Bulus Ya Rubuta wa Afisawa

Bulus ya rubuta wasiƙarsa zuwa ga Afisawa domin ya ƙarfafa su cikin bangaskiyar Kirista. Da kalmomi masu motsa zuciya ƙwarai, ya bayyana jinƙan Allah da aka nuna wajen kiran Al’ummai ta wurin bangaskiya ga Kiristi ba tare da wajabta musu bin Dokar Musa ba. Kuma ya ƙarfafa su su kasance da tsarki da kuma halin da ya dace da wannan bangaskiya, waɗanda ake bukata daga dukan waɗanda suka sami sanin ceto.

61 bayan haihuwar Almasihu

Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)

Bulus Ya Gaishe da Afisawa

Bayan gaisuwarsa, ta musamman da ta gama gari, Bulus ya ɓarke da godiya ga Allah cikin farin ciki saboda albarkun ruhaniya da ya ba Al’ummai, da kuma kiransu bisa ga nufinsa na jinƙai su zama zaɓaɓɓun mutanensa, masu tsarki marasa aibi. An riga an ƙaddara a karɓe su a matsayin ’ya’yansa ta wurin bangaskiya ga Yesu Kiristi. Ta wurin jininsa an fanshe su, an kuma gafarta zunubansu, ba ta wurin Dokar Musa ba, sai dai ta wurin yalwar jinƙansa. Ya ba manzanni hikima a al’amuran ruhaniya da kuma basirar amfani da ita, ya kuma bayyana musu asirin nufinsa (karɓar Al’ummai cikin ikilisiyarsa ba tare da wajabta musu bin dokar Yahuda ba), da shirin da za a bi a tattara Yahudawa da Al’ummai tare ƙarƙashin Yesu Kiristi su zama ikilisiya ɗaya. Ta wurin Kiristi, Yahudawa masu ba da gaskiya sun karɓi gādon ruhaniya da aka yi wa ’ya’yan Ibrahim na ruhaniya alkawari, domin an riga an ƙaddara su, ko kuwa an sake zaɓensu, bisa ga nufin yardarsa, ta wurin bangaskiya ga Kiristi. Su da suka fara ba da gaskiya ga Kiristi za su zama sanadin yabon ɗaukakarsa ta wurin kai sanin ceto ga duniya. A cikinsa Al’ummai ma sun ba da gaskiya, sa’ad da suka ji maganar gaskiya daga manzanni. Kuma ta wurinsa aka ba da Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba ya yi alkawari, a matsayin tabbacin gādon har abada na Yahudawa, da kuma yanzu na Al’ummai, har sai sun shiga tare cikin mallakar sama da aka saya musu, domin yabo da ɗaukakar Kiristi.

Afisawa 1:1–14

1 Bulus, wanda Allah ya zaɓa don yă zama manzon Kiristi Yesu,

Zuwa ga tsarkaka da suke a Afisa, da kuma suke amintattu cikin Kiristi Yesu.

2 Alheri da salama daga Allah Ubanmu da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

3 Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama. 4 Gama ya zaɓe mu a cikin Kiristi tun dā can, kafin ma a halicci duniya don mu zama masu tsarki da kuma marasa aibi a gabansa. 5 A cikin ƙauna, ya ƙaddara mu zama ’ya’yansa na riƙo ta wurin Kiristi Yesu, bisa ga nufinsa na alheri. 6 Ya yi haka don mu yabi Allah saboda alherin da ya yi mana saboda mu na ƙaunataccen Ɗansa ne. 7 A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah 8 wanda ya ba mu babu iyaka tare da dukan hikima da fahimta. 9 Allah ya yi abin da ya nufa, ya kuma sanar mana shirin asirin da ya riga ya shirya yă cika ta wurin Kiristi. 10 Nufinsa ke nan, idan lokaci ya cika, yă harhaɗa dukan abubuwa a ƙarƙashin ikon Kiristi, wato, dukan abubuwan da suke sama da abubuwan da suke ƙasa.

11 A cikinsa ne kuma aka zaɓe mu mu sami gādo daga Allah, an kuwa ƙaddara mu ga haka bisa ga nufin wannan da yake zartar da dukan abubuwa yadda ya yi nufi yă yi. 12 Manufar Allah ita ce cewa mu da muka fara sa bege a cikin Kiristi, mu yi zaman yabon ɗaukakar Allah. 13 An kuma haɗa ku a cikin Kiristi lokacin da kuka ji saƙon nan na gaskiya, wanda yake labari mai daɗi na cetonku. Da kuka ba da gaskiya, sai aka yi muku alamar shaida a cikinsa da Ruhu Mai Tsarki. 14 Ruhu Mai Tsarkin nan shi ne tabbacin da Allah ya yi na cewa zai ba mu kome da ya yi alkawari, har ya sa muka sani nan gaba Allah zai ceci waɗanda suke nasa. Wannan kuwa domin yabon ɗaukakarsa ne.

