Musa Ya Maimaita Dokar Hukunci
1451 kafin haihuwar Almasihu
Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™ (OHCB)
Maimaitawar Shari’a 17:2–18:22
2 In an sami wani namiji ko ta mace mai zama a cikinku, a ɗaya daga biranen da Ubangiji ya ba ku yana aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnku ta wurin karya alkawarinsa, 3 wanda ya saba wa umarnina, har ya yi sujada ga waɗansu alloli, yana rusuna musu, ko ga rana, ko ga wata, ko kuwa ga taurarin sama, 4 in kuwa aka faɗa muku wannan, to, dole a bincika sosai. In kuwa gaskiya ne, aka kuma tabbatar cewa wannan abin ƙyama ya faru a cikin Isra’ila, 5 sai a ɗauki namijin, ko ta mace wanda ya aikata wannan mugun abu zuwa ƙofar birni, a jajjefe wannan mutum sai ya mutu. 6 Bisa ga shaidar mutum biyu ko uku, za a iya kashe mutum, amma ba za a iya kashe mutum bisa ga shaida mutum guda ba. 7 Hannuwan shaidun ne za su zama na farko a kisan wanda ake zargin, sa’an nan hannuwan dukan mutane. Dole ku fid da mugu daga cikinku.
8 In aka kawo ƙarar da yake da wuya sosai ga alƙali a kotunanku, ko wadda aka zub da jini ne, ko ta faɗa ce, ko kuwa ta wadda aka ci mutunci ce, ku kai su wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa. 9 Ku je wurin firistoci, waɗanda suke Lawiyawa, ga kuma alƙalin wanda yake mulki a lokacin. Ku bincika daga gare su, za su kuwa ba da hukunci. 10 Dole ku aikata hukuncin da suka yi a wurin da Ubangiji zai zaɓa. Ku lura fa, ku aikata kome da suka faɗa muku. 11 Ku yi bisa ga dokar da suka koyar muku da kuma hukuncin da suka yi muku. Kada ku juya daga abin da suka faɗa muku, ko zuwa dama, ko zuwa hagu. 12 Duk mutumin da ya yi rashin hankali wa alƙali, ko ga firist wanda yake aiki a nan wa Ubangiji Allahnku, dole a kashe shi. Dole ku fid da mugu daga Isra’ila. 13 Dukan mutane kuwa za su ji, su kuma ji tsoro, ba kuwa za su ƙara yin rashin hankali kuma ba.
14 Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kuka mallake ta, kuka kuma zauna a cikinta, sai kuka ce, “Bari mu naɗa sarki a kanmu kamar sauran al’umman da suke kewaye da mu,” 15 ku tabbata kun naɗa sarki a kanku wanda Ubangiji Allahnku ya zaɓa ne. Dole yă zama daga cikin ’yan’uwanku. Kada ku sa baƙo a kanku, wanda ba mutumin Isra’ila ɗan’uwanku ba. 16 Sarkin, ba zai nemi dawakai da yawa wa kansa ba, ko yă sa mutane su koma Masar don su sami ƙarin dawakai ba, gama Ubangiji ya faɗa muku, “Ba za ku ƙara koma wancan hanya kuma ba.” 17 Sarkin ba zai auri mata masu yawa ba, in ba haka ba zuciyarsa za tă karkata. Ba zai tara azurfa da zinariya da yawa ba.
18 Sa’ad da ya hau kursiyin mulkinsa, sai yă rubuta wa kansa a littafin kofin wannan doka da aka ɗauka daga na firistoci, waɗanda suke Lawiyawa. 19 Zai kasance tare da shi, zai kuma karanta shi dukan kwanakin ransa, saboda yă koyi girmama Ubangiji Allahnsa, yă kuma bi dukan kalmomin wannan doka da kuma waɗannan ƙa’idodi a hankali 20 don kada yă ɗauki kansa ya fi ’yan’uwansa, yă kuma juya daga dokar zuwa dama, ko zuwa hagu. Sa’an nan shi da kuma zuriyarsa za su daɗe suna mulki a Isra’ila.
