Shirye-shiryen Hidimar Haikali

1015 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

1 Tarihi 23:2–24:31

2 Ya kuma tattara dukan shugabannin Isra’ila a wuri ɗaya, haka kuma ya yi da firistoci da Lawiyawa. 3 Aka ƙidaya Lawiyawan da suke ’yan shekaru talatin da haihuwa ko fiye, suka kai wajen mutum dubu talatin da takwas. 4 Dawuda ya ce, “Cikin waɗannan, dubu ashirin da huɗu za su lura da aikin haikalin Ubangiji, dubu shida su zama manyan na ma’aikata da alƙalai. 5 Dubu huɗu su zama matsaran ƙofofi, dubu huɗu kuma su yabi Ubangiji da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe waɗanda na tanada saboda wannan manufa.”

6 Dawuda ya rarraba Lawiyawa ƙungiya-ƙungiya bisa ga ’ya’yan Lawi maza. Gershon, Kohat da Merari.

7 Na Gershonawa,

Ladan da Shimeyi.

8 ’Ya’yan Ladan maza su ne,

Yehiyel na farko, Zetam da Yowel, su uku ne duka.

9 ’Ya’yan Shimeyi maza su ne,

Shelomot, Haziyel da Haran, su uku ne duka.

Waɗannan su ne kawunan iyalan Ladan.

10 ’Ya’yan Shimeyi maza kuwa su ne,

Yahat, Zina, Yewush da Beriya.

Waɗannan su ne ’ya’yan Shimeyi maza, su huɗu ne duka.

11 Yahat shi ne na fari, Ziza kuma na biyu, amma Yewush da Beriya ba su haifi ’ya’ya maza da yawa ba; saboda haka aka ƙidaya su kamar iyali ɗaya a wurin rabon aiki.

12 ’Ya’yan Kohat maza su ne,

Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel, su huɗu ne duka.

13 ’Ya’yan Amram maza su ne,

Haruna da Musa.

Haruna shi ne aka keɓe, shi da zuriyarsa har abada, don su tsarkake kayayyakin mafi tsarki, su miƙa hadayu a gaban Ubangiji, su yi hidima a gabansa su kuma furta albarku a cikin sunansa har abada. 14 An ƙidaya aka kuma haɗa ’ya’yan Musa maza mutumin Allah a sashen kabilar Lawi.

15 ’Ya’yan Musa maza su ne,

Gershom da Eliyezer.

16 Zuriyar Gershom su ne,

Shebuwel ne ɗan fari.

17 Zuriyar Eliyezer su ne,

Rehabiya ne ɗan fari.

Eliyezer ba shi da waɗansu ’ya’ya maza, amma ’ya’yan Rehabiya maza sun yi yawa.

18 ’Ya’yan Izhar maza su ne,

Shelomit ne ɗan fari.

19 ’Ya’yan Hebron maza su ne,

Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.

20 ’Ya’yan Uzziyel maza su ne,

Mika na fari da Isshiya na biyu.

21 ’Ya’yan Merari maza su ne,

Mali da Mushi.

’Ya’yan Mali maza su ne,

Eleyazar da Kish.

22 Eleyazar ya mutu ba ’ya’yan maza, yana da ’ya’ya mata ne kawai. ’Yan’uwansu, ’ya’yan Kish maza, suka aure su.

23 ’Ya’yan Mushi maza su ne,

Mali, Eder da Yeremot, su uku ne duka.

24 Waɗannan ne zuriyar Lawi bisa ga iyalansu, kawunan iyalai kamar yadda aka rubuta su a ƙarƙashin sunayensu aka kuma ƙirga kowa, wato, masu aikin da suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye waɗanda suka yi hidima a cikin haikalin Ubangiji. 25 Gama Dawuda ya ce, “Tun da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya ba da hutu ga mutanensa, ya kuma zo ya zauna a Urushalima har abada, 26 Lawiyawa ba sa ƙara bukata su ɗauki tabanakul ko kuwa waɗansu kayayyakin da ake amfani da su a hidima.” 27 Bisa ga umarnin ƙarshe na Dawuda, za a ƙidaya Lawiyawa daga ’yan shekara ashirin ko fiye.

28 Aikin Lawiyawa shi ne su taimaki zuriyar Haruna a hidimar haikalin Ubangiji; su lura da filaye da kuma ɗakunan da suke gefe, su tsarkake dukan kayayyaki masu tsarki, su kuma yi waɗansu ayyuka a gidan Allah. 29 Su ne za su lura da burodin da aka ajiye a tebur, lallausan gari don hadaya ta gari, waina marar yisti, toyawa da kwaɓawa, da kuma dukan awon yawa da kuma girman abubuwa. 30 Su ne kuma za su tsaya kowace safiya su yi godiya, su kuma yabi Ubangiji. Za su kuma yi haka da yamma 31 da kuma a duk sa’ad da aka miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a Asabbatai da bukukkuwan Sabon Wata da kuma a ƙayyadaddun bukukkuwa, za su yi hidima a gaban Ubangiji kullum bisa ga yawan da aka tsara da kuma a hanyar da aka tsara musu.

