An Halaka Sojojin Sennakerib

710 kafin haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

2 Sarakuna 19:8–19

8 Da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye, ya kuma iske sarkin yana yaƙi da Libna.

9 To, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana zuwa masa da yaƙi. Saboda haka ya sāke aika manzanni zuwa wurin Hezekiya cewa, 10 “Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda, kada ka bar allahn da kake dogara gare shi yă ruɗe ka cewa, ‘Urushalima ba za tă fāɗi a hannun sarkin Assuriya ba.’ 11 Ba shakka ka riga ka ji abin da sarkin Assuriya ya yi da dukan ƙasashe, yana hallaka su gaba ɗaya. Kai kuwa kana ji za a cece ka? 12 Allolin al’umman da kakannina suka hallaka, sun cece su ne, allolin Gozan, da na Haran, da na Rezef, da kuma na mutane Eden da suke a Tel Assar? 13 Ina sarkin Hamat, da sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarfayim, ko na Hena da kuma na Iffa?”

14 Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga manzannin ya karanta. Sa’an nan ya tashi ya tafi haikalin Ubangiji ya shimfiɗa wasiƙar a gaban Ubangiji. 15 Hezekiya kuwa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda yake zaune tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah bisa dukan mulkokin duniya. Kai ka yi sama da duniya. 16 Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka ji; ka buɗe idanunka ya Ubangiji ka gani; ka saurari kalmomin da Sennakerib ya aiko don yă yi wa Allah mai rai ba’a.

17 “Da gaske ne, ya Ubangiji, cewa sarakunan Assuriya sun hallakar da waɗannan al’ummai da ƙasashensu. 18 Sun jefar da allolinsu cikin wuta, suka hallaka su, gama ba alloli ba ne, katakai ne da kuma duwatsu, ayyukan hannuwan mutane. 19 To, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannunsa, don dukan mulkokin duniya su san cewa kai kaɗai, ya Ubangiji ne Allah.”

Zabura 73

Zabura ta Asaf.

1 Tabbatacce Allah mai alheri ne ga Isra’ila,

ga waɗanda suke masu tsabta a zuciya.

2 Amma game da ni, ƙafafuna suna gab da yin santsi;

tafin ƙafana ya yi kusan zamewa.

3 Gama na yi kishin masu girman kai

sa’ad da na ga cin gaban da masu mugunta suke yi.

4 Ba sa yin wata fama;

jikunansu lafiya suke da kuma ƙarfi.

5 Ba sa shan wata wahalar da sauran mutane ke sha;

ba su da damuwa irin na ’yan adam.

6 Saboda girman kai ya zama musu abin wuya;

tā da hankali ya zama musu riga.

7 Daga mugayen zukatansu laifi kan fito

mugaye ƙulle-ƙullen da suke cikin zukatansu ba su da iyaka.

8 Suna ba’a, suna faɗin mugayen abubuwa;

cikin girman kan suna barazana yin danniya.

9 Bakunansu na cewa sama na su ne,

kuma harsunansu sun mallaki duniya.

10 Saboda haka mutanensu sun juya gare su

suna kuma shan ruwa a yalwace.

11 Suna cewa, “Yaya Allah zai sani?

Mafi Ɗaukaka yana da sani ne?”

12 Ga yadda mugaye suke,

kullum ba su da damuwa, arzikinsu yana ta ƙaruwa.

13 Tabbatacce a banza na bar zuciyata da tsabta;

a banza na wanke hannuwa don nuna rashin laifi.

14 Dukan yini na sha annoba;

an hukunta ni kowace safiya.

15 Da na ce, “Zan faɗa haka,”

da na bashe ’ya’yanka.

16 Sa’ad da na yi ƙoƙari in gane wannan,

sai ya zama danniya a gare ni

17 sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah;

sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.

18 Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi;

ka jefar da su ga hallaka.

19 Duba yadda suka hallaka farat ɗaya,

razana ta share su gaba ɗaya!

20 Kamar yadda mafarki yake sa’ad da mutum ya farka,

haka yake sa’ad da ka farka, ya Ubangiji,

za ka rena su kamar almarai.

21 Sa’ad da zuciyata ta ɓaci

hankalina kuma ya tashi,

22 na zama marar azanci da jahili;

na zama kamar dabba a gabanka.

23 Duk da haka kullum ina tare da kai;

ka riƙe ni a hannun damana.

24 Ka bishe ni da shawararka,

bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka.

25 Wa nake da shi a sama in ba kai ba?

Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai.

26 Jikina da zuciyata za su iya raunana,

amma Allah ne ƙarfin zuciyata

da kuma rabona har abada.

27 Waɗanda suke nesa da kai za su hallaka;

kakan hallaka dukan waɗanda suke maka rashin aminci.

28 Amma game da ni, yana da kyau in kasance kusa da Allah.

Na mai da Ubangiji Mai Iko Duka mafakata;

zan yi shelar dukan ayyukanka.

2 Sarakuna 19:20–35

20 Sai Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo zuwa wurin Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, na ji addu’arka game da Sennakerib sarkin Assuriya. 21 Ga abin da Ubangiji yana cewa game da shi,

“ ‘Budurwar Sihiyona

ta rena ka tana kuma yin maka ba’a.

Diyar Urushalima

ta kaɗa kanta yayinda kake gudu.

22 Wane ne ka zaga, ka kuma yi masa saɓo?

Wa kake gāba da shi har ka ɗaga muryarka,

har ka tā da idanunka da fahariya?

Kana gāba da Mai Tsarki na Isra’ila!

23 Ta wurin manzanninka

ka tara wa Ubangiji zagi.

