Ɗaukakar Ikkilisiya da Nasararta a Nan Gaba

710 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ishaya 59:16–61:11

16 Ya ga cewa babu wani,

ya yi mamaki cewa babu wanda zai shiga tsakani;

saboda haka hannunsa ya aikata masa ceto,

adalcinsa kuma ya raya shi.

17 Ya yafa sulke a matsayin rigar ƙirji,

da hulan kwanon ceto a kansa;

ya sa rigunan ɗaukar fansa

ya kuma nannaɗe kansa da kishi kamar a cikin alkyabba.

18 Bisa ga abin da suka yi,

haka za a sāka

fushi a kan abokan gābansa

ramuwa kuma a kan maƙiyansa;

zai sāka wa tsibirai abin da ya dace da su.

19 Daga yamma, mutane za su ji tsoron Ubangiji,

daga mafitar rana kuma, za su girmama ɗaukakarsa.

Gama zai zo kamar rigyawa mai tsananin gudu

cewa numfashin Ubangiji zai tafi tare da shi.

20 “Mai fansa zai zo Sihiyona,

zuwa waɗanda suke cikin Yaƙub da suka tuba daga zunubansu,”

in ji Ubangiji.

21 “Game da ni dai, ga alkawarina da su,” in ji Ubangiji. “Ruhuna, wanda yake a kanka, da kuma maganata da na sa a bakinka ba za tă rabu da bakinka ba, ko daga bakunan ’ya’yanka ba, ko kuwa daga bakunan zuriyarsu ba daga wannan lokaci zuwa gaba da kuma har abada,” in ji Ubangiji.

60:1 “Ki tashi, ki haskaka, gama haskenki ya zo,

ɗaukakar Ubangiji ya taso a kanki.

2 Duba, duhu ya rufe duniya

duhu mai kauri kuma yana bisa mutane,

amma Ubangiji ya taso a kanki

ɗaukakarsa kuma ya bayyana a bisanki.

3 Al’ummai za su zo wurin haskenki,

sarakuna kuma zuwa asubahin sabon yininki.

4 “Ki ɗaga idanunki ki duba kewaye da ke.

Duka sun tattaru suka kuma zo wurinki;

’ya’yanki maza daga nesa,

ana kuma ɗaukan ’ya’yanki mata a hannu.

5 Sa’an nan za ki duba ki kuma haskaka

zuciyarki zai motsa ya kuma cika da farin ciki;

za a kawo miki wadata daga tekuna,

za a kawo miki arzikin al’ummai.

6 Manyan ayarin raƙuma za su cika ƙasar,

ƙananan raƙuma ke nan daga Midiyan da Efa.

Daga Sheba kuma duka za su zo,

suna ɗauke da zinariya da turare

suna shelar yabon Ubangiji.

7 Dukan garkunan Kedar za su taru a wurinki

ragunan Nebayiwot za su yi miki hidima;

za a karɓe su kamar hadayu a kan bagadenki,

zan kuma darjanta haikalina mai ɗaukaka.

8 “Su wane ne waɗannan da suke firiya kamar gizagizai,

kamar kurciyoyi suna zuwa sheƙarsu?

9 Babu shakka tsibirai suna dogara gare ni;

jiragen Tarshish kuma su ne a gaba,

suna kawo ’ya’yanki maza daga nesa,

tare da azurfa da zinariya,

domin su girmama Ubangiji Allahnki,

Mai Tsarkin nan na Isra’ila,

gama ya cika ki da daraja.

10 “Baƙi za su sāke gina katangarki,

sarakunansu kuma za su yi miki hidima.

Ko da yake a cikin fushi na buge ki,

da tagomashi zan yi miki jinƙai.

11 Ƙofofinki kullum za su kasance a buɗe,

ba za a ƙara rufe su da rana ko da dare ba,

saboda mutane su kawo miki dukiyar al’ummai,

sarakunansu za su kasance a gaba a jerin gwanon nasara.

12 Gama al’umma ko masarautar da ba tă bauta miki ba, za tă hallaka;

za tă lalace sarai.

13 “Darajar Lebanon za tă zo wurinki,

itatuwan fir da dai ire-irensu da kuma itatuwan saifires duka

za su zo don su ƙayatar da wurina mai tsarki;

zan kuma ɗaukaka wurin ƙafafuna.