Bulus Ya Yi Addu’a domin a Haskaka Fahimtarsu

Bulus ya gode wa Allah saboda tubarsu, ya kuma yi addu’a domin a ƙara haskaka musu fahimtar gaskiya, su kuma kai ga cikakkiyar fahimtar albarkun bishara da kuma Maƙaginta mai ɗaukaka. Ta wurin ikonsa aka ta da Kiristi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi zuwa matsayi da mulki mafi girma a wannan duniya da kuma duniya mai zuwa. An sa kome ƙarƙashinsa domin amfanin ikilisiya, wadda ake ɗauka musamman a matsayin jikinsa, shi kuma Babban Kanta ne. Ikilisiya tana karɓar cikar baiwarta da alherinta na ruhaniya daga gare shi wanda yake cika dukan mutane a kowane wuri, kuma shi ne kome a cikin kome.

Afisawa 1:15–23

15 Saboda haka, tun lokacin da na ji labarin bangaskiyarku cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunar da kuke yi wa dukan mutanen Allah, 16 ban fasa yin godiya saboda ku ba, ina tuna da ku cikin addu’o’ina. 17 Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhun hikima da na ganewa, domin ku san shi da kyau. 18 Ina kuma addu’a cewa zuciyarku tă waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa. 19 Ina addu’a ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali, wanda yake namu. Ikon da yake aiki a cikinmu, ɗaya ne da ikon nan 20 da ya tā da Kiristi daga matattu, ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya. 21 Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa. 22 Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi iko a kan kome don amfanin ikkilisiya. 23 Kuma ikkilisiya ce jikinsa; ta kuma cika da Kiristi, wanda ya cika kome ta kowace hanya.

Ceto ta Wurin Bangaskiya, Ba ta Wurin Doka ko Cancanta Ba

Domin ya motsa Afisawa su nuna godiya, Bulus ya tuna musu da ƙaunar Kiristi, wanda ya rayar da su, ko kuwa ya cika su da alherinsa, sa’ad da suke matattu cikin laifuffuka da zunubai. Ya bayyana halayensu da zamansu sa’ad da suke arna. Sa’an nan, a madadin Yahudawa da suka tuba, ya yarda cewa su ma, kafin tubarsu, sun yi rayuwa haka, har su ma, kamar Al’ummai, sun zama ’ya’yan fushi bisa ga dabi’a. Amma Allah cikin jinƙansa mai girma, saboda alherinsa na kyauta, ya tanadi hanyar cetonsu, ya kuma rayar da su: ya rayar da Yahudawa da Al’ummai duka a cikin Kiristi, daga mutuwar zunubi zuwa rayuwar adalci. Ya ta da su tare, ta wurin tashin Kiristi daga matattu ya ba su ɗanɗanon tashinsu da zai zo, ta wurin ɗaukakarsa kuma ya ba su begen cewa ta wurinsa za a karɓe su cikin wuraren samaniya. A wannan ya nuna yalwar jinƙansa da gafararsa marar misali ta wurin Kiristi Yesu. Domin ta wurin jinƙan Allah, ta wurin bangaskiya, aka cece su: ba ta wurin ayyukan Dokar Musa ba, ko kuwa wata cancantar kansu ba, “domin kada kowa ya yi fahariya,” sai dai ta wurin baiwar kyauta da nufin Allah. Domin su aikinsa ne, waɗanda ya halitta a cikin Kiristi Yesu domin ayyuka masu kyau, waɗanda Allah ya riga ya ƙaddara cewa za su sami ikon yi ta wurin aikin Ruhu Mai Tsarki nasa.

