Cikakken Labarin Mamaya ta Biyu ta Sennakerib
710 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
17 Sai sarkin Assuriya ya aika da babban shugaban sojojinsa, da shugaban dattawansa, da wakilinsa daga birnin Lakish tare da ƙungiyar sojoji masu yawa zuwa Urushalima domin su yaƙi Sarki Hezekiya. Da suka haura sai suka tsaya a wurin lambatun da yake kawo ruwa daga Tafkin Tudu, kusa da hanyar Filin Mai Wanki. 18 Suka kira sarki, sai Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka je wurinsu.
19 Jagoran dogarawan sarkin Assuriya ya ce musu, “Ku ce wa Hezekiya,
“ ‘Ga abin da babban sarkin Assuriya ya ce, da wa kake taƙama? 20 Ka ce kana da dabara da ƙarfin soji, amma bagu kawai kake yi. Da wa ka dogara har da za ka yi mini tawaye? 21 Na sani kana dogara da Masar, wadda take kamar karar masara, wadda in ka jingina a kai, za tă karye tă soki hannunka. Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga dukan wanda ya dogara da shi. 22 Sai ya ci gaba da cewa, in kuma ka ce mini “Muna dogara ga Ubangiji Allahnmu ne,” ba masujadansa da bagadansa ne Hezekiya ya ciccire, yana ce wa Urushalima da Yahuda, “Dole ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima”?
23 “ ‘Yanzu, ka zo ku shirya da shugabana, sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, in za ka sami mahayansu! 24 Yaya za ka yi tsayayya da mafi ƙanƙantan hafsan shugabana, ko da kana dogara da Masar don kekunan yaƙi da mahaya dawakai? 25 Ban da haka ma, kana gani cewa na zo in hallaka wannan wuri ne ba tare da na ji daga Ubangiji ba? Ubangiji da kansa ne ya ce da ni in kawo wa wannan ƙasa hari in hallaka ta.’ ”
26 Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa suka ce wa jagoran dakarun, “Muna roƙonka ka yi wa bayinka magana da harshen Arameyik da yake muna ji. Kada ka yi mana magana da Yahudanci domin kada mutanen da suke bisa katanga su ji!”
27 Amma shugaban sojojin ya ce, “Ai, ba gare ku da sarkinku kaɗai ne shugabana ya aike ni ba. Amma har ga mutanen da suke zaune a kan katangar birnin, waɗanda za su ci kashinsu, su sha fitsarinsu!”
28 Sai shugaban sojojin ya yi kira da Yahudanci ya ce, “Ku ji muryar babban sarki, sarkin Assuriya! 29 Ga abin da sarki ya faɗa; kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku. Ba zai iya cetonku daga hannuna ba. 30 Kada ku yarda Hezekiya yă rinjaye ku cewa ku dogara ga Allah, sa’ad da ya ce da ku, ‘Ba shakka Ubangiji zai cece mu; yana ce da ku birnin nan ba zai faɗa a hannun sarkin Assuriya ba.’
31 “Kada ku saurari Hezekiya. Ga abin da sarkin Assuriya ya ce, ku shirya zaman lafiya da ni, ku fito zuwa wurina. Kowane ɗayanku kuwa zai ci ’ya’yan inabinsa da ’ya’yan ɓaurensa, yă kuma sha ruwa daga randarsa, 32 har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi, da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu!
“Kada ku saurari Hezekiya, don karya yake muku, sa’ad da ya ce, ‘Ubangiji zai cece mu.’ 33 Akwai allahn wata al’ummar da ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannun sarkin Assuriya? 34 Ina allolin Hamat da na Arfad? Ina allolin Sefarfayim, da na Hena, da na Iffa? Sun cece Samariya daga hannuna? 35 Wanne a cikin dukan allolin ƙasashen nan ya iya ceton ƙasarsa da gare ni? Shugaban sojojin ya kuma ci gaba da cewa, ta yaya Ubangiji zai ceci Urushalima daga hannuna?”
36 Amma mutane suka yi shiru ba su amsa masa ba, domin sarki ya umarta cewa, “Kada ku amsa masa.”
37 Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf, marubuci, suka je wurin Hezekiya da tufafinsu a kece, suka faɗa masa abin da shugaban sojojin ya faɗa.
