An aika da macizai masu dafi mai ƙuna

1452 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ƙidaya 21:4–9

4 Suka kama hanya daga Dutsen Hor ta hanya zuwa Jan Teku, don su kauce wa Edom. Amma mutane suka rasa haƙuri a hanya; 5 suka yi wa Allah da Musa gunaguni, suka ce, “Me ya sa kuka fitar da mu daga Masar, kuka kawo mu mu mutu a wannan hamada? Babu abinci! Babu ruwa! Mu dai mun gaji da wannan abinci marar amfani!”

6 Sai Ubangiji ya aiko da macizai masu dafin a cikinsu, suka sassari mutane, Isra’ilawa masu yawa kuwa suka mutu. 7 Mutanen suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi, da muka yi wa Ubangiji da kai gunaguni. Ka yi addu’a don Ubangiji yă ɗauke mana macizan nan.” Saboda haka Musa ya yi addu’a domin mutane.

8 Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ƙera siffar maciji ka rataye shi a bisa doguwar sanda; kowa da maciji ya sare shi, idan ya dubi macijin nan da ka rataye, zai rayu.” 9 Saboda haka Musa ya ƙera macijin tagulla, ya kuma rataye shi bisa doguwar sanda. Sa’an nan duk wanda maciji ya sare shi, ya kuma dubi macijin tagullar, zai warke.

Tafiya ta talatin da biyar: Daga Zalmona zuwa Funon

Ƙidaya 33:42

42 Suka tashi daga Zalmona, suka yi sansani a Funon.

Tafiya ta talatin da shida: Daga Funon zuwa Obot

Ƙidaya 33:43

43 Suka tashi daga Funon, suka yi sansani a Obot.

Ƙidaya 21:10

10 Isra’ilawa suka kama hanya, suka yi sansani a Obot.

Tafiya ta talatin da bakwai: Daga Obot zuwa Iye Abarim

Ƙidaya 33:44

44 Suka tashi daga Obot, suka yi sansani a Iye Abarim, a iyakar Mowab.

Ƙidaya 21:11

11 Sai suka tashi daga Obot, suka yi sansani a Iye Abarim a hamadar da take fuskantar Mowab, wajen fitowar rana.

Tafiya ta talatin da takwas: Daga Iye Abarim zuwa Dibon Gad 1451 kafin haihuwar Almasihu

Tafiya ta talatin da takwas: daga Iye Abarim, ko Iyim, zuwa Dibon Gad.

Ƙidaya 33:45

45 Suka tashi daga Iyim, suka yi sansani a Dibon Gad.

Ƙidaya 21:12–18

12 Daga nan kuma suka ci gaba, suka yi sansani a Kwarin Zered. 13 Suka tashi daga nan, suka sauka kusa da Arnon wanda yake a hamadar da ta miƙe zuwa iyakar Amoriyawa. Arnon shi ne iyakar Mowab, wanda yake tsakanin Mowab da Amoriyawa. 14 Shi ya sa Littafin Yaƙoƙin Ubangiji ya ce,

“Waheb ta cikin yankin Sufa, da kwaruruka

na tuddan Arnon, 15 da gangaren kwaruruka,

wanda ya nausa zuwa garin Ar,

ya kuma dangana da kan iyakar Mowab.”

16 Daga can, suka gangara zuwa Beyer, wato, rijiyar da Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka tattara mutane duka, zan kuwa ba su ruwa.”

17 Sai Isra’ilawa suka rera wannan waƙa,

“Ki ɓuɓɓugo da ruwa, Ke rijiya!

Rera waƙa game da ita,

18 game da rijiyar da ’ya’yan sarki suka haƙa,

rijiyar da manyan mutane masu sandunan sarauta suka nuna da sandunansu.”

Sa’an nan suka tashi daga hamadar, suka tafi Mattana,

Shan kashin Sihon, Sarkin Amoriyawa

Ƙidaya 21:21–32

21 Isra’ila suka aiki manzanni wurin Sihon sarkin Amoriyawa su ce,

22 “Ka bari mu ratsa ta ƙasarka. Ba za mu shiga wata gona ba, ba za mu kuma shiga gonar inabi, ko mu sha ruwa daga wata rijiya ba. Za mu bi ta babbar hanyar sarki, har mu fita ƙasarka.”

