Yesu a Gaban Bilatus a Karo na Biyu
Juma'a gab da fitowar rana (Yohanna 19:14)
A hankali, ba da son rai ba, cikin tsoro kuma, Bilatus ya amince da buƙatar Majalisa cewa a gicciye Kiristi.
30 ko 29 bayan haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Mattiyu 27:15–26
27:15 A wannan irin Biki, gwamna yana da wata al’ada, ta sakin ɗan kurkuku guda wanda taron suka zaɓa.
16 To, a wannan lokaci kuwa suna da wani shahararren ɗan kurkuku da ake kira Barabbas.
17 Saboda haka da taron suka taru, sai Bilatus ya tambaye su ya ce, “Wane ne a cikinsu kuke so in sakar muku. Barabbas ko Yesu wanda ake kira Kiristi?”
18 Don ya san saboda sonkai ne suka ba da Yesu a gare shi.
19 Yayinda Bilatus yake zaune a kan kujerar shari’a, sai matarsa ta aika masa da wannan saƙo cewa, “Kada ka sa hannunka a kan marar laifin nan, domin na sha wahala ƙwarai, a cikin mafarki yau game da shi.”
20 Amma manyan firistoci da dattawa suka shawo kan taron, su ce, a ba su Barabbas, amma a kashe Yesu.
21 Gwamna ya yi tambaya ya ce, “Wane ne cikin biyun nan, kuke so in sakar muku?”
Suka ce, “Barabbas.”
22 Bilatus ya yi tambaya, “To, me zan yi da Yesu wanda ake kira Kiristi?”
Duka suka ce, “A gicciye shi!”
23 Bilatus ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?”
Amma suka ƙara tā da ihu, suna cewa, “A gicciye shi!”
24 Da Bilatus ya ga cewa ba ya kaiwa ko’ina, sai ma hargitsi ne yake so yă tashi, sai ya ɗibi ruwa, ya wanke hannuwansa a gaban taron ya ce, “Ni kam, ba ruwana da alhakin jinin mutumin nan. Wannan ruwanku ne!”
25 Sai dukan mutane suka amsa, suka ce, “Bari alhakin jininsa yă zauna a kanmu da ’ya’yanmu!”
26 Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.
Markus 15:6–15
15:6 Yanzu fa, al’ada ce a lokacin Bikin, a saki ɗan kurkuku guda wanda mutane suka roƙa.
7 Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ’yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi. 8 Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yă yi musu abin da ya saba yi.
9 Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?”
10 Don ya san saboda sonkai ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi.
11 Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu.
12 Bilatus ya tambaye su ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?”
13 Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!”
14 Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?”
Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!”
15 Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.
Luka 23:13–25
23:13 Bilatus ya tara manyan firistoci, da masu mulki, da mutane, 14 ya ce musu, “Kun kawo mini wannan mutum, a matsayin wanda yana zuga mutane su yi tawaye. Na bincike shi a gabanku, ban ga a kan me kuka kawo kararsa ba. 15 Haka ma Hiridus, shi ya sa ya dawo da shi nan wurinmu. Kamar yadda ku ma kun gani, ba abin da mutumin nan ya yi, da ya isa mutuwa.
16 Saboda haka, zan yi masa bulala, in sāke shi.”
18 Suka yi ihu gaba ɗaya suka ce, “A yi gaba da wannan mutum! A sake mana Barabbas!” 19 (Barabbas yana kurkuku saboda laifin tā da hankali a birnin, da kuma don kisankai.)
20 Sai Bilatus ya sāke yin musu magana don yana so ya saki Yesu. 21 Amma sai suka ci gaba da ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!”
22 Ya sāke ce musu, sau na uku, “Don me? Wane laifi wannan mutum ya yi? Ni dai ban same shi da wani dalilin da ya isa a kashe shi ba. Saboda haka, zan sa a hore shi, sa’an nan in sāke shi.”
23 Amma suna ihu, suna nacewa, suna cewa, dole a gicciye shi, har ihunsu ya rinjaye shi.
24 Sai Bilatus ya biya bukatarsu da ya ji roƙonsu.
25 Ya saki mutumin da aka jefa a kurkuku saboda tā da hankali, da kisankai, shi wanda suka roƙa. Sa’an nan ya ba da Yesu ga nufinsu.
Yohanna 18:39–19:16
18:39 Amma fa kuna da wata al’ada in lokacin Bikin Ƙetarewa ya yi, nakan sakar muku da ɗan kurkuku ɗaya. To, kuna so in sakar muku ‘sarkin Yahudawa’?”
40 Sai suka ɗau kururuwa suna cewa, “Kai, ba shi ba! A ba mu Barabbas!” To, Barabbas ɗin nan yana da hannu dumu-dumu a wani tawaye.
19:1 Sa’an nan Bilatus ya tafi da Yesu ya kuma sa aka yi masa bulala. 2 Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai ruwan shunayya. 3 Suka yi ta zuwa wurinsa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!” Suna ta marinsa a fuska.
4 Bilatus kuwa ya sāke fitowa ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi don ku san cewa ban same shi da wani abin zargi ba.” 5 Sa’ad da Yesu ya fito sanye da rawanin ƙayar da kuma riga mai ruwan shunayya, sai Bilatus ya ce musu, “Ga mutumin!”
6 Nan da nan da manyan firistoci da ma’aikatansu suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce, “A gicciye! A gicciye!”
Amma Bilatus ya amsa ya ce, “Ku, ku ɗauke shi ku gicciye. Ni dai ban same shi da wani abin zargi ba.”
7 Yahudawa dai suka nace suna cewa, “Mu fa muna da doka, kuma bisa ga dokar dole yă mutu domin ya mai da kansa Ɗan Allah.”
8 Da Bilatus ya ji haka, sai tsoro ya ƙara kama shi, 9 sai ya sāke koma cikin fada. Ya tambayi Yesu, “Daga ina ka fito?” Amma Yesu bai amsa masa ba. 10 Bilatus ya ce, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka san cewa ina da ikon sakinka, ko gicciye ka ba?”
11 Yesu ya amsa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.”
12 Daga nan fa, Bilatus ya yi nemi yă saki Yesu, sai dai Yahudawa suka yi ta ihu suna cewa, “In ka saki wannan mutum, kai ba abokin Kaisar ba ne. Duk wanda ya ɗauka kansa a matsayin sarki, ai, yana gāba da Kaisar ne.”
13 Da Bilatus ya ji haka, sai ya fito da Yesu, ya kuma zauna a kujerar shari’ar da ake ce da shi Daɓen Dutse (wanda a harshen Arameyik ana ce da shi Gabbata). 14 Ranar Shirye-shiryen Makon Bikin Ƙetarewa ce kuwa, wajen sa’a ta shida.
Sai Bilatus ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku.”
15 Amma suka yi ihu suka ce, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!”
Bilatus ya ce, “A! In gicciye sarkinku?”
Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu dai, ba mu da wani sarki sai Kaisar.”
16 A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi.
Saboda haka sojoji suka tafi da Yesu.