32 A haka kuwa Lawiyawa suka yi ayyukansu don Tentin Sujada, don Wuri Mai Tsarki da kuma a ƙarƙashin ’yan’uwansu zuriyar Haruna, saboda hidimar haikalin Ubangiji.

24:1 Waɗannan su ne sassan ’ya’yan Haruna maza.

’Ya’yan Haruna maza su ne Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar. 2 Amma Nadab da Abihu sun mutu kafin mahaifinsu, ba su kuma haifi ’ya’ya maza ba; saboda haka Eleyazar da Itamar suka yi hidimar firistoci. 3 Tare da taimakon Zadok zuriyar Eleyazar da Ahimelek wani zuriyar Itamar. Dawuda ya karkasa su zuwa ɓangarori don aikinsu bisa ga hidima. 4 Akwai ɗumbun shugabanni a cikin zuriyar Eleyazar fiye da zuriyar Itamar, aka kuma karkasa su haka, kawuna goma sha shida daga zuriyar Eleyazar da kuma kawuna iyalai takwas daga zuriyar Itamar. 5 Aka karkasa su babu sonkai ta wurin jifa ƙuri’a, gama akwai manyan ma’aikatan wuri mai tsarki da manyan ma’aikatan Allah a cikin zuriyar Eleyazar da Itamar.

6 Shemahiya ɗan Netanel, wani Balawe ne marubuci, ya rubuta sunayensu a gaban sarki da kuma a gaban manyan ma’aikata. Zadok firist, Ahimelek ɗan Abiyatar da kuma kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa, iyali guda daga Eleyazar, guda kuma daga Itamar.

7 Ƙuri’a ta farko ta faɗa a kan Yehoyarib,

na biyu a kan Yedahiya,

8 na uku a kan Harim,

na huɗu a kan Seyorim,

9 na biyar a kan Malkiya,

na shida a kan Miyamin,

10 na bakwai a kan Hakkoz,

na takwas a kan Abiya,

11 na tara a kan Yeshuwa,

na goma a kan Shekaniya,

12 na goma sha ɗaya a kan Eliyashib,

na goma sha biyu a kan Yakim,

13 na goma sha uku a kan Huffa,

na goma sha huɗu a kan Yeshebeyab,

14 na goma sha biyar a kan Bilga,

na goma sha shida a kan Immer,

15 na goma sha shida a kan Hezir,

na goma sha takwas a kan Haffizzez,

16 na goma sha tara a kan Fetahahiya,

na ashirin a kan Ezekiyel,

17 na ashirin da ɗaya wa Yakin,

na ashirin da biyu a kan Gamul,

18 na ashirin da uku wa Delahiya

da kuma na ashirin da huɗu a kan Ma’aziya.

19 Ga tsarin aikinsu na hidima sa’ad da suka shiga haikalin Ubangiji, bisa ga ƙa’idar da kakansu Haruna ya kafa, yadda Ubangiji, Allah na Isra’ila ya umarce shi.

20 Game da sauran zuriyar Lawi kuwa,

Daga ’ya’yan Amram maza. Shubayel;

daga ’ya’yan Shubayel maza. Yedehiya.

21 Game da Rehabiya kuwa, daga ’ya’yansa maza. Isshiya shi ne na fari.

22 Daga mutanen Izhar, Shelomot;

daga ’ya’yan Shelomot maza, Yahat.

23 ’Ya’yan Hebron maza su ne, Yeriya na fari, Amariya na biyu, Yahaziyel na uku da Yekameyam na huɗu.

24 Ɗan Uzziyel shi ne, Mika;

daga ’ya’yan Mika maza, Shamir.

25 Ɗan’uwan Mika shi ne, Isshiya;

daga ’ya’yan Isshiya maza, Zakariya.

26 ’Ya’yan Merari su ne, Mali da Mushi.

Ɗan Ya’aziya shi ne, Beno.

27 ’Ya’yan Merari su ne,

daga Ya’aziya, Beno, Shoham, Zakkur da Ibri.

28 Daga Mali, Eleyazar, wanda ba shi da ’ya’ya maza.

29 Daga Kish, ɗan Kish shi ne,

Yerameyel.

30 Kuma ’ya’yan Mushi maza su ne, Mali, Eder da Yerimot.

Waɗannan su ne Lawiyawa bisa ga iyalansu.

31 Suka kuma jifa ƙuri’a, kamar dai yadda ’yan’uwansu zuriyar Haruna suka yi, a gaban Sarki Dawuda da gaban Zadok, Ahimelek, da kuma a gaban kawunan iyalan firistoci da na Lawiyawa. Aka yi da iyalan wa daidai da iyalan ƙane.