Nadamar Yahuda Maci Amana da Kashe Kansa

A haikali da kuma wani wuri a bayan ganuwar Urushalima. Juma'a da safe

30 ko 29 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Mattiyu 27:3–10

27:3 Sa’ad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin. 4 Ya ce, “Na yi zunubi da na ci amanar marar laifi.”

Suka ce masa, “Ina ruwanmu da wannan? Wannan dai ruwanka ne.”

5 Sai Yahuda ya zubar da kuɗin a cikin haikalin ya tafi. Sa’an nan ya je ya rataye kansa.

6 Manyan firistoci suka ɗauki kuɗin, suka ce, “Doka ta hana a sa kuɗin a cikin ma’aji, da yake kuɗin jini ne.” 7 Saboda haka, sai suka yanke shawara su yi amfani da kuɗin suka sayi filin mai yin tukwane, saboda binne baƙi. 8 Shi ya sa ake kiran filin, Filin Jini har yă zuwa yau. 9 Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika cewa, “Suka ɗauki azurfa talatin, kuɗin da mutanen Isra’ila suka sa a kansa, 10 suka kuma yi amfani da su, suka sayi filin mai yin tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”

Yesu a Gaban Bilatus a Karon Farko

Urushalima. Juma'a, da sassafe

Mattiyu 27:2, 11–14

27:2 Suka daure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga gwamna Bilatus.

11 Ana cikin haka, Yesu kuwa yana tsaye a gaban gwamna, sai gwamnan ya tambaye shi, “Kai ne Sarkin Yahudawa?”

Yesu ya ce, “I, haka ne, kamar yadda ka faɗa.”

12 Da manyan firistoci da dattawa suka zarge shi, bai ba da amsa ba.

13 Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Ba ka jin shaidar da suke kawowa a kanka?”

14 Amma Yesu bai ce uffam game da ko ɗaya daga cikin zargin da suka yi masa ba. Har gwamna ya yi mamaki ƙwarai.

Markus 15:2–5

15:2 Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?”

Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”

3 Manyan firistoci suka zarge shi a kan abubuwa da yawa.

4 Don haka Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba za ka amsa ba? Dubi abubuwa da yawa da suke zarginka da su.”

5 Amma har yanzu, Yesu bai ba da amsa ba, Bilatus ya yi mamaki.

Luka 23:1–5

23:1 Sai dukan majalisa suka tashi, suka kai shi gaban Bilatus. 2 Suka fara zarginsa suna cewa, “Mun sami wannan mutum yana rikitar da al’ummarmu. Yana hana a biya haraji ga Kaisar. Yana kuma cewa, shi Kiristi ne, sarki kuma.”

3 Sai Bilatus ya tambayi Yesu ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?”

Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”

4 Sai Bilatus ya sanar wa manyan firistoci da taron ya ce, “Ni fa, ban sami wani ainihin abin zargi game wannan mutum nan ba.”

5 Amma suka nace, suna cewa, “Yana tā da hankulan mutane, ko’ina a Yahudiya da koyarwarsa. Ya fara daga Galili, ga shi har ya kai nan.”

Yohanna 18:28–38

18:28 Sa’an nan Yahudawa suka fitar da Yesu daga wurin Kayifas zuwa fadar gwamnar Roma. A yanzu dai, safiya ta yi, don gudu kada su ƙazantar da kansu Yahudawa ba su shiga cikin fadar ba; sun so su iya ci Bikin Ƙetarewa. 29 Saboda haka Bilatus ya fito wajensu ya ce, “Wace ƙara kuke kawowa game da mutumin nan?”

30 Suka amsa suka ce, “Da a ce shi ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bashe shi gare ka ba.”

31 Bilatus ya ce, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga dokarku.”

Sai Yahudawa suka ƙi suka ce, “Ba mu da ikon yanke wa wani hukuncin kisa.” 32 Wannan kuwa ya faru ne don a cika kalmomin da Yesu ya yi da suka nuna irin mutuwar da zai yi.

33 Sai Bilatus ya koma cikin fada, ya kira Yesu ya tambaye shi, “Shin, kai ne sarkin Yahudawa?”

34 Yesu ya yi tambaya ya ce, “Wannan ra’ayin kanka ne, ko waɗansu ne suka yi maka magana game da ni?”

35 Bilatus ya amsa ya ce, “Ni mutumin Yahuda ne? Ai, mutanenka ne da kuma manyan firistoci suka bashe ka gare ni. Me ka yi?”

36 Yesu ya ce, “Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da na duniyan nan ne da bayina sun yi yaƙi su hana Yahudawa kama ni. Amma fa mulkina daga wani waje ne.”

37 Sai Bilatus ya ce, “To, wato, kai sarki ne!”

Yesu ya amsa ya ce, “Haka yake, ni sarki ne yadda ka faɗa. Tabbatacce, saboda wannan dalili ne aka haife ni, kuma don wannan ne na zo duniya, domin in shaidi gaskiya. Duk wanda yake gefen gaskiya yakan saurare ni.”

38 Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Mece ce gaskiya?”

Da ya faɗi haka, sai ya sāke fitowa wurin Yahudawa ya ce, “Ni fa ban sami wani abin zargi game da shi ba.

Yesu a Gaban Hiridus Antifas Mai Mulkin Lardi

Urushalima. Juma'a, da sassafe

Luka 23:6–12

23:6 Da Bilatus ya ji haka, sai ya yi tambaya, “Ko shi mutumin Galili ne?” 7 Da ya ji cewa, Yesu yana ƙarƙashin mulkin Hiridus ne, sai ya aika da shi zuwa wurin Hiridus, don a lokacin Hiridus yana Urushalima.

8 Da Hiridus ya ga Yesu, sai ya yi murna ƙwarai, don tun dā ma yana marmari ya gan shi a kan abin da ya ji game da shi. Ya yi fata ya ga Yesu, yă kuma yi waɗansu ayyukan banmamaki. 9 Ya yi masa tambayoyi masu yawa, amma Yesu bai ba shi ko amsa ba. 10 Manyan firistoci da malaman dokoki suna tsaye a wurin, suna kawo zargi masu ƙarfi a kansa. 11 Sai Hiridus da sojojinsa suka wulaƙanta shi, suka yi masa ba’a. Sa’an nan, suka sa masa babban riga, suka mai da shi wurin Bilatus. 12 A ranar, Hiridus da Bilatus suka zama abokan juna, don tun dā ma, su abokan gāba ne.