalima Yana da Shekara Goma Sha Biyu 7 ko 8 bayan haihuwar Almasihu
Wataƙila shekara ta 7 ko ta 8 bayan haihuwar Kiristi
Luka 2:41–50
2:41 Kowace shekara, iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa. 42 Da Yesu ya cika shekaru goma sha biyu, sai suka tafi Bikin bisa ga al’ada. 43 Bayan Bikin, da iyayen suka kama hanya don su koma gida, sai Yesu, yaron nan, ya tsaya a Urushalima, ba da saninsu ba. 44 Su kuwa sun ɗauka yana tare da su, saboda haka, suka yi ta tafiya har na yini guda. Sa’an nan suka fara nemansa cikin ’yan’uwansu da abokansu. 45 Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima nemansa. 46 Bayan kwana uku, sai suka same shi a filin haikali zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu yana kuma yi musu tambayoyi. 47 Dukan waɗanda suka ji shi, suka yi mamakin fahimtarsa, da amsoshinsa. 48 Da iyayensa suka gan shi sai suka yi mamaki. Mahaifiyarsa ta ce masa, “Ɗana, don me ka yi mana haka? Ni da mahaifinka duk mun damu muna nemanka.”
49 Sai ya ce, “Don me kuke nemana? Ba ku san cewa, dole in kasance a gidan Ubana ba?” 50 Amma ba su fahimci abin da yake faɗin musu ba.
Shekaru Goma Sha Takwas a Nazaret 6 zuwa 26 bayan haihuwar Almasihu
Wataƙila daga shekara ta 7 zuwa ta 26 bayan haihuwar Kiristi (ko daga ta 6 zuwa ta 25)
Luka 2:51–52
2:51 Sai ya koma Nazaret tare da su, yana yi musu biyayya. Mahaifiyarsa kuma ta riƙe dukan waɗannan abubuwa a zuciyarta. 52 Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane.