Taron Jama’a na Farko
1015 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
1 Sa’ad da Dawuda ya tsufa yana kuma da cikakken shekaru, ya sa ɗansa Solomon sarki bisa Isra’ila.
1 Dawuda ya sa aka kira dukan shugabannin Isra’ila su taru a Urushalima, shugabannin kabilu, manyan hafsoshin ɓangarorin hidimar sarki, manyan hafsoshin dubu-dubu da manyan hafsoshin ɗari-ɗari, da kuma shugabanni masu lura da dukan mallaka da dabbobin da suke na sarki da kuma ’ya’yansa maza, tare da fadawa, jarumawa da kuma dukan mayaƙa masu kwarjini.
2 Sarki Dawuda ya miƙe tsaye ya ce, “Ku saurare ni, ’yan’uwana da kuma mutanena. Na yi niyya in gina gida a matsayin wurin hutu domin akwatin alkawarin Ubangiji, domin zatin Allahnmu, na kuma yi shiri don in gina shi. 3 Amma Allah ya ce mini, ‘Ba za ka gina gida domin Sunana ba, saboda kai mayaƙi ne ka kuma zub da jini.’
4 “Duk da haka Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya zaɓe ni daga dukan iyalina don in zama sarki bisa Isra’ila har abada. Ya zaɓi Yahuda a matsayin shugaba, kuma daga gidan Yahuda ya zaɓi iyalina, daga ’ya’yan mahaifina maza kuwa ya gamsu ya mai da ni sarki bisa dukan Isra’ila. 5 Cikin dukan ’ya’yana maza, Ubangiji kuwa ya ba ni su da yawa, ya zaɓi ɗana Solomon yă zauna a kujerar mulkin Ubangiji a bisa Isra’ila. 6 Ya ce mini, ‘Solomon ɗanka shi ne wanda zai gina gidana da filayen da suke kewaye da shi, gama na zaɓe shi yă zama ɗana, ni kuma zan zama mahaifinsa. 7 Zan kafa mulkinsa har abada in bai kauce ga kiyaye umarnaina da dokokina ba, yadda ake yi a wannan lokaci.’
8 “Saboda haka yanzu ina umartanku a gaban dukan Isra’ila da na taron jama’ar Ubangiji, da kuma a kunnuwan Allahnmu. Ku yi hankali ku kiyaye dukan umarnan Ubangiji Allahnku don ku mallaki wannan kyakkyawar ƙasa ku kuma bar wa zuriyarku gādo har abada.
9 “Kai kuma ɗana Solomon, ka san Allah na mahaifinka, ka kuma yi masa hidima da dukan zuciya da kuma yardar rai, gama Ubangiji yana binciken zuciya, yana kuma gane dukan aniyar tunani. In ka neme shi, za ka same shi; amma in ka yashe shi, zai ƙi ka har abada. 10 Ka lura fa, gama Ubangiji ya zaɓe ka don ka gina haikali a matsayin wuri mai tsarki. Ka yi ƙarfin hali ka kuma yi aiki.”
1 Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka
zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.
2 Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata,
Allahna, wanda nake dogara.”
3 Tabbatacce zai cece ka
daga tarkon mai farauta
da kuma daga cututtuka masu kisa.
4 Zai rufe ka da fikafikansa,
a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka;
amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.
5 Ba za ka ji tsoron razanar dare,
ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba,
6 ko bala’in da yake aukowa cikin duhu,
ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana.
7 Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka,
dubu goma a hannun damanka,
amma ba abin da zai zo kusa da kai.
8 Za ka dai gan da idanunka
yadda ake hukunta mugaye.
9 In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka,
har ma Ubangiji wanda yake mafakata,
10 to, babu wani mugun abin da zai same ka,
ba masifar da za tă zo kusa da tentinka.
11 Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai
don su tsare ka a dukan hanyoyinka;
12 za su tallafe ka da hannuwansu,
don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.
13 Za ka taka zaki da gamsheƙa;
za ka tattake babban zaki da maciji.
14 Ubangiji ya ce, “Domin ya ƙaunace ni, zan kuɓutar da shi;
zan kiyaye shi, gama ya yarda da sunana.
15 Zai kira bisa sunana, zan kuma amsa masa;
zan kasance tare da shi a lokacin wahala,
zan kuɓutar da shi in kuma girmama shi.
16 Da tsawon rai zan ƙosar da shi
in kuma nuna masa cetona.”
Da alama zabura ce daga ƙarshen rayuwar Dawuda
Zabura ce ta yabo. Ta Dawuda.
1 Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki;
zan yabi sunanka har abada abadin.
2 Kowace rana zan yabe ka
in kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin.
3 Ubangiji da girma yake ya kuma cancanci yabo
girmansa ya fi ƙarfin ganewar mutum.
4 Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara;
za su yi magana game da manyan ayyukanka.
5 Za su yi zancen ɗaukakarka mai daraja,
zan kuma yi tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.
6 Za su yi magana game da ikon ayyukanka masu bantsoro,
zan kuma yi shelar manyan ayyukanka.
7 Za su yi bikin yalwar alherinka
suka kuma rera adalcinka da farin ciki.
8 Ubangiji mai alheri da kuma tausayi,
mai jinkirin fushi cike kuma da ƙauna.
9 Ubangiji nagari ne ga duka;
yana tausayin dukan abubuwan da ya yi.
10 Dukan abubuwan da ka yi za su yabe ka, ya Ubangiji;
tsarkakanka za su ɗaukaka ka.
11 Za su yi maganar ɗaukakar mulkinka
za su kuma yi zancen ikonka,
12 saboda dukan mutane su san manyan ayyukanka
da ɗaukakar darajar mulkinka.
13 Mulkinka madawwamin mulki ne,
sarautarka kuma za tă dawwama cikin dukan zamanai.
Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransa
mai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi.
14 Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗi
yana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa.
15 Idanun kowa yana dogara gare ka,
kana kuma ba su abincinsu a lokacin da ya dace.
16 Ka buɗe hannunka
ka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai.
17 Ubangiji mai adalci ne cikin dukan hanyoyinsa
yana kuma nuna ƙauna ga dukan abubuwan da ya yi.
18 Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi,
ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.
19 Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa;
yakan ji kukansu yă kuma cece su.
20 Ubangiji yakan lura da dukan waɗanda suke ƙaunarsa,
amma dukan mugaye zai hallaka su.
21 Bakina zai yi magana cikin yabon Ubangiji.
Bari kowace halitta ta yabi sunansa mai tsarki
har abada abadin.