Ɗaukakar Ikkilisiya da Nasararta a Nan Gaba (continued)

710 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Ishaya 62–64

1 Saboda Sihiyona ba zan yi shiru ba,

saboda Urushalima ba zan huta ba,

sai adalcinta ya haskaka kamar hasken safiya,

cetonta kuma ya haskaka kamar fitila mai haske.

2 Al’ummai za su ga adalcinki,

sarakuna kuma za su ga ɗaukakarki;

za a kira ki da sabon suna

sunan da bakin Ubangiji zai ambata.

3 Za ki zama rawanin daraja a hannun Ubangiji,

rawanin sarauta a hannun Allahnki.

4 Ba za a ƙara ce da ke Yasasshiya ba,

ko a kira ƙasarki Kango.

Amma za a ce da ke Hefziba

ƙasarki kuma Bewula;

gama Ubangiji zai ji daɗinki,

ƙasarki kuma za tă yi aure.

5 Kamar yadda saurayi kan auri yarinya,

haka ’ya’yanki maza za su aure ki;

kamar kuma yadda ango yakan yi farin ciki da amaryarsa,

haka Allahnki zai yi farin ciki da ke.

6 Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima;

ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana.

Ku da kuke kira bisa sunan Ubangiji,

kada ku ba kanku hutu,

7 kuma kada ku ba shi hutu sai ya kafa Urushalima

ya kuma mai da ita yabon duniya.

8 Ubangiji ya rantse da hannunsa na dama

ta hannunsa kuma mai iko cewa,

“Ba zan ƙara ba da hatsinki

ya zama abinci ga abokan gābanki ba,

baƙi kuma ba za su ƙara shan ruwan inabin

wanda kika sha wahala samu ba;

9 amma waɗanda suka girbe shi za su ci shi

su kuma yabi Ubangiji,

waɗanda kuma suka tattara ’ya’yan inabi za su sha shi

a filayen wurina mai tsarki.”

10 Ku wuce, ku wuce ƙofofi!

Ku shirya hanya saboda mutane.

Ku gina, ku gina babbar hanya!

Ku kawar da duwatsu.

Ku ɗaga tuta saboda al’ummai.

11 Ubangiji ya yi shela

ga iyakokin duniya cewa,

“Faɗa wa Diyar Sihiyona,

‘Ga Mai Cetonki yana zuwa!

Ga ladarsa tana tare da shi,

sakamakonsa yana raka shi.’ ”

12 Za a ce da shi Tsattsarkar Mutane,

Fansassu na Ubangiji;

za a kuma ce da ke Wadda Aka Nema

Birnin da Ba Za a Ƙara Yashe ta ba.

63:1 Wane ne wannan mai zuwa daga Edom,

daga Bozra, saye da jajjayen rigunarsa?

Wane ne wannan, sanye cikin daraja,

tafe cikin girmar ƙarfinsa?

“Ni ne, mai magana cikin adalci,

mai ikon ceto.”

2 Me ya sa rigunanka suka yi ja,

sai ka ce na wanda yake tattaka ’ya’yan inabi?

3 “Na tattake ’ya’yan inabi ni kaɗai;

cikin al’ummai kuma babu wani tare da ni.

Na tattake su cikin fushina

Na matse su cikin hasalata;

jininsu ya fantsamar wa rigunana,

na kuma ɓata dukan tufafina.

4 Gama ranar ɗaukan fansa tana a cikin zuciyata,

kuma shekarar fansata ta zo.

5 Na duba, amma babu wanda zai taimaka,

na yi mamaki cewa ba wanda ya goyi baya;

saboda haka hannuna ya yi mini ceto,

fushina kuma ya rayar da ni.

6 Na tattake al’ummai cikin fushina;

cikin hasalata kuma na sa sun bugu

na kuma zub da jininsu a ƙasa.”

7 Zan ba da labarin alherin Ubangiji,

ayyukan da suka sa a yabe shi,

bisa ga dukan abubuwan da Ubangiji ya yi mana,

I, ayyuka masu kyan da ya yi

domin gidan Isra’ila,

bisa ga jinƙansa da yawan alheransa.

8 Ya ce, “Babu shakka su mutanena ne,

’ya’ya maza waɗanda ba za su ruɗe ni ba”;

ta haka ya zama Mai Cetonsu.

9 Cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu,

mala’ikan da yake gabansa ya cece su.

Cikin ƙauna da jinƙai ya fanshe su;

ya kuma ɗaga su ya riƙe su

dukan kwanakin dā

10 Duk da haka suka yi tawaye

suka ɓata wa Ruhu Mai Tsarki rai.

Saboda haka ya juya ya kuma zama abokin gābansu

shi kansa kuma ya yaƙe su.

11 Sa’an nan mutanensa suka tuna kwanakin dā,

kwanakin Musa da mutanensa,

ina yake shi wanda ya fitar da su ta teku,

da makiyayan garkensa?

Ina shi yake wanda ya sa

Ruhunsa Mai Tsarki a cikinsu,

12 wanda ya aika hannu ɗaukakarsa mai iko

ya kasance a hannun dama na Musa,

wanda ya raba ruwaye a gabansu,

don yă sami wa kansa madawwamin suna,

13 wanda ya bishe su cikin zurfafa?

Kamar doki a fili,

ba su yi tuntuɓe ba;

14 kamar shanun da suke gangarawa zuwa kwari,

haka Ruhun Ubangiji ya ba su hutu.

Ga yadda ka bishe mutanenka

don ka ba wa kanka suna mai ɗaukaka.

15 Ka duba daga sama ka gani

daga kursiyinka da yake bisa, mai tsarki da kuma mai ɗaukaka.

Ina kishinka da kuma ikonka?

Ka janye juyayi da kuma tausayin da kake yi mana daga gare mu.

16 Amma kai Ubanmu ne,

ko Ibrahim bai san mu ba

Isra’ila kuma bai yarda da mu ba;

kai, ya Ubangiji, kai ne Ubanmu,

Mai Fansarmu tun fil azal ne sunanka.

17 Don me, ya Ubangiji, ka sa muna barin hanyoyinka

muka kuma taurare zukatanmu don kada mu girmama ka?

Ka komo domin darajar bayinka,

kabilan da suke abin gādonka.

18 Gama a ɗan lokaci mutanenka suka mallaki wurinka mai tsarki,

amma yanzu abokan gābanmu sun tattake wurinka mai tsarki.

19 Mu naka tun fil azal;

ba ka taɓa yin mulki a kansu ba,

ba a taɓa kira su da sunanka ba.

64:1 Da ma za ka tsage sammai ka sauko,

ai, da duwatsu za su yi rawar jiki a gabanka!

2 Kamar sa’ad da wuta takan ci rassa

ta sa ruwa ya tafasa,

ka sauko ka sanar da sunanka ga abokan gābanka

ka kuma sa al’ummai su yi rawan jiki a gabanka!

3 Gama sa’ad da ka aikata abubuwan bantsoron da ba mu sa tsammani ba,

ka sauko, duwatsu kuma suka yi rawar jiki a gabanka.

4 Tun fil azal babu wanda ya taɓa ji,

babu kunnen da ya gane,

babu idon da ya ga wani Allah in ban da kai,

wanda ya aikata waɗannan al’amura a madadin waɗanda suke sa zuciya a gare shi.

5 Kakan taimaki waɗanda suke murnan yin abin da yake daidai,

waɗanda sukan tuna da hanyoyinka.

Amma sa’ad da muka ci gaba da yin zunubi,

kakan yi fushi.

Ta yaya za mu sami ceto ke nan?

6 Dukanmu mun zama kamar wanda yake marar tsabta,

kuma dukan ayyukanmu masu adalci sun zama kamar ƙazaman tsummoki;

duk mun zama kamar busasshen ganye,

kamar iska haka zunubanmu sukan share mu.

7 Babu wanda yake kira bisa sunanka

ko ya yi ƙoƙarin riƙe ka;

gama ka ɓoye fuskarka daga gare mu

ka kuma sa muka lalace saboda zunubanmu.

8 Duk da haka, Ubangiji, kai ne Ubanmu.

Mu yumɓu ne, kai kuma mai ginin tukwane;

dukanmu aikin hannunka ne.

9 Kada ka yi fushi fiye da kima, ya Ubangiji;

kada ka tuna da zunubanmu har abada.

Da ma ka dube mu, muna roƙonka,

gama dukanmu mutanenka ne.

10 Biranenka masu tsarki sun zama hamada;

har Sihiyona ma ta zama hamada; Urushalima ta zama kango.

11 Haikalinmu mai tsarki da kuma mai daraja, inda kakanninmu suka yabe ka,

an ƙone da wuta,

kuma dukan abubuwan da muke ƙauna sun lalace.

12 Bayan dukan wannan, ya Ubangiji, ba za ka yi wani abu ba?

Za ka yi shiru ka hore mu fiye da kima?