14 ’Ya’ya maza masu zaluntarku za su zo suna rusunawa a gabanki;

dukan waɗanda suka rena ki za su rusuna a ƙafafunki

su kuma ce da ke Birnin Ubangiji,

Sihiyona na Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

15 “Ko da yake an yashe ki aka kuma ƙi ki,

har babu wani da ya ratsa a cikinki,

zan mai da ke madawwamiyar abar taƙama

da kuma farin cikin dukan zamanai.

16 Za ki sha madarar al’ummai

a kuma shayar da ke da nonon sarauta.

Sa’an nan za ki san cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki,

Mai Fansarki, Mai Ikon nan na Yaƙub.

17 A maimakon tagulla zan kawo zinariya,

azurfa kuma a maimakon baƙin ƙarfe.

A maimakon katako zan kawo tagulla,

baƙin ƙarfe kuma a maimakon duwatsu.

Zan sa salama ta zama gwamnarki

adalci kuma mai mulkinki.

18 Ba za a ƙara jin hayaniyar tashin hankali a ƙasarki ba,

balle lalacewa ko hallaka a cikin iyakokinki,

amma za ki kira katangarki Ceto

ƙofofinki kuma Yabo.

19 Rana ba za tă ƙara zama haskenki a yini ba,

balle hasken wata ya haskaka a kanki,

gama Ubangiji zai zama madawwamin haskenki,

Allahnki kuma zai zama ɗaukakarki.

20 Ranarki ba za tă ƙara fāɗuwa ba

watanki kuma ba zai ƙara shuɗewa ba;

Ubangiji zai zama madawwamin haskenki,

kwanakin baƙin cikinki za su ƙare.

21 Sa’an nan dukan mutanenki za su zama masu adalci

za su kuma mallaki ƙasar har abada.

Su ne reshen da na shuka,

aikin hannuwana,

don nuna darajata.

22 Mafi ƙanƙanta a cikinki za tă zama dubu,

ƙarami zai zama al’umma mai girma.

Ni ne Ubangiji,

cikin lokacinsa zan yi haka da sauri.”

61:1 Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina,

domin Ubangiji ya shafe ni

domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta.

Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci,

don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru

in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu

2 don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji

da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu,

don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,

3 in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona,

in maido musu rawani mai kyau

a maimako na toka,

man murna

a maimako na makoki,

da kuma rigar yabo

a maimako na ruhun fid da zuciya.

Za a ce da su itatuwan oak na adalci,

shukin Ubangiji

don bayyana darajarsa.

4 Za su sāke gina kufai na dā

su raya wurare da aka lalace tun da daɗewa;

za su sabunta biranen da aka rurrushe

da aka lalace tun zamanai masu yawa da suka wuce.

5 Baƙi za su yi kiwon garkunanki;

baƙi za su yi miki noman gonaki da gonakin inabinki.

6 Za a kuma kira ku firistocin Ubangiji,

za a kira ku masu hidimar Allahnmu.

Za ku ci wadatar waɗansu al’ummai,

kuma a cikin dukiyarsu za ku yi taƙama.

7 A maimakon kunyarsu

mutanena za su sami rabi riɓi biyu,

a maimakon wulaƙanci

za su yi farin ciki cikin gādonsu;

ta haka za su gāji rabo riɓi biyu a ƙasarsu,

da kuma madawwamin farin ciki zai zama nasu.

8 “Gama ni, Ubangiji, ina ƙaunar adalci;

na ƙi fashi da aikata laifi.

Cikin adalcina zan sāka musu

in kuma yi madawwamin alkawari da su.

9 Za a san da zuriyarsu a cikin al’ummai

’ya’yansu kuma a cikin mutane.

Dukan waɗanda suka gan su za su san

cewa su mutane ne da Ubangiji ya sa wa albarka.”

10 Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji;

raina yana farin ciki a cikin Allahna.

Gama ya suturce ni da rigunan ceto

ya yi mini ado da rigar adalci,

yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist

kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.

11 Gama kamar yadda ƙasa takan sa tsire-tsire su tohu

lambu kuma ya sa iri ya yi girma,

haka Ubangiji Mai Iko Duka zai sa adalci da yabo

su tsiro a gaban dukan al’ummai.