Ka kuma ce,

“Da yawa kekunan yaƙina

na haye kan ƙwanƙolin duwatsu,

wurin mafi tsawo na Lebanon.

Na sassare itacen al’ul nasa mafi tsawo

mafi daraja na itacen fir nasa.

Na ratsa har can tsakiyar kurmi,

mafi kyau na kurminsa.

24 Na tona rijiyoyi a ƙasashen waje

na kuma sha ruwa a can.

Da tafin ƙafafuna

na busar da dukan rafuffukan Masar.”

25 “ ‘Ba ka taɓa ji ba?

Tun da daɗewa na ƙaddara haka.

Tuntuni kuwa na shirya shi;

yanzu kuma na sa ya faru,

cewa ka mai da birane masu katanga

tarin duwatsu.

26 Ƙarfin mutanensu ya tsiyaye,

suka razana aka kuma kunyata su.

Suna kama da tsirai a gona,

kamar sabon toho

kamar ciyawa mai tohuwa bisa rufin ɗaki

wanda ya bushe saboda zafi, kafin yă yi girma.

27 “ ‘Amma na san wurin zamanka

da fitarka da shigarka

da yadda kake fushi da ni.

28 Domin kana fushi da ni

reninka ya iso kunnuwata,

zan sa ƙugiyata a hancinka

da linzamina a bakinka,

zan kuma sa ka koma

a ta hanyar da ka zo.’

29 “Wannan zai zama alama a gare ka, ya Hezekiya,

“Bana, za ku ci amfanin gonar da ya tsira da kansa,

baɗi kuma amfanin gonar da ya tsiro daga na bara.

Amma a shekara ta uku, za ku yi shuki, ku kuma girbe,

ku dasa gonakin inabi, ku kuma ci ’ya’yansa.

30 Sau ɗaya kuma ragowar masarautar Yahuda

za tă yi saiwoyi a ƙasa ta kuma ba da ’ya’ya a bisa.

31 Gama daga Urushalima za a sami ragowa,

daga Dutsen Sihiyona kuma za a sami waɗanda suka tsira.

Himmar Ubangiji Maɗaukaki za tă cika wannan.

32 “Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce game da sarkin Assuriya,

“Ba zai shiga birnin nan ba

ko yă harba kibiya a nan.

Ba zai kusace ta da garkuwa

ko yă yi mata zoben yaƙi ba.

33 Ta hanyar da ya zo ne zai koma;

ba zai shiga birnin nan ba, in ji Ubangiji.

34 Zan kāre birnin nan in cece ta,

saboda kaina da kuma bawana Dawuda.”

35 A daren nan mala’ikan Ubangiji ya fita ya kashe dakaru dubu ɗari da tamanin da biyu a sansanin Assuriyawa. Da mutane suka farka da safe, sai ga gawawwaki ko’ina.

Zabura 75–76

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Kada A Hallaka.” Zabura ta Asaf. Waƙa ce.

1 Muna maka godiya, ya Allah,

muna maka godiya, gama Sunanka yana kusa;

mutane na faɗin ayyukanka masu banmamaki.

2 Ka ce, “Na zaɓi ƙayyadadden lokaci;

ni ne wanda yake shari’ar gaskiya.

3 Sa’ad da duniya da dukan mutanenta suka girgiza,

ni ne wanda na riƙe ginshiƙan daram. Sela

4 Ga masu girman kai na ce, ‘Kada ku ƙara taƙama,’

ga mugaye kuma, ‘Kada ku ɗaga ƙahoninku.

5 Kada ku ɗaga ƙahoninku gāba da sama;

kada ku yi magana da miƙaƙƙen wuya.’ ”

6 Ba wani daga gabas ko yamma

ko hamada da zai ɗaukaka mutum.

7 Amma Allah ne mai yin shari’a,

yakan saukar da wannan, yă kuma tayar da wani.

8 A hannun Ubangiji akwai kwaf

cike da ruwan inabi mai kumfa gauraye da kayan yaji;

yakan zuba shi, dukan mugayen duniya kuwa

su sha shi tas.

9 Game da ni dai, zan furta wannan har abada;

zan rera yabo ga Allah na Yaƙub,

10 wanda ya ce, “Zan yanke ƙahonin dukan mugaye,

amma za a ɗaga ƙahonin adalai sama.”

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura ta Asaf. Waƙa ce.

76:1 A cikin Yahuda an san Allah;

sunansa da girma yake a cikin Isra’ila.

2 Tentinsa yana a Salem

mazauninsa yana a Sihiyona.

3 A can ya kakkarya kibiyoyin wuta,

garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi. Sela

4 Darajarka tana da haske,

fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa.

5 Jarumawa sun zube kamar ganima

sun yi barcinsu na ƙarshe;

ba ko jarumi guda

da zai iya ɗaga hannuwansa.

6 A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub,

doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi.

7 Kai kaɗai ne za a ji tsoro.

Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi?

8 Daga sama ka yi shelar hukunci,

ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,

9 sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a,

don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar. Sela

10 Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo,

waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka.

11 Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su;

bari dukan ƙasashen maƙwabta

su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro.

12 Ya kakkarya ƙarfin masu mulki;

sarakunan duniya suna tsoronsa.

2 Sarakuna 19:36–37

36 Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya tā da sansanin ya kuma janye. Ya koma Ninebe ya zauna a can.

37 Wata rana yayinda yake sujada a haikalin Nisrok, allahnsa, sai ’ya’yansa maza, Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka gudu zuwa ƙasar Ararat. Sai Esar-Haddon ɗansa ya gāje shi.