23 Amma Sihon bai bar Isra’ila su ratsa ta yankinsa ba. Sai ya tara dukan sojojinsa, suka fita zuwa cikin hamada, su yaƙi Isra’ila. Da ya kai Yahaz, sai ya yaƙi Isra’ila. 24 Isra’ila fa suka kashe shi da takobi, suka ƙwace ƙasarsa, tun daga kogin Arnon har zuwa kogin Yabbok, zuwa kan iyakar Ammonawa kawai, gama sun yi wa iyakansu katanga. 25 Isra’ila suka ci dukan biranen Amoriyawa, suka kuma zauna a cikinsu, haɗe da babban birnin Heshbon da dukan ƙauyukanta. 26 Sihon sarkin Amoriyawa ya yi mulkin Heshbon, bayan ya ci sarkin Mowab na dā da yaƙi, ya kuma ƙwace dukan ƙasarsa har zuwa arewancin kogin Arnon.

27 Shi ya sa Amoriyawa suka rubuta wannan waƙa game da Heshbon suka ce,

“Ku zo mu sāke gina Heshbon,

birnin Sihon.

28 “Mayaƙansa sun fito kamar

harshen wuta

suka ƙone birnin Ar na Mowab

suna hallaka ’yan ƙasar

tuddan Arnon.

29 Kaitonki, Mowab!

Gunkinki Kemosh

ya yashe mutanenki;

aka kuma kama su, aka kai su bauta

wajen Sihon sarkin Amoriyawa.

30 “Amma mun tumɓuke su,

mun hallaka garuruwan Heshbon har zuwa Dibon.

Mun ragargaza su har zuwa Nofa

wanda ya miƙe zuwa Medeba.”

31 Ta haka Isra’ila suka zauna a ƙasar Amoriyawa.

32 Sai Musa ya aika ’yan leƙen asiri zuwa Yazer. Daga baya, sai Isra’ilawa suka ci ƙauyukan da suke kewaye, suka kuma kori Amoriyawa da suke zaune a can.

Shan kashin Og, Sarkin Bashan

Ƙidaya 21:33–35

33 Sai suka juya suka haura kan hanya ta zuwa Bashan, inda Og yake sarauta, ya kuwa fito tare da dukan sojojinsa suka yi yaƙi da Isra’ila a Edireyi.

34 Ubangiji ya ce wa Musa, “Kada ka ji tsoronsa, gama na ba da shi a gare ka, da dukan sojojinsa da kuma ƙasarsa. Ka yi da shi yadda ka yi da Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon.”

35 Ta haka suka kashe shi, tare da ’ya’yansa maza da kuma dukan sojojinsa, ba wanda ya ragu. Suka kuma mamaye ƙasarsa.

Tafiya ta talatin da tara: Daga Dibon Gad zuwa Almon Dibilatayim

Ƙidaya 33:46

46 Suka tashi daga Dibon Gad, suka yi sansani a Almon Dibilatayim.

Tafiya ta arba’in: Zuwa tsaunukan Abarim

Tafiya ta arba’in: daga Almon Dibilatayim zuwa tsaunukan Abarim.

Ƙidaya 33:47

47 Suka tashi daga Almon Dibilatayim, suka yi sansani a duwatsun Abarim, kusa da Nebo.

Ƙidaya 21:19–20

19 daga Mattana, suka tafi Nahaliyel, daga Nahaliyel, suka tafi Bamot, 20 daga Bamot kuma suka tafi kwarin da yake cikin Mowab inda ƙwanƙolin Fisga yake fuskantar hamada.

Tafiya ta arba’in da ɗaya: Daga Abarim zuwa filayen Mowab

Tafiya ta arba’in da ɗaya: daga Abarim zuwa filayen Mowab kusa da Urdun.

Ƙidaya 33:48

48 Suka tashi daga duwatsun Abarim, suka yi sansani a filayen Mowab kusa da Urdun, ɗaura da Yeriko.