Afisawa 2:1–10

1 Ku kam, a dā ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku. 2 Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah. 3 Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah. 4 Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai, 5 ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku. 6 Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya. 7 Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu. 8 Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah. 9 Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai. 10 Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

An Mai da Yahudawa da Al’ummai Ikilisiya Ɗaya cikin Kiristi

Bayan ya bayyana halin faɗuwa na mutumin Yahuda da Ba’al’umme, Bulus ya roƙi Al’ummai su tuna cewa kafin tubarsu ba su da sanin Kiristi. An hana su shiga gatan mutanen Yahuda, ba su da rabo cikin alkawarin da aka yi wa Ibrahim, ba su da bege mai tushe na gafarar zunubai ko na rashin mutuwar rai, kuma ba su da Allah a duniya. Amma yanzu, ta wurin bangaskiya ga Kiristi, Allah ya kawo waɗanda suke nesa da alkawarin kusa ta wurin jinin Kiristi. Kiristi ya mutu domin mutumin Yahuda da Ba’al’umme, ya kuma zama hadayar salama, ya kafa ikilisiya ɗaya daga masu ba da gaskiya na mutanen biyu. Ta wurin mutuwarsa a cikin jiki ya soke ƙa’idodin Yahuda da suka raba su, suka kuma jawo ƙiyayyarsu. Ya haɗa su biyu a cikinsa su zama sabon mutum ɗaya, ko sabon jiki ɗaya, yana kawo salama a tsakaninsu, domin ya sulhunta su biyu da Allah ta wurin hadayar jikinsa ta kafara, bayan ya kashe, ko ya hallaka, ƙiyayyar da zunubi ya haifar tsakanin Allah da mutum. Bayan tashinsa daga matattu ya yi wa mutumin Yahuda da Ba’al’umme wa’azin salama da sulhu iri ɗaya ta wurin manzanninsa, kuma ta wurinsa dukansu suna da hanyar zuwa ga Uba ɗaya ta wurin Ruhu Mai Tsarki ɗaya. Al’ummai ba baƙi ba ne kuma, sai dai an haɗa su da Yahudawa, an kuma ba su gata ɗaya da mutanensa masu tsarki. Suna cikin iyalinsa, ko ikilisiyarsa da ake gani, wadda aka gina bisa koyarwar annabawa a tsohon tsarin zamanin da na manzanni a sabon tsarin, Yesu Kiristi kansa kuwa shi ne dutsen kusurwa, yana haɗa Yahudawa da Al’ummai tare a gini ɗaya. A cikinsa ginin, wanda ya ƙunshi Yahudawa da Al’ummai da aka haɗa tare, yana girma ta wurin ƙarin sababbin masu tuba ya zama haikali mai tsarki ga Allah. Kuma ta wurin Kiristi ana gina su, ’yan’uwansa, tare su zama wurin zaman Allah, Ruhunsa yana zaune a cikinsu.

Afisawa 2:11–22

11 Saboda haka, ku tuna dā ku Al’ummai ne bisa ga haihuwa, waɗanda kuma ake kira masu “kaciya” sukan kira ku “marasa kaciya” (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu). 12 Ku kuma tuna a lokacin ba ku san Kiristi ba. A ware kuke daga mutanen Isra’ila, ba ku kuma da dangantaka da alkawaran da Allah ya yi da su. Kun yi zama a duniyan nan babu bege kuma babu Allah. 13 Amma yanzu a cikin Kiristi Yesu, ku da dā kuke can da nesa an kawo ku kusa ta wurin jinin Kiristi.

14 Gama shi kansa shi ne salamarmu, shi ne ya kawo ƙungiyoyi biyu suka zama ɗaya, ya kuma rushe katangan nan ta ƙiyayya wadda ta raba mu. 15 Kiristi ya ba da jikinsa don yă kawar da doka da dukan umarnanta da kuma ƙa’idodinta. Ya yi haka domin yă halicci sabuwar zuriya daga zuriyoyin nan biyu. Ta haka kuma ya kawo salama tsakaninsu. 16 A kan gicciye, Kiristi ya kawar da ƙiyayyar da take tsakaninmu da juna. Ya kuma kawo sulhu tsakaninmu da Allah. 17 Ya zo ya yi muku wa’azin salama; ku da kuke nesa da shi, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa. 18 Gama ta wurinsa dukanmu za mu iya zuwa gun Uba ta wurin Ruhu guda.

19 Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ’yan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma. 20 Ku gini ne wanda manzanni da annabawa suke tushensa, Kiristi kuma shi ne dutse mafi muhimmanci na ginin. 21 Ta wurinsa ne dukan ginin yake a haɗe, shi ne kuma yake sa ginin yă yi girma, yă zama haikali mai tsarki domin Ubangiji. 22 Ku ma sashe ne na wannan ginin da Kiristi ya yi inda Allah yake zaune ta wurin Ruhunsa.