18:1 Firistocin da suke Lawiyawa, tabbatacce dukan kabilar Lawi, ba za su sami rabo ko gādo tare da Isra’ila ba. Za su yi rayuwa a kan hadayun da aka kawo wa Ubangiji da wuta ne, gama wannan ne gādonsu. 2 Ba za su sami gādo a cikin ’yan’uwansu ba; Ubangiji ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari.
3 To, ga rabon da jama’a za su ba firistoci daga hadayun da suka miƙa ta bijimi ne, ko ta tunkiya ce; sai su ba firistoci kafaɗar, kumatun, da kuma kayan cikin. 4 Za ku ba su nunan fari na hatsinku, da sabon ruwan inabinku, da manku, da kuma gashi na fari daga askin da kuka yi na tumakinku. 5 Gama Ubangiji Allahnku ya zaɓe su da zuriyarsu daga cikin dukan kabilanku don su tsaya su yi hidima a cikin sunan Ubangiji har abada.
6 Idan Balawe ya tashi daga wani garinku, wurin da yake da zama a Isra’ila, ya tafi a wurin da Ubangiji ya zaɓa, zai iya dawo a duk lokacin da ya ga dama. 7 Zai iya yin hidima a cikin sunan Ubangiji Allahnsa kamar dukan sauran ’yan’uwansa Lawiyawa waɗanda suke hidima a can, a gaban Ubangiji. 8 Zai sami rabo daidai da sauran, ko da yake ya karɓi kuɗin mallaka na iyali da ya sayar.
9 Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku kwaikwayi hanyoyin banƙyama na al’ummai da suke can. 10 Kada a sami wani a cikinku da ya miƙa ɗansa, ko ’yarsa a wuta, ko a sami mai duba, ko mai maita, ko mai fassara gaibi, ko mai sihiri, 11 ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha’ani da matattu. 12 Duk wanda yake yin waɗannan abubuwa, shi abin ƙyama ne ga Ubangiji, saboda waɗannan abubuwa banƙyama ne kuwa Ubangiji Allahnku ya kori waɗancan al’ummai kafin ku. 13 Dole ku zama marasa zargi a gaban Ubangiji Allahnku.
14 Al’ummai da za ku kora sukan saurari waɗannan masu maita, ko masu duba. Amma ku, Ubangiji Allahnku bai yarda muku ku yi haka ba. 15 Ubangiji Allahnku zai tayar muku da wani annabi kamar ni daga cikin ’yan’uwanku. Dole ku saurare shi. 16 Gama abin da kuka nema daga Ubangiji Allahnku ke nan a Horeb, a ranar taro, sa’ad da kuka ce, “Kada ka bari mu ji muryar Ubangiji Allahnmu, ko mu ƙara ganin wuta mai girma, in ba haka ba, za mu mutu.”
17 Sai Ubangiji ya ce mini, “Abin da suka faɗa yana da kyau. 18 Zan tayar musu da wani annabi kamar ka daga cikin ’yan’uwansu; zan sa kalmomina a cikin bakinsa, zai kuma faɗa musu kome da na umarce shi. 19 Duk wanda bai saurari kalmomina da annabin nan yake magana da sunana ba, ni kaina zan nemi hakki a kan mutumin. 20 Amma duk annabin da ya ɗauka cewa yana magana da sunana a kan wani abin da ban umarce shi ya faɗa ba, ko kuwa wani annabin da ya yi magana da sunan waɗansu alloli, dole a kashe shi.”
21 Mai yiwuwa ku ce wa kanku, “Yaya za mu san cewa wannan saƙo ba Ubangiji ne ya faɗa ba?” 22 In abin da annabin ya furta da sunan Ubangiji bai faru ba, ko bai zama gaskiya ba, saƙo ne da Ubangiji bai faɗa ba ke nan. Wannan annabi ya yi rashin hankali ne kawai. Kada ku ji tsoronsa.