Tafiya ta talatin da biyu: Daga Eziyon Geber zuwa Kadesh
Tafiya ta talatin da biyu: daga Eziyon Geber zuwa Hamadar Zin, ko Kadesh Barneya, a karo na biyu, bayan shekaru talatin da takwas na yawo.
1489 zuwa 1452 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
36 Suka tashi daga Eziyon Geber, suka yi sansani a Kadesh, cikin Hamadan Zin.
Miriyam ta mutu, jama’a kuma suka yi gunaguni don ruwa 1452 kafin haihuwar Almasihu
1 A watan fari, dukan jama’ar Isra’ilawa suka iso Hamadan Zin. Suka sauka a Kadesh. A nan ne Miriyam ta mutu, aka kuma bizne ta.
2 Sai aka rasa ruwa da jama’a za su sha, mutane suka taru, suka tayar wa Musa da Haruna. 3 Suka yi gunaguni wa Musa suka ce, “Da ma mun mutu sa’ad da ’yan’uwanmu suka mutu a gaban Ubangiji! 4 Don me ka kawo jama’ar Ubangiji a wannan hamada, don mu da dabbobinmu mu mutu a nan ke nan? 5 Don me ka fitar da mu daga Masar zuwa wannan banzan wuri, inda babu hatsi ko ɓaure, inabi ko rumman. Kuma babu ruwan da za a sha?”
6 Sai Musa da Haruna suka tashi daga taron, suka tafi ƙofar Tentin Sujada, suka fāɗi rubda ciki, sai ɗaukakar Ubangiji ta bayyana musu. 7 Ubangiji ya ce wa Musa, 8 “Ka ɗauki sandanka, kai da Haruna, ɗan’uwanka, ku tara jama’a, ku yi magana da dutsen a gabansu ya ba da ruwan da yake cikinsa. Za ka sa ruwa ya ɓuɓɓugo musu daga dutsen. Ta haka za ka ba taron jama’a da garkunansu ruwan sha.”
9 Sai Musa ya je ya ɗauki sandan kamar yadda Ubangiji ya umarce shi. 10 Shi da Haruna, suka tara jama’a a gaban dutsen, Musa ya ce musu, “Ku saurara, ku ’yan tawaye, dole mu kawo muku ruwa daga wannan dutse?” 11 Sai Musa ya ɗaga hannu, ya bugi dutsen sau biyu da sandansa. Ruwa kuwa ya yi ta kwararowa, jama’a da dabbobinsu suka sha.
12 Amma Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna. “Tun da yake ba ku gaskata ni ba, ba ku kuwa ɗaukaka ni a idon Isra’ilawa ba, to, ba za ku kai taron jama’an nan a ƙasar da na ba su ba.”
13 Waɗannan su ne ruwan Meriba, inda Isra’ilawa suka yi wa Ubangiji gunaguni, inda kuma ya nuna kansa mai tsarki a cikinsu.
Edom ya ƙi barin jama’a su wuce
Edom ya ƙi barin jama’a su ratsa ƙasarsa.
14 Musa ya aiki manzanni daga Kadesh zuwa wurin sarkin Edom cewa,
“Ga abin da ɗan’uwanka Isra’ila ya ce ka san duk irin wahalolin da ya same mu. 15 Kakanninmu sun gangaro zuwa Masar, muka zauna can shekaru da yawa. Masarawa suka wulaƙanta mu, da kuma kakanninmu, 16 amma da muka yi kuka a gaban Ubangiji, ya kuwa ji mu, sai ya aiko mala’ika, ya fitar da mu daga Masar.
“Yanzu ga mu a Kadesh, garin da yake kan iyakar yankinka. 17 Muna roƙonka, ka yarda mana mu bi ta ƙasarka. Ba za mu bi ta wani fili, ko gonar inabi ba, ko mu sha ruwa daga wata rijiya ba. Za mu bi ta babban hanyar sarki, ba kuwa za mu kauce dama, ko hagu ba, har mu wuce yankinka.”
18 Amma Edom ya amsa ya ce,
“Ba za ku bi ta nan ba; in kuka kuskura, za mu fito, mu yaƙe ku da takobi.”
19 Sai Isra’ilawa suka amsa, suka ce,
“Za mu bi ta babbar hanya, in mu, ko dabbobinmu suka sha ruwanku, za mu biya. Mu dai muna so mu wuce ne kawai.”
20 Sai mutanen Edom suka sāke amsa suka ce,
“Ba za ku bi nan ba dai.”
Sai Edom ya fito da runduna mai ƙarfi da yawa gaske a kan Isra’ila. 21 Da yake Edom suka ƙi su bar su su ratsa yankinsu, sai Isra’ila suka juya suka janye daga gare su.
Shan kashin Arad Bakan’ane
40 Sarki Arad Bakan’ane, wanda yake zaune a Negeb na Kan’ana, ya ji labari cewa Isra’ilawa suna zuwa.
1 Sa’ad da sarkin Arad, mutumin Kan’ana, wanda yake zaune a Negeb, da ya ji cewa Isra’ila yana zuwa ta hanyar Atarim, sai ya fito, yă yaƙi Isra’ilawa, yă kuma kama waɗansunsu. 2 Sai Isra’ila suka yi alkawari wa Ubangiji suka ce, “In ka ba da waɗannan mutane a hannunmu, za mu hallaka dukan garuruwansu ƙaf.” 3 Ubangiji kuwa ya saurari kukan Isra’ila, ya kuma ba da Kan’aniyawa a gare su. Suka hallaka su da biranensu ƙaf; saboda haka aka sa wa wurin suna Horma.
Tafiya ta talatin da uku: Daga Kadesh Barneya zuwa Dutsen Hor
37 Suka tashi daga Kadesh, suka yi sansani a Dutsen Hor, a iyakar Edom.
Mutuwar Haruna
22 Dukan Jama’ar Isra’ilawa suka tashi daga Kadesh, suka zo Dutsen Hor. 23 A Dutsen Hor, kusa da iyakar Edom, Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna, 24 “Haruna zai rasu. Ba zai shiga ƙasar da na ba Isra’ilawa ba, domin ku biyu, kun ƙi ku bi umarnina a ruwan Meriba. 25 Ka kawo Haruna da ɗansa Eleyazar, ka kai su a bisan Dutsen Hor. 26 Ka tuɓe taguwar Haruna ka sa wa ɗansa Eleyazar, gama Haruna zai rasu a can.”
27 Musa ya yi yadda Ubangiji ya umarta. Suka hau Dutsen Hor a idon dukan jama’a. 28 Musa ya tuɓe taguwar Haruna, ya kuma sa wa Eleyazar ɗan Haruna. Nan kuwa Haruna ya mutu a bisa dutsen. Sa’an nan Musa da Eleyazar suka sauka daga dutsen,
38 Bisa ga umarni Ubangiji, Haruna firist, ya hau Dutsen Hor, inda ya mutu a rana ta fari ga watan biyar, a shekara ta arba’in, bayan Isra’ilawa suka fito daga Masar. 39 Haruna yana da shekara ɗari da ashirin da uku, sa’ad da ya mutu a Dutsen Hor.
29 sa’ad da dukan jama’a kuwa suka ji cewa Haruna ya mutu, sai dukan gidan Isra’ila suka yi makoki dominsa har kwana talatin.
Tafiya ta talatin da huɗu: Daga Dutsen Hor zuwa Zalmona
41 Suka tashi daga Dutsen Hor, suka yi sansani a Zalmona.