19:1 Da sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya shiga haikalin Ubangiji. 2 Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna marubuci da shugabannin firistoci, dukansu sanye da tufafin makoki, zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz. 3 Suka ce masa, “Hezekiya ya ce, yau ranar wahala ce, da ta cin mutunci, da ta shan kunya, ga shi, ’ya’ya suna gab da a haife su, amma ba ƙarfin da za a yi yunƙuri a haife su. 4 Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka ya ji dukan maganganun sarkin yaƙi, wanda maigidansa, sarkin Assuriya, ya aiko don yă rena Allah mai rai. Bari Ubangiji Allahnka yă tsawata masa saboda maganar da ya ji. Saboda haka ka yi addu’a domin raguwar da har yanzu suke a raye.”
5 Da fadawan sarki Hezekiya suka isa wurin Ishaya, 6 Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku, in ji Ubangiji, ‘Kada abin da ka ji yă firgita ka, wato, waɗannan kalmomin da karen nan na sarkin Assuriya ya yi saɓo da su. 7 Saurara! Zan sa masa wani ruhun da zai sa yă ji wata jita-jitar da za tă sa yă koma ƙasarsa. A can zan sa a kashe shi da takobi a ƙasarsa.’ ”
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’ya’yan Kora maza. Maskil ne.
1 Mun ji da kunnuwanmu, ya Allah;
kakanninmu sun faɗa mana
abin da ka aikata a kwanakinsu,
tun dā can.
2 Da hannunka ka kori al’ummai
ka kuma dasa kakanninmu;
ka ragargaza mutanen
ka kuma sa kakanninmu suka haɓaka.
3 Ba da takobinsu ba ne suka ci ƙasar,
ba kuwa ƙarfin hannunsu ne ya ba su nasara ba;
hannun damanka ne, ƙarfin hannunka,
da kuma hasken fuskarka, gama ka ƙaunace su.
4 Kai ne Sarkina da kuma Allahna,
wanda ya ba da nasarori wa Yaƙub.
5 Ta wurinka mun tura abokan gābanmu baya;
ta wurin sunanka muka tattake maƙiyanmu.
6 Ba na dogara ga bakana,
takobina ba ya kawo nasara;
7 amma kana ba mu nasara a kan abokan gābanmu,
ka sa abokan gābanmu suka sha kunya.
8 A cikin Allah muke fariyarmu dukan yini,
kuma za mu yabi sunanka har abada. Sela
9 Amma yanzu ka ƙi mu ka kuma ƙasƙantar da mu;
ba ka ƙara fita tare da mayaƙanmu.
10 Ka sa muka gudu a gaban abokin gāba,
kuma abokan gābanmu suka washe mu.
11 Ka ba da mu a cinye kamar tumaki
ka kuma watsar da mu a cikin al’ummai.
12 Ka sayar da mutanenka a kuɗin da bai taka ƙara ya karye ba
babu wata riba daga sayar da su da ka yi.
13 Ka mai da mu abin dariya ga maƙwabtanmu,
abin dariya da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.
14 Ka sa muka zama abin ba’a a cikin al’ummai;
mutanen suna kaɗa mana kai.
15 Dukan yini ina cikin wulaƙanci,
fuskata kuma ta rufu da kunya
16 saboda ba’ar waɗanda suke zagi suke kuma ƙina,
saboda abokan gābana, waɗanda suka sha alwashi sai sun yi ramuwa.
17 Dukan wannan ya faru da mu,
ko da yake ba mu manta da kai ba
ko mu kasance masu ƙarya ga alkawarinka.
18 Zukatanmu ba su juya baya;
ƙafafunmu ba su kauce daga hanyarka ba.
19 Amma ka ragargaza mu ka kuma maishe mu abin farautar karnukan jeji
ka kuma rufe mu cikin duhu baƙi ƙirin.
20 Da a ce mun manta da sunan Allahnmu
ko mun miƙa hannuwanmu ga baƙin alloli,
21 da Allah bai gane ba,
da yake ya san asiran zuciya?
22 Duk da haka saboda kai mun fuskanci mutuwa dukan yini;
aka ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.
23 Ka farka, ya Ubangiji! Don me kake barci?
Ta da kanka! Kada ka ƙi mu har abada.
24 Me ya sa ka ɓoye fuskarka
ka manta da azabanmu da kuma danniyar da ake mana?
25 An kai mu ƙasa zuwa ƙura;
jikunanmu sun manne da ƙasa.
26 Ka tashi ka taimake mu;
ka cece mu saboda ƙaunarka marar ƙarewa.