Yahudawa Sun Dawo daga Zaman Bauta (continued)

536 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Zabura 116–117

1 Ina ƙaunar Ubangiji, gama ya ji muryata;

ya ji kukata ta neman jinƙai.

2 Domin ya juye kunnensa gare ni,

zan kira gare shi muddin ina da rai.

3 Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni,

wahalar kabari sun zo a kaina;

na cika da wahala da ɓacin rai.

4 Sai na kira ga sunan Ubangiji na ce,

“Ya Ubangiji, ka cece ni!”

5 Ubangiji mai alheri ne da kuma mai adalci;

Allahnmu yana cike da tausayi.

6 Ubangiji yana tsare masu tawali’u;

sa’ad da nake cikin tsananin bukata, ya cece ni.

7 Ka kwantar da hankali, ya raina,

gama Ubangiji mai alheri ne a gare ka.

8 Gama kai, ya Ubangiji, ka ceci raina daga mutuwa,

idanuna daga hawaye,

ƙafafuna daga tuntuɓe,

9 don in iya tafiya a gaban Ubangiji

a ƙasar masu rai.

10 Na gaskata, saboda haka na ce,

“An azabtar da ni ƙwarai.”

11 Kuma cikin rikicewana na ce,

“Dukan mutane maƙaryata ne.”

12 Yaya zan sāka wa Ubangiji

saboda dukan alherinsa gare ni?

13 Zan daga kwaf na ceto

in kuma kira ga sunan Ubangiji.

14 Zan cika alkawurana ga Ubangiji

a gaban dukan mutanensa.

15 Abu mai daraja a gaban Ubangiji

shi ne mutuwar tsarkakansa.

16 Ya Ubangiji, da gaske ni bawanka ne;

ni bawanka ne, ɗan baiwarka;

ka ’yantar da ni daga sarƙoƙi.

17 Zan yi hadayar godiya gare ka

in kuma kira bisa sunan Ubangiji.

18 Zan cika alkawurana ga Ubangiji

a gaban dukan mutanensa,

19 a filayen gidan Ubangiji,

a tsakiyarki, ya Urushalima.

Yabi Ubangiji.

117:1 Yabi Ubangiji, dukanku al’umma;

ku ɗaukaka shi, dukanku mutane.

2 Gama ƙaunarsa da girma take gare mu,

amincin Ubangiji kuma madawwami ne har abada.

Yabi Ubangiji.

Zabura 125

Waƙar haurawa.

1 Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona,

wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada.

2 Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima,

haka Ubangiji ya kewaye mutanensa

yanzu da har abada kuma.

3 Sandar mulkin mugaye ba zai ci gaba da kasance

a kan ƙasar da take rabon adalai ba,

domin kada masu adalci su yi amfani

da hannuwansu su aikata mugunta.

4 Ka yi alheri, ya Ubangiji, ga waɗanda suke nagartattu,

ga waɗanda suke masu aikata gaskiya a zuciyarsu.

5 Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyi

Ubangiji zai kore su tare da masu aikata mugunta.

Salama tă kasance tare da Isra’ila.

Zabura 127–128

Waƙar haurawa. Ta Solomon.

1 In ba Ubangiji ne ya gina gida ba,

masu gininta suna wahala a banza ne.

In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba,

masu tsaro suna yin tsaro a banza.

2 Banza ne ka farka da wuri

ka koma da latti,

kana fama don abincin da za ka ci,

gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.

3 ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,

yara lada ne daga gare shi.

4 Kamar kibiyoyi a hannun jarumi

haka ’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

5 Mai albarka ne mutumin

da korinsa sun cika da su.

Ba za a kunyata su ba

sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

Waƙar haurawa.

128:1 Masu albarka ne dukan masu tsoron Ubangiji,

waɗanda suke tafiya a hanyoyinsa.

2 Za ka ci amfanin aikinka;

albarku da wadata za su zama naka.

3 Matarka za tă zama kamar kuringar inabi mai ’ya’ya

a cikin gidanka;

’ya’yanka maza za su zama kamar tohon zaitun

kewaye da teburinka.

4 Ta haka mai albarka yake

wanda yake tsoron Ubangiji.

5 Bari Ubangiji ya albarkace ka daga Sihiyona

dukan kwanakin ranka;

bari ka ga wadatar Urushalima,

6 bari kuma ka rayu ka ga ’ya’ya ’ya’yanka.

Salama tă kasance tare da Isra’ila.

Zabura 134

Waƙar haurawa.

1 Yabi Ubangiji, dukanku bayin Ubangiji

waɗanda kuke hidima da dare a gidan Ubangiji.

2 Ku tā da hannuwanku a cikin wurinsa mai tsarki

ku kuma yabi Ubangiji.

3 Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa,

ya albarkace ku daga